Connect with us

RAHOTANNI

Hada-Hadar Cinikin Dabbobin Layya A Kasuwanni A Borno Da Yobe

Published

on

LEADESHIP A YAU, ta leka yadda hada-hadar cinikin raguna ke gudana a jihohin Borno da Yobe, yayin da wakilin mu ya tattauna da dillalai da ma su sayen dabbobin a birnin Maidugurin jihar Borno da wasu kasuwanni a jihar Yobe, daidai lokacin da babbar Sallar layya ke gabatowa, don jin ta bakin bangarorin da abin ya shafa.

A zantawar wakilin mu a jihar Yobe da Mamman Aliya, dillalin raguna a kasuwar dabbobi ta garin Potiskum a jihar Yobe, ya sanar da cewa akwai dabbobin sai dai masaya ne su ka yi kadan. Ya ce tun ranar Lahadin da ta gabata, raguna biyu ne kacal ya sayar; daga cikin raguna 20 da ya kawo sayarwa a kasuwar.

A nashi bangaren kuma, shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi a kasuwar, Alhaji Audu Sarkin Gabari, ya ce kasuwar dabbobi a wannan shekara sai a hankali, ya ce, “Abu na farko shi ne saboda yadda kowane bangare, tsakanin mai saya da mai sayarwa kowa kuka yake, kuma burin kowa ya samu yadda yake so; burin mai saya samun arha, shi kuma mai sayarwa ya sayar da tsada.

“Abu na biyu, a wannan kasuwa ta mu akwai dabbobi amma cinikin ba kamar kowace shekara ba. Kuma gaskiya akwai bambancin farashin tsakanin bara da bana, kuma wannan ya zo ne dalilin yadda ake fama da matsalar tattalin arziki, wanda a da za ka tarar mutum daya zai saya wa sama da mutum 10 ragunan layya; bayan kanshi, amma a bana ta kan shi yake, ka ga ta nan an samu gibi kenan.

“Bugu da kari kuma, a bara za ka tarar yan kasuwar mu, mutum daya ya na da jarin hada-hadar kasuwancin dabbobi 50 zuwa 100; ya saya ya sayar, amma a wannan shekara dakyar yake iya juya jarin dabbobi 20 zuwa 30. Kuma wannan ya zo ne ta dalilin barkewar wannan annoba ta korona, ta jawo kusan kowa ya cinye jarin sa.”

Ya kara da cewa, a shekarun baya zuwa bara- kafin zuwan korona, a kowane mako; a irin wannan lokaci, su na tayar da motar raguna 20 ko fiye da hakan zuwa sassa daban-daban na kasar nan. Ya ce amma a bana dakyar su ke iya tayar da mota 10 zuwa 12 a mako.

Malam M. Tata, wani magidanci wanda wakilin mu ya yi kicibis dashi a kasuwar, ya zo sayen dabbar layya, ya ce a bana ya fi samun sa’ar cinikin dabbobin, fiye da shekarar da ta gabata.

A can jihar Borno kuma, shi kuma Alhaji Bako Kura, wani dillalin raguna a kasuwar dabbobi da ke bakin NTA a birnin Maiduguri, ya bayyana cewa a wannan shekara, ragunan sun yi tsada, ya ce hakan ya faru ne saboda karancin su, inda ya bayar da misali da cewa: ragon da ake sayarwa 50 a shekarar da ta gabata, a bana sai 60 zuwa 75.

Sannan kuma ya kara da cewa, “duk da yadda a wannan shekara babu kudi a hannun mutane, saboda yadda harkoki ba su gudana yadda ya dace, amma dai kuma ga ka dabbobin sun yi karanci kuma babu masu saya.”

Haka zalika kuma ya ce, ana shigo da dabbobin ne ta Damaturu, Gombe, Azare, Potiskum, da Taraba, kuma hakan ya na da nasaba da tabarbarewar tsaro wanda ya tagayyara gabashin jihar Borno, inda a da ta nan ne ake shigo da ragunan har su yi sauki kuma a kai wasu sassan kasar nan, yanzu babu kowa a wajen.” In ji shi.

Ya ce farashin raguna a wannan shekara ya na kamawa daga naira dubu 100 da wani abu, dubu 75, ko 65, wanda farashin matsakaitan raguna shi ne 60 zuwa 55 yayin da kananan ragunan ke kai naira 35,000.

Wani mai sayan ragunan; Alhaji Garba Ramadan a kasuwar, ya shaidar da cewa bana raguna ba za su tabu ba, saboda yanayin shigo da dabbobin zuwa birnin Maiduguri, al’amari mai nasaba ta matsalolin tsaro.

Ya ce, “Yanzu ka ga wadannan raguna guda biyu, na saya kowane dayan su naira 60,000. Sannan kuma a shekarun baya, kowace shekara raguna uku nake yanka wa ga Sallar layya, amma bana saboda yanayin tsada da karancin su, ya jawo biyun nan nake kokarin in yi layya da su.

“A ganina, abinda ya jawo hauhawar farashin dabbobin shi ne matsalar tsaro wadda ta jawo rufe kan iyakokin mu da kasashen makobta, wanda a shekarun baya ana shigo dasu ta hanyar Damasak daga Nijar, Gamboron- Ngala ta bangaren Kamaru. To amma ta dalilin tabarbarewar tsaro ya jawo rufe kan iyakokin, kuma wannan ya jawo tsadar su. Wanda idan an kwatamta farashin ragunan a bara da bana, ai akwai tazara mai nisa, kuma gashi ba su samu isasshen kiwo ba,” ya nanata.
Advertisement

labarai