Connect with us

LABARAI

Hadarin Mota A Saudiyya: Shugabannin APC 3 Na Jihar Zamfara Sun Mutu

Published

on

Da safiyar Juma’ar jiya ne aka samu rahoton afkuwar wani mummunan hadari a kan hanyar Makka zuwa Madina da ke kasar Saudiyya wanda ya yi sanadiyyar rasuwar Alhazai uku daga jihar zamfara.

Alhazan sun rasu ne  bayan tafiyar kimanin kilomita 120 a kan hanyarsu ta zuwa Madina daga Makka kamar yadda  babban jami’in kula da lafiyar Alhazai na Hukumar kula da aikin Haji ta kasa (NAHCON) Dakta Ibrahim Kana ya bayyana.

Dakta Kana ya ci gaba da cewa, sunan da jami’an kula da lafiyar suke da su na wadanda suka yi hadarin su ne: “Shinkafi Mudi  Mallamawa, namiji, shekarar haihuwa 10/02/1952,Lambar fasfo: A09413309; Abdullahi Jafaru Gidan Sambo, namiji, Shekarar haihuwa 03/07/1956, lambar fasfo: A09413813; da kuma Abdullahi Shugaba, namiji, shekara haihuwa 22/05/1963,lambar fasfo: A50080535.”

Babban jami’in kula da lafiya na Hukumar  NAHCON  ya bayyan cewa tuni suka tura jami’ansu zuwa wurin da wannan ala’amari ya faru “an dauke gawawwakin guda uku zuwa “King Fahd Hospital” da ke Madina, su kuma sauran wadanda suka ji raunuka an bar su a wani asibiti kusa da in da suka yi hadarin.”

Mataimakin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Zamfara Abdulrazak Kaura wanda shi ma yana  daga cikin wadanda suka je aikin Hajin na bana ya tabbatar da cewa Alhazai ukun da suka rasu dukkaninsu shugabannin jam’iyyar APC ne a kananan hukumomin da ke jihar Zamfara.

Ya ce, marigayi Jafarau Gidan Sambo shi ne shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Kaura Namoda sai Mudi Mallamawana karamar hukumar Shinkafi da kuma Abdullahi shi kuma shugaban jama’iyyar APC na Ruwan Dorowa da ke karamar hukumara  Maru. 

Wadanda suka tsallake daga hadarin kamar yadda ya ce su ne Nasiru Anka daga karamar hukumar Anka,da Tafa Nasarawa Bukkuyum  daga karamar hukumar Bukkuyum da kuma Garba Ziti shi kuma daga karamar hukumar  Gummi.
Advertisement

labarai