Connect with us

ZAMANTAKEWA

Gyaran Zuciya

Published

on

Assalaamu alaikum, yan’uwa barkanmu da sake saduwa a wannan mako cikin wannan fili namu mai albarka, karkashin wannan Jarida tamu mai farin jini da daraja. A wannan mako za mu yi takaitaccen bayani kan nesantar wadansu cutuka wadanda suka lalata mana al’umma, samuwasrsu ya haddasa gaba da kiyayya tsakanin al’umma, al’umma ta rasa aminci, jin haushin juna da nesantar juna suka zama tambarin al’umma, dukkanin al’ummar da ta wayi gari cikin wadannan halaye, hakika kaskanci da tozarci sun zo mata, zagwanyewa da koma baya ta kowacce fuska ya same ta. Wadannan cututtuka su ne: hassada, munana zato ko zargi, munafurci, girman kai, wauta ko jahilci.

Alkur’ani Mai Girma ya yi kira a matakai daban-daban wajen nesantar wadancan abubuwa da na zayyano, sannan Allah ya siffanta muminai nagari ba sa kusantar su, balle su aikata. Allah ya bayyana irin mu’amalar da za a yi wa wanda ya aikata su, a inda Ya ce cikin Suratul Furkan, sura ta 25, aya ta 63, “WA IBADUR RAHMAANIL LAZEENA YAMSHUNA ALAL ARDI HAUNAA, WA IZAA KHA’DABAHUMUL JAAHILUNA KAALUU SALAAMA”. Bayan Allah ya fara bayyana halin bayinSa nagari, siffa ta biyu sai ya ce “….Idan wawa ya zo musu da jahilci (wauta), sai su ce aminci (zaman lafiya”. Wato idan shashasha, ma’abocin wauta da jahilci ya zo da shirme da wauta, to kai mumini sai ka bi shi da hankali da ilimi. Wani ma’abocin wauta ya zo gun Imam Ahmad Bn Hambal, ya rinka tsine masa, shi kuwa sai ya sanya masa albarka. Da aka tambaye shi dalilin hakan, sai ya ce ai tsinuwa ce a tare da shi, (ita ya gado a gidansu, ita ce dabi’ar gidansu), don haka ya zo yake yada ta. Ni kuwa dake albarka ce a tare da ni, dan haka na sanya masa ita. Ma’ana dai, kowa na tallan hajar da ya gado a gidansu. To haka rayuwar magabata na kwarai take cike da ire-iren wadannan misalai, kyawawan halaye abin koyi.

Ubangiji ya koro siffofin muminai a cikin surori da dama, mafi kusa daga ciki, Suratul Mu’uminun, inda ya bayyana su cikin kyawawan halaye, da rashin wauta da shashanci da shirme. Don haka koda mumini ya aikata sa’bo, to fa ba ya dogewa a kai, bal ma tuba yake da nadamar abin da ya aikata. Ba zai rinka kurara kansa da aikin assha ba, ba zai rinka da’awar cewa su ne bariki ba, ku su ne tantagayyar yan iska da dai sauran maganganu na shirme. Bal ma, idan mumini ya ji wani na fadar haka, to takaici yake saboda muni da hatsarin wannan magana, wacce shi a tunaninsa wayewa ce da birgewa, bayan kuwa ita ce tsantsar jahilci da gidahumanci gami da wauta da rashin hankali.

Na daga cikin abubuwan da ke gyara zukatan muminai, su tace su, su tsarkake su, nesantar gulma ko maganar da ba ka da tabbas a cikinta, da yad’a ta. Allah ya ce “Ya ku muminai! Idan fasiki ya zo muku da labari, to ku nemi bayani, domin kada ku cuci wadansu mutane a cikin jahilci, saboda kada ku wayi gari a kan abin da kuka aikata kuna nadama” (Hujurat:6). Malamai suka ce, Allah ya yi hani da daukan maganar firgici da wani zai kawo har sai kun bincika, kun tabbatar da gaskiyar magana. Domin saboda tsoron munin abin da zai bayu sakamakon wannan magana, Allah ya ambaci mai kawo labarin; da fasiki. Fasiki shi ne dukkan wanda ya karkace daga hanyar kwarai, amma a nan, fasiki shi ne mai kai da labarin akwai tashin tashina a cikinsa, ko abin tsoro domin sanya rudu a tsakanin al’umma.

Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah S.A.W cewa: lokacin da aka yi sulhu da Kabilar Banil Musd’alik, da lokacin karbar zakka ya yi, sai Annabi S.A.W ya tura Alwalidu Ibnu Ukbah Ibn Abi Mu’aid’ domin ya karbo. Bayan ya tafi, sai ya labe a hanya bisa wani dalilinsa, ya dawo ya cewa Annabi S.A.W sun hana shi. Da Annabi S.A.W ya ji haka, sai ya hada rundunar yaki, domin a yake su sakamakon karya alkawari. To su kuma a can, suna jiran ganin wanda za a aiko domin sun hada dukiyarsu, kawai dan aike suke jira su ba shi. Da suka ji shiru, sai suka yi shawarar zuwa gun Annabi S.A.W da kansu. Sun taho Madina, su ma rundunar da Annabi ya shirya don su yake su, sun fito, sai suka yi kicibus, kowa ya labartawa kowa inda zai je. Nan take suka juya suka koma gun Annabi S.A.W, sai Allah ya saukar da wancan aya da na kawo.

Abin da nake so na ce da mu a nan shi ne, duk yadda kake ga kusanci ga mutum, a lokacin da ya zo maka da labarin hayaniya da firgici, kar ka yi gaggawar daukan zafi, kar ka nemi daukan fansa, a’a ka dakata, ka bincika ka ji gaskiyar lamari. Ai duk cikin mutanen da ke duniya, babu wanda ya kai Annabi S.A.W ilimi, hankali, sanin shari’a, kusanci ga Allah, son mutanenSa, amma tare da haka Allah ya saukar masa da aya wacce hukuncinta ya shafi al’umma gaba daya.

Daga cikin abubuwan dake gyara zukatan muminai, su tace su, su tsarkake su, su ne nesantar hassada da gaba da raini, da nesantar dukkanin wani hali na wus da tir da Allah wadai. Ubangiji ya gindaya mana sharudan da idan mun bi su, za mu tsira, Allah ya ce “Ya ku muminai! Kada wadansu mutane su raina wadansu, (kar su musu izgili, ko kallon hadarin ka ji, ko wulakanci), mai yiyuwa wadanda aka raina din su zamto su Allah ya fi kauna sama da masu rainin. Kar wadansu mataye su raina wadansu, mai yiyuwa wadanda aka raina su fi alheri sama da masu rainin. Kar ku aibanta juna! Kar ku rinka jifan juna da suna marar kyau (sunan da mutun ba ya so a kira shi da shi). Ya munana, kiran junan da sunan fasikanci bayan kuwa an yi imani! Duk wadanda ba su tuba ba, (ba su daina ambaton juna da sunan banza ba, ko kiran juna da mugunyar hali da rain ko izgili), to irin wadannan su ne azzalumai”. (Ahzab: 5). ku muminai! “Ya muminai! Ku nisanci abu mai yawa na zato, lalle zato laifi ne. Kada ku bi diddigin juna! Kuma kada sashenku ya yi gibar sashe. Dayanku zai so ya ci naman dan’uwansa musulmi bayan ya mutu, ya yanki naman ya ci yana mushe? Tabbas za ku ki haka, ba za ku so ba……”.

Cikin wadannan ayoyi, mun fahimci hatsarin raini ga wani, ko yi masa izgili, ko kiransa da sunan banza, sannan mun fahimci hatsarin munana zato, da bin diddigin gano laifin juna, da giba duk a tsakanin musulmai. Akwai zato karbabbe wanda idan mutum ya bude kofa a zarge shi, akwai kuma zaton da kawai mutum ne zai raya da tunaninsa, ba tare da mutum ya bude kofar a zarge shi ba. Manzon Allah S.A.W ya hana mu zato, Ya ce: “Na hana ku zato, domin zato shi ne mafi karyar labari”.

Yan’uwana, hakika Manson Allah S. A. W ya hana mu girman kai, Ya yi umarni da mu ki shi, kar mu zama masu yi.

Wannan kadan kenan daga cikin al’amuran da idan an nisance su, zukatan muminai za su gyaru, su dinku, su zama yan’uwan juna, su zama al’umma guda, su kauwala al’umma ta zamto tsintsiya madaurinki daya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: