Connect with us

RA'AYINMU

Hada Kai Don Yaki Da Matsalar Tsaro

Published

on

A halin da a ke ciki yanzu a Najeriya, babban abinda ya fi firgitawa da saka fargaba a zukatan ’yan Najeriya shi ne kisan kiyashi da satar mutane da garkuwa da jama’a, domin a yanzu fargaba kan annobar Korona ta fara kwaranyewa daga zukatan al’umma, duk da cewa, a yanzu ne ma a ka fi samun bullarta. La’alla hakan ba zai rasa nasaba da yadda batun annobar ya ki ci ya ki cinyewa ba. Don haka mutane har sun fara saba rayuwa da ita da kuma jin bayanai a kanta, amma lamarin tsaro ya sha bamban da na Korona. Lamarin ya yi ta’azzara da ko a cikin gidaje mutane su na cikin fargabar za a iya zuwa a dauke su.

Duk da cewa, jami’an tsaro su na yin iyaka bakin kokarinsu ta hanyar kama da dama daga cikin masu garkuwa da mutanen, to amma kasancewar abin bai lafa ba har yanzu, illa ma ta’azara da ya ke kara yi, fargabar ba ta kau ba.
Babban abin lura shi ne, lamarin ya na shafar tattalin arzikin dukkan al’ummar kasar da yanayin tafiyar da rayuwarsu ba tare da bambancin kabila, yare ko yankinsu ba. To, amma wani babban hatsari da ya mamaye wannan batun matsalar tsaro ta garkuwa da mutane shi ne, shigo da batun kabilanci ko yanki. Da yawan wasu na zargin wata kabila guda daya da aikata irin wannan ta’addanci. Don haka maimakon su rika zargi da sukar ainihin aikata laifin, sai su ka bige da sukar wannan kabila da su ke zargi, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya, inda a ke samun kashe-kashe tsakanin manoma da makiyaya, sabanin yankin Arewa maso Yamma, inda ba a samun irin wannan zargi na kabilanci, domin kisa duka kisa ne.
Illar hakan ita ce, duk lokacin matsala ta shafi wata kabila, to a hankali za ta gangaro ta shafi addinin da mafi yawan wannan kabila su ka fi imani da shi. Shi kuwa rikici idan har ya shafi addini, to ya kan kasance babbar matsalar da za ta iya rasa karshe. Ma’ana; za a iya kasa kawo karshen matsalar kenan.
kwararru da masana sun tabbatar da cewa, danganta lamarin da kabilanci ta kowacce ko yanki babban hatsari ne da ke fuskantar kasar. Balahirar Boko Haram kadai ta ishe mu ishara a Nijeriya. kwararrun na da ra’ayin cewa, hada hannu waje guda, don shawo kan lamarin shi ne abu mafi muhimmanci, maimakon zargin juna, domin hannu da yawa shi ne maganin kazamar miya.
Don haka LEADERSHIP A YAU ke kira ga masu ruwa da tsaki a cikin batun matsalar tsaron al’umma, musamman malamai da limaman addinai daban-daban, da su kawar da bambance-bambancen da ke tsakani da kuma son kai ta hanyar assasa gaba da kiyayya a tsakanin mabiya addinan, su bai wa jami’an tsaro dukkan hadin kan da su ka kamata, don kawo karshen wannan gagarumar matsala da za ta iya halaka kowa a kasar kuma matsalar da ta hana kowa rayuwa cikin nutsuwa da inganci ba tare da la’akari da addininsa ko kabilarsa ba a tsakanin al’ummar kasar.
Kasancewar mutum a kowane irin addini ko kabila ya ke, ba zai hana ya amfana da zaman lafiya ba, haka nan kuma ba zai hana ya cutu da rashin samun zaman lafiya ba. To, ashe kenan taimaka wa wajen tabbatarwa da wanzuwar zaman lafiya a cikin kasa shi ne abinda ya wajaba a kan dukkan masu ruwa da tsari da kuma sauran al’umma.
Irin tashin hankalin da mutane ke tsintar kansu a ciki a duk lokacin da a ka yi garkuwa da wani mutum, ba wai kawai na irin makudan kudin da a ke biya ba ne da sunan biyan diyya ko fansa, a’a, fargabar ta kan iya biyo baya har bayan an sako wadanda a ka kama din da danginsu bakidaya. Wasu ma tun daga lokacin ba su sake iya sake dawo wa daidai a rayuwarsu, saboda jikkata da su ka yi ko kuma wani ciwo da ya kama su. Wasu kuwa ba ma sa samun nasarar kubuta da rayuwarsu.
Mu na masu bayar da shawarar cewa, ya kamata a kowane mataki a bayar da umarnin samar da wata tawaga tun daga matakin tarayya har zuwa jihohi, kananan hukumomi da unguwanni, don gudanar da aiki tukuru, saboda a kawo karshen matsalar. Nuna wa juna yatsa da zargin juna ba su a ke bukata ba a wannan gaba kuma hakan ba komai zai haifar ba illa ya sake ruruta wutar rikicin.
Hakkin gwamnati ta tabbatar da cewa ta kare rayuka da dukiyoyin al’ummarta a kowane mataki. To, amma hakan zai yiwu ne kawai tare da hadin kan al’ummar kasa, musamman masu ruwa da tsaki a kan batun da ya taso.
Tilas ne gwamnatoci a kowane mataki tun daga na tarayya, jihohi da kananan hukumomi su tashi tsaye wajen ganin su na daukar matakan dakile barnar tun kafin ta afku; ba wai kawai sai bayan fitinar ta afku ba a bazama kokarin shawo kanta.
Hakika matukar a na barin barnar ta na afkuwa, sannan a maganta ta, to zai yi wahala a kawo karshenta. Su kuma sauran masu ruwa da tsaki, kamar malaman adduni da na gargajiya, wajibinsu ne su shiga iya wuya wajen ganin sun wayar da kan mabiyansu da al’ummarsu tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai, don a gudu tare a tsira tare. Allah ya sa mu dace! Amin summa amin.

Advertisement

labarai