Hadarin Mota Ya Ci Rayukan ’Yan Rakiyar Amarya 22 A Katsina

Hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutane 22 a sanadiyar wani hadarin mota da ya afku a gadar jere da ke cikin karamar hukumar Kafur da ke Jihar Katsina.

Kakakin hukumar Abubakar Usman ya ce hadarin ya afku ne a dai dai gadar jere inda motoci guda biyu kiras J5 suka yi taho mu gama anan take mutane 22 suka rasa ransu a ya yin da mutane 11 suka samun munanan raunuka.

Ya kara da cewa tuni wadanda suka samu raunuka jami’an ‘yan sanda suka kai su baban asibitin Malunfashi domin yi masu magani wadanda suka rasa rayukansu kuma tuni akan yi jana’izarsu kamar yadda addini Musulunci ya tanada.

“kamar yadda na yi bayani motoci ne guda biyu kiran J5 inda suke dauke da mutane 36 wasu daga cikinsu sun dauko amarya ne za a kaita gidan miji wannan hadari ya faru, sai dai amarya da direbanta na daga cikin mutane uku da suka tsira daga wannan hadari” inji shi.

Kazalika ya kara da cewa mafiyawan wadanda wannan hadari ya rutsa da su mata ne da kuma kananan yara da suka rako amarya zuwa gidan mijinta, ya kara da cewa tuni aka yi jana’izar wadanda su ka rasu kuma a ka kasa gane su, sauran kuma an mika su zuwa ga iyalansu da ‘yan uwansu.

Exit mobile version