Yayin da hutun bukukuwan ranar kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin da na tsakiyar kaka suke gudana, harkokin al’adu na al’ummar kasa, da zirga-zirgar ababen hawa da sabbin kirkire-kirkire a fagen yin sayayya sun zamo kyakkyawan madubin duba irin karfin juriya da ci gaban da tattalin arzikin kasar ke samu.
Hutun na kwanaki takwas, wanda ya fara a ranar 1 ga watan Oktoba, ya kunshi tururuwar mutane da yin sayayya wadanda ba a taba ganin irinsu ba a fadin kasar. Da misalin karfe 4 na asuba a ranar 1 ga watan Oktoba, tun kafin gari ya waye, dandalin Tiananmen ya cika makil da mutane. A wannan rana ta bikin ranar kafuwar jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, mutane 121,000 ne suka zuba ido a kan sandar daga tutar kasa, suna dakon lokacin da tutar kasar Sin za ta daga sama tare da fitowar rana lokaci guda.
Tsare-tsaren hanyoyin sufuri sun taka muhimmiyar rawa wajen saukaka kai-komon jama’a. A farkon rabin hutun, tafiye-tafiyen fasinjoji a tsakanin yankuna sun kai matsayi mafi girma da yawan kusan biliyan 1.25. Manyan titunan mota, layukan dogo, da hanyoyin ruwa da zirga-zirgar jiragen sama duk sun samu bunkasa a mizanin shekara-shekara, wanda ke nuna yadda sassan kasar Sin ke da kwakkwarar alaka da juna.
Manufofin da aka tsara sun karfafa kashe kudi. Kafin wannan hutu, gwamnatin tsakiya ta ware yuan biliyan 69 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 9.7 a matsayin lamuni na musamman don tallafa wa hada-hadar kayayyakin masarufi, wanda hakan ya kai ga jimillar abin da ake warewa a shekara ta kai yuan biliyan 300. Daga watan Janairu zuwa na Agusta, shirye-shiryen ba da tallafi na hada-hadar kasuwanci sun jawo hankulan masu nema miliyan 330, wanda hakan ya haifar da cinikin sama da yuan tiriliyan 2. (Abdulrazaq Yahuza Jere)