Sulaiman Bala Idris" />

Hadaka Wurin Aikata Barna (Organized Crime)

Yau zan fara ne da bayar da hakuri ga masu karatu, dangane da rashin samun damar wallafa sakonninku, wanda ba da gangan nake yi ba, sai domin wasu dalilai kwarara; amma nan ba da jimawa ba, zan fara kawo ra’ayoyi da kuma karin bayani, har da martani dangane da maudu’an da na ke sharhi akansu.

A wannan makon zan takaita zantuka na ne a kan wani bangare na nazarin masana a fanin ilmin kimiyyar sanin halayyar jama’a da zamantakewa (Sociology). Inda na kudurci aniyar kokartawa don baje wa mai karatu yadda ake hada karfi da karfe wurin aikata barna, domin amfaninmu bakidaya.

Wannan wani bangare ne na barna, wanda kuma ake matukar ba shi muhimmanci a duniyar ilmin kimiyyar sanin halayyar jama’a da zamantakewa (Sociology). Domin kuwa a na taka muhimmiyar rawa da shi wurin cutar da al’umma.

Abin da ake nufi da hada karfi da karfi wurin aiwatar da barna shi ne tarayyar mutum sama da daya wurin saba doka da oda. Ko da kuwa ya kankantar laifi yake, matukar an samu gamayyar mutum sama da daya, to ya zama ‘Organized crime’.

Ban da wannan kuma, akwai laifinku da babu yadda za a yi mutum daya tilo ya iya aikata su, dole ne sai ya nemo wasu mutane wadanda za su taimaka ma shi kafin ya aiwatar da barnar da ya ke so.

Misalai da zan zayyano su ne za su yi karin haske ko manuniya dangane da abin da na ke nufi. Kuma wani abu ne da ya kamata kowanne mutum ya san da zaman shi, ta yadda idan ka ga an aikata wata barna ka san a wane sahu take.

Cikin misalan laifukan da sai an bukaci taron jama’a shi ne fashi. Bai taba yiwuwa a aiwatar da fashi ba tare da an samu taruwar jama’a ba ‘Team’. Idan za a yi fashi a banki, dole ne sai wadanda za su yi fashin sun kai daga mutum biyu zuwa sama. Kuma a cikin ‘yan shirya yadda za a yi fashin cikin nasara, sai ya kasance akwai wani ma’aikacin bankin ko kuma wanda ya san ciki da wajen bankin (sirrin bankin). Sannan sai an samu wanda shi aikinshi kawai kwarewa a tukin mota, haka akwai wanda ya kware a iya harba bindiga, dole ne kuma sai an samu gwani a harkar kiwon lafiya da sauransu. Kowanne muhimmin abu da ake bukata, sai an samar da wanda ya kware a kansa kafin a cimma nasara. Babu yadda za a yi a yi fashi a banki har a kai ga cin nasara ba tare da samuwar wadannan jerin gwanaye ba. don suna yin aiki ne a kungiyance. Kuma kowanne yana da aikin da aka tanadar mashi, wanda zai yi.

Wani karin misali shi ne batun safarar hodar iblis. Shi ma wannan wani samfuri ne na barna wanda idan za a yi shi dole ne sai an samu mutum biyu zuwa sama. Kamar idan za a shigo da hodar daga kasar Nijar zuwa jihar Kaduna. Dole ne zai zama akwai shugaba wanda ya aiko da hodar Iblis din, kuma kowacce marrarabar hanya sai an sa mutum daya wanda aikinshi kawai ya tabbatar da hodar ta wuce cikin nasara, kamar daga Nijar idan ta shigo Katsina akwai wani ko wasu da ke aikin lura da tabbacin fitar hodar, idan wanda yake dauke da hodar ya karasa Kudan ko Hunkuyi, nan ma dole a samu wani wanda yake zaman tabbatar da an shigar da hodar Kaduna lafiya ba tare da wani tarnaki ba.

Idan kuma aka samu bacin rana, ‘yan sanda suka cafke wanda ke dauke da hodar a kan hanya, nan da nan za su yi waya a tsakankaninsu, kafin wani lokaci za su hadu a ofishin ‘yan sandan da aka kama musu kaya. Kuma za su je ne a matsayin masu kayan da aka kama. Masu safarar hodar iblis sun fi kowanne kungiya ta hada karfi da karfe wurin aikata barna karfi da sanayya a duniya. Sannan sun fi kowacce kungiyar mabarnata gaggawa wurin daukar mataki idan rana ta baci mu su.

A Nijeriya, wani karin haske dangane da hadin karfi da karfe wurin aikata barna shi ne yadda ‘yan siyasa su ke amfani da ‘yan daba ko sara-suka wurin cimma muradunsu na siyasa, wadanda ake turawa su halaka abokin hamayya.

Irin na ‘yan siyasa, ana iya aika mutum daya wurin aikata barna, amma shima wanda aka aika din akwai wani dan ta’addan da aka tanada wanda idan ya nemi ya fallasa asiri ko kuma ya saba da wanda ya sa shi aikin sai ya kashe shi.

Hatta satar rashin hankali da a ke yi kullum a Nijeriya, tana iya shiga cikin jerin hada karfi da karfe wurin aikata barna ‘organized crime’, domin daga wannan ofishin zuwa wancan ofishin zuwa wancan har a iya fitar da kudin. Wannan kuwa a walau a gwamnatance, ko a kasuwanni, ko a mu’amalar daidaikunmu.

Exit mobile version