Connect with us

LABARAI

Hadarin Jirgin Ruwa Ya Ci Ran Mutum Shida A Neja

Published

on

Mutane tara da suka hada da wata mai ciki ne suka mutu a kauyan Shata Sabo, da ke karamar Hukumar Shiroro, ta Jihar Neja, jiya a kan hanyar su ta zuwa kasuwa domin su sayar da kayayyakin gonan su.

LEADERSHIP A YAU, ta nakalto cewa, Jirgin yana dauke ne da mutane 10 da suka hada da matar mai ciki, Jirgin ya jirkice ne a lokacin da ake tsula ruwan sama da tsakar ranan a yankin wanda ke kan iyaka da karamar hukumar Bosso, ta Jihar.

An bayar da labarin cewa, mutum guda ne kadai ya sami tsira cikin mutanan da suke cikin Jirgin su goma, rafin wanda daya ne daga cikin hanyoyin babban rafin Kaduna, wanda ke dauke da babban Dam din samar da hasken lantarki na Shiroro.

Babban daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Neja, Alhaji Ibrahim Ahmed Inga, ya tabbatar da faruwan lamarin ga jaridar LEADERSHIP A YAU, ya kara da cewa, tuni hukumar ta aike da masu ceto domin su nemo sauran gawarwakin da suka nutse.

Da yake amsa tambayar, ko ana da tabbacin duk wadanda suka nutsen sun mutu ne, sai ya ce, yawanci dai a irin hakan, in har mutum ya nutse na awanni uku, ya kamata ka san cewa wannan mutumin ya mutu ne, amma dai masu binciken namu suna wajen, za mu sami bayani daga gare su in sun kammala.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: