Connect with us

NOMA

Hada Ilimin Gargajiya Da Na Zamani Na Samar Da Amfani Mai Yawa –Mansur Aliyu

Published

on

Alhaji Mansur Aliyu, shi ne shugaban kungiyar Hayin Dogo Ideal Multipopurse Cooporatibe Society Samaru Zariya, shi ne kuma Shugaban Samaru and Enbirons Solidarity Association (SESA) har ila yau shi ne Babban Sakataren United Hunters Society Abuja and Nasawara Branch, a halin yanzu ya na daya daga cikin manonan da su ka rungumi dabarun gargajiya da na zamani wajen ciyar da harkar noma gaba, wakilinmu Bello Hamza ya samu zantawa da shi domin amfanin masu karatunmu. Ga kuma yadda tattaunawar ta su ta kasance;
Za mu so ka gabatar mana da kanka ga masu karatunmu.
SunanaAlhaji Mansur Aliyu.

Shekararka nawa da fara noma?
Gaskiya tun muna ‘yan yara kananan da yake mun sami tarbiyya haka ne daga iyaye, ana zuwa da mu muna ganin yadda ake yi, zan iya ce maka na kai shekara arba’in da ‘yan wasu abubuwa.

Yaushe ka noman gadan-gadan?
To fara noma na gadan-gadan bai wuce shekara biyar ba cikakke, da yake ka san in ka mallakar gona ta kanka shi ne zai ba ka himman ka yi wasu ayyuka da zai sa ka kira kanka cikakken manomi.

Noman me ka fuskanta lokacin da ka fara cin gashin kanka?
Da yake gonata na gefen rafi ne, gaskiya na kan yi noman hatsi wanda ya kama daga dawa da masara da shinkafa sannan kuma in ka koma bangaren rani haka bayan mun cire amfanin gona, to nakan yi kabeji da tumatur da kuma albasa sosai.

Wane yanayin noma kake yi? Kana yin tsarin wanda aka gada kaka da kakanni ne ko kana sa wani salo na zamani?
E to ai da yake salo ne na zamani, aikin zamani sai da zamani. Musamman in an ce za a yi aikin kaka da kakanni ne misali ka ga da lokacin da iyayenmu suka nuna mana noman, ana amfani da garmar hannu ne, to amma yanzu an sami ci gaba aka koma ana amfani da garmar shanu to kuma akwai batun tantan. kowanne ta bangaren ita garmar shanu da kuma ita tractors ina amfani da su, saboda dole ne indai kana so ka cimma abin da ka ke bukata sai ka yi amfani da duka biyun.

Tun da ka fara noma ka taba samun wani tallafi ko ta hanyar basussuka da ake bayarwa a bankuna?
Da yake ka san duk abin da za ku yi imma kuna neman wani tallafi sai kun yi a kungiyan ce, to akwai kungiyar da na kafa, ana kiranta Hayin Dogo Ideal Multipurpose Corporatibe Society, wannan kungiyar a yankin karamar humar Sabongari da Giwa da cikin Zariya mu ne na farko wajen tsari. Gwamnati ta kan kira mu akan duk abin da ya taso na harkar ci gaban noma, misali mun sami tallafi na taki akan ba shi cikin farashi, na farko bara waccan shekarar 2016 an ba mu tallafi na taki, ni dai an ba ni tallafin taki da iri da maganin feshi da duk abubuwan da za mu bukata ka tsaye daga kamfani, tsarin shi ne idan mun girbe za mu mayar da hatsi ne ko kudi, to wannan ya taimakamin gaskiya ya bunkasa mani al’amurra, amma kuma daga baya gwamnati bata ci gaba da tsarin ba.

Ya kake ganin yanayin ka’idoji da ake gindayawa wajen samun wadannan tallafin, suna da sauki ko suna da wahala?
In har dai irin tsarin da na amfana ne gaskiya idan da yadda aka dakko an ci gaba a haka akwai cigaba kwarai da gaske, tunda kusan komai za a ba ka, in ka tsaya kuma ka bi ka’idar noman yadda ya kamata, to za ka ci riba ba karama ba shekara daya, tunda ka ga ka’idar hectare shi ne a wannan kayan da suka bamu indai an gyara shi yadda ya kamata to a duk hectare ba za ka ka samu kasa da buhu hamsin ko zuwa sittin, irin masarar yana da kyau to ka ga misali kuma in ka cire za ka mayar musu da buhu shabiyu ne, kuma ba ko kwabon ka a ciki, to a cikin buhu sittin ka samu buhu sittin, an baka kudin noma, an baka kudin sharar gona an ba ka kudin duk abin da za ka yi an ba ka taki an ba ka komai da komai ai akwai riba sosai, saboda a cikin buhu sittin ko hamsin ka cire buhu goma sha biyu ka ba gwamnati ka ajiye sauran ai ka ci riba.

Wane kira kake da shi ga gwamnati na su ci gaba da wannan shiri tunda kun sami amfani da shi?
To gaskiya ina kira ga gwamnati da ta farfado da shirin, to amma matsalar da aka samu shi ne wajen cika alkawari daga bangare manoma, gwamnati ta yi kokari a lokacin nan, ta ba jama’a to amma wajen biya sai ya zama an sami matsala, kuma na tabbatar in da jama’a sun bada hadin kai sun mayar wa da gwamnati yadda ya kamata to za a ci gaba, to amma da aka samu mastala a wancan lokacin sai basu ci gab aba, amma da a ce mutane za su rika ba da wa, saboda abin da na ke so ka gane akwai wadanda aka basu kayan, sai suka dinga diba suna sayarwa, wani na kara aure ya yi wani na sayen mashin ya yi, to ka ga kuma ka sayar da kayan da aka ba ka ba ka yi amfani da shi ba, to kuma ranar biya fa? Ai ka ga dole a samu matsala, to amma ka ga kayan da aka ba ka ka yi amfani da su yadda ya dace ba za ka samu matsala wajen biya ba, za ka iya fitar da komai da komai ka biya. Saboda haka ina kira ga gwamnati da za ta yi hakuri ta daure saboda ita gwamnati uwa ce kuma uba ce.

Wane matakin gwamnati ne ta ba ku wannan tallafin?
Lallai daga jihar Kaduna ne a yadda aka gaya mana, saboda shirin na KADP ne, lallai da za a dawo da shi saboda gwamnati sun ce shiri ne na taimakon talakawa, masu son ayi harkar noma, tun da arziki ne sosai, to gaskiya tsakani da Allah in aka dawo da wannan shirin a dauki tsatstsauran mataki sosai a tabbatar da cewa jama’a sun yi amfani da kayayyakin da aka ba su a lokacin da ya kamata za a samu ci gaba.

Wane kira kake da shi ga manoma?
Zan ba su shawara ta gare su shi ne su rike kungiya da kyau, sannan in kun yi amfani da kungiya kun anso kayayyaki daga gwamnati to ku yi kokari ku mayar musu a yadda ya kamata kuma a kan lokaci..

Mun gode
Ni ma na goode
Advertisement

labarai