Abba Ibrahim Wada" />

Haaland Zai Yi Kokari A Madrid – Xabi Alonso

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Xabi Alonso, ya bayyana cewa yakamata Real Madrid tayi kokarin sayan dan wasan gaba na Borussia Dortmund, Erling Braut Haaland.

A kwanakin baya ne dai aka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta gama shiryawa domin zawarcin dan wasan gaban wanda tauraruwarsa take haskawa a daidai wannan lokacin a duniya.

Kociyan kungiyar, Zinadine Zidane ne ya bada umarnin cewa yakamata shugaban gudanarwar kungiyar, Florentino Perez ya sayo masa dan wasan wanda tun bayan komawarsa Dortmund a watan Janairu ya buga wasanni 11 sannan ya zura kwallo 12 a raga.

Sai dai abune mai wahala kungiyar ta Dortmund ta rabu da dan wasan nata a karshen kakar wasa mai zuwa saboda tana ganin bata dade da sayan dan wasan ba kuma har yanzu matashi ne wanda bai kai shekara 20 ba har yanzu.

“Dole ne Real Madrid tayi iya yinta taga ta dauki Haaland idan har tana son ta dawo da kokarinta na shekarun baya saboda akwai matsalar dan wasan gaba wanda zai dinga jan ragamar kungiyar wajen zura kwallo a raga” in ji Alonso

Ya ci gaba da cewa “Ina girmama ‘yan wasan da suke kungiyar a yanzu amma suma sun san basa bawa kungiyar abinda take bukata kuma idan akwai wanda zai kawo sakamakon da ake bukata yakamata a kawo shi”

Tun bayan komawar Luca Jobic kungiyar a farkon wannan kakar har yanzu matashin dan wasan bai buga abinda yakamata ba wanda hakan yasa kociyan kungiyar yake ganin akwai bukatar ya sayo matashin lamba tara wanda zai maye gurbin Karim Benzema.

Farashin dan wasa Haaland dai fam miliyan 63 ne kamar yadda Dortmund din tayi masa kudi kuma tuni aka bayyana cewa banda Real Madrid akwai kungiyoyi irinsu Chelsea da Bayern Munchen wadanda suma za su shiga zawarcin dan wasan idan har ta tabbata a kasuwa yake

Exit mobile version