CRI Hausa" />

Habasha Ta Yaba Ci Gaban Babban Aikin Meskel Da Sin Ke Gudanarwa

A jiya Lahadi gwamnatin kasar Habasha ta yaba da irin ci gaban da aka samu na wasu muhimman ayyukan more rayuwa da kasar Sin ke gudanarwa a babban birnin Habasha, Addis Ababa.

Wannan yabo na zuwa ne a lokacin bikin nuna godiya da aka shirya domin yabawa kwarewar da ma’aikata Sinawa da ‘yan kasar Habasha dake aiki a kamfanin kasar Sin suka nuna wadanda ke aikin gina dandalin taro na Meskel, wanda a halin yanzu yake daf da kammalawa a tsakiyar birnin Addis Ababa, babban kamfanin gine gine na kasar Sin CCCC ne ke gudanar da aikin.
Adanech Abiebie, mataimakiyar magajin garin birnin Addis Ababa, ta yaba da irin ci gaban da aka samu wajen gudanar da aikin, ta kuma jaddada muhimmancin babbar gudunmawar da ma’aikatan kamfanin Sinawa da ‘yan Habasha ke bayarwa wajen tafiyar da aiki, inda ta ce suna sadaukar da dukkan lokacinsu da karfinsu babu kakkautawa, dare da rana, domin cimma nasarar kammala aikin cikin kankanin lokaci.
A cewar Abiebie, dandalin taron Meskel, wani muhimmin aiki ne na zamani da ake ginawa, kuma akwai wasu makamantansa dake tafe wadanda za a gudanar a birnin har ma da sauran sassan kasar ta gabashin Afrika.
Aikin gina dandalin taron na Meskel yana kumshe da muhimman bangarori da suka hada da katafaren wajen aje motoci na karkashin kasa wanda zai iya daukar ababen hawa kusan 1,400 a lokaci guda, akwai manyan allunan talla na LED guda shida, kamar yadda cibiyar bunkasa harkokin tallace tallace wato ECMDE, ta bayyana, wacce ita ce ta karbi bakuncin shirya bikin.
Tilahun Tadesse, babban jami’in cibiyar ECMDE, a nasa bangaren ya bayyana cewa, ana sa ran aikin zai baiwa helkwatar siyasar kasashen Afrika Addis Ababa, damar zama wani birni na zamani, kana zai samar da hanyoyin tattara kudaden shiga ta hanyar daga martaba wajen da kuma bunkasa yawon bude ido.(Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)

Exit mobile version