Kimanin mutane goma ne suka rasa rayukansu yadda sama da wasu mutanen goma sha biyu suka raunata sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya afku a garin Majiya titin zuwa hadeja da ke karamar hukumar Tauran jihar Jigawa.
Kakakin hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Jigawa malam Adamu Shehu ya tabbatar da afkuwar wannan al’amari a yayin zantawarsa da manema labarai a birnin Dutse.
Ya ce, hadarin ya farune tsakanin wata mota mai lamba ZY 749 AGL kirar Hilud mallakar gidan Radiyon Wazobiya da kuma wata mota kirar Sharon mai dauke da lamba GWL 262 ZA.
Haka kuma ya bayyana cewa, duk da cewar har yanzu ana cigaba da binciken musabbabin afkuwar al,amarin, amma wasu wadanda al’amarin ya faru akan idonsu sun ce hadarin ya afku ne sakamakon gudun zarta ka’ida da motocin biyu ke yi.
Sannan ya kuma ce, hadarin ya afku da misalin karfe sha daya da rabi na safiyar Alhamis din makon yadda nan take mutane goma suka rasu a lokacin.
Kakakin ya karada cewa, bayan jami’ansu sun sami labarin wannan al’amari sun garzaya zuwa wajen yadda tareda tallafin matasan yankin suka yi jigilar kwashe masu hadarin zuwa Babban Asibitin Ringim dake jihar ta Jigawa.