Gwamnan jahar Imo, Sanata Hope Uzodinma ya bayyana haka lokacin da yake karban bakwancin wata kungiyar mazauna kasar waje da suka shiraya taro kan ingantacen ilumi. Kungiyar mai suna UNESCO tare da UNIC sun ziyarci Gwamna Hope Uzodinma a fadar Gwamnati dake Oware.
Gwamnan ya ce babban aikin dake gabansa shine samar da ingantaciyyar ilumi ga al’umman jihar Imo.
Ya kara da cewa, an samu koma baya a bangaren ilumi bayan billowar annobar cutar Korona a Duniya wanda ta shafi Nijeriya harma da jihar Imo.
Ya ce, za mu yi kokarin samar da wasu cibiyoyin na musamman da za su rika bada ilimi a tasiwurar zamani idan aka samu makamancin Korona nan gaba.
Gwamnan ya shawarci al’umman jihar Imo da su kasance masu kulawa da dokokin yaki da yaduwar annobar cutar Korona.