Ibrahim Muhammad" />

Hadakar Kungiyoyi A Jihar Kano Sun Nemi Gwamnati Ta Rusa Sabbin Masarautu

Hadakar kungiyoyi da daidaikun mutane yan kasuwa da ma’aikata da masu sana’oi masu kishin ci gaban al’umma sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje a kan ta girmama umurnin kotu da bukatar al’ummar jihar Kano na neman dakatar da sabbin masarautu data kirkiro da ba zai amfani ci gaban al’ummar jihar ba.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin daya daga cikin shugabannin hadakar kungiyoyin, wanda ya yi bayani a madadinsu Kwamared Ibrahim Waiya da yake zantawa da wakilimmu. Ya ce, ya kamata Gwamnatin Kano ta duba halin da al’ummar Kano suke ciki na koma baya da irin tarin dinbin almajirai da take dasu a nemo hanyar da za a kyautatawa rayuwarsu da kuma dakile matsalar shaye-shaye da ya yi katutu a tsakanin matasa da inganta harkar lafiya da sauran fannoni na ci gaban rayuwa maimakon a tsaya ana maganar kirkirar masautu da ba abin da za su haifar sai kawai rarraba kan al’ummar jihar Kano.
Kwamared Ibrahim Waiya ya musanta zargi da ake na cewa kungiyoyin nasu da suke fafutukar rashin nuna goyon baya ga samar da sabbin masarautu da cewa, wasu ne ke sasu da cewa ba haka bane, hasalima su basu da wata alaka da wani ko wasu, su dai haduwa ce ta kaunar ci gaban al’ummar Kano duba da cewa masarautar Kano tun shekaru daruruwa da suka gabata abu guda ne kuma suna hada kan al’umma da kyautata tarbiyyar al’umma ta hada kansu da zaman lafiya.
Ya ce, su a matsayinsu ma basu da wata alaka da masarauta batu ne na ceto al’ummar Kano domin kangeta daga rarraba da rugujewa da ake nema a haifar mata don a ruguje irin tasiri da daukaka da mutuntaka da take da ita, Don haka wajibi ne a kansu su tashi tsaye domin kare martabar Kano masarautarta da kuma mtuncin al’ummarta.
Kwamared Ibrahim Waiya ya ce, duba da irin matsin rayuwa da ake dashi bai kamata a dauki kudaden al’umma a zuba domin yin masarautu da sai an kashe makudan kdade wajen tafi dasu kama daga dawakai, motocin alfarma da kuma gidaje da kayan alatu da za’a sanya musu bayan a gefe guda akawai dinbin ayyuka na ceton lafiya da habaka tattalin arzikin al’umma daya kamata ayi dasu.
Ya ce, manufar wannan hadaka tasu shi ne fitowa don nuna rashin amincewa da duk wani abu da ake a jihar Kano da bai dace da kawo ci gaba a al’umma ba, saboda a baya sun yi sakaci ana abin da baida anfani ga al’umma da yake cutar dasu, don haka suka fito suke wannan fafutuka don ceto al’ummar jihar Kano wanda ya kamata ace duk wata Gwamnatai ta tsaya a kan muranda da al’umma suke so da zai kawo ci gabansu ba abu na son rai ba.
Kwamared Ibrahim Waiya ya ce, duba da yanda cikin yan kwanaki aka kirkiri doka har aka sanya hannu da sunan kirkiro masarautu hakan ya saba ka’ida domin an watasarda bukatun neman yardar al’umma anzo da wani abu da bazai zama mai anfani ga jihar Kano ba. Abin da suke bukata ga Gwamnatin Kano shi ne a samu fahimtar juna tsakaninta da masarauta a janye wannan sabbin masarautu Gwamnati kuma ta nemi afuwar kuskuren da tayi wa al’ummar Kano.
Wasu daga cikin mutane a hadakar kungiyoyin suma sun yi kira ga Gwamnati ta mutunta doka ta janye wadannan masarautu abar masarautar Kano a yanda take don ci gaba da mutunta al’adunta da hadin-kan al’ummarta kamar yanda aka sani.

Exit mobile version