CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home DAGA BIRNIN SIN

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ya Ingiza Hadin Kan Sin Da Kasashen Gabas Da Tsakiyar Nahiyar Turai

by CRI Hausa
February 10, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
1 min read
Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ya Ingiza Hadin Kan Sin Da Kasashen Gabas Da Tsakiyar Nahiyar Turai
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron koli na Sin da kasashen gabas da tsakiyar Turai wato taron China-CEEC ta kafar bidiyo a jiya Talata tare da ba da jawabi. Cikin jawabin, Xi Jinping ya ba da shawarwari game da hadin kan Sin da kasashe 17 na wadannan yankuna, tare da gabatar da jerin muhimman matakai.
A cewarsa, sanin kowa ne, cikin dukkan dandamalin da Sin ta kafa, ci gaban wannan dandali na hadin kan Sin da kasashen gabas da tsakiyar Turai da aka kafa a shekarar 2012, ya fi jan hankalin mutane duk da cewa ba a dade da kafa shi ba.
Shugaba Xi ya ce, dandalin ya samu bunkasuwa mai kyau saboda dabaru guda 4, wato shawarwari da ake yi tsakanin mambobin da neman amfanawa juna da cin moriya tare, da kuma samun ci gaba ta hanyar bude kofa ga sauran kasashe da hakuri da juna, har ma da kirkire-kirkire ba tare da tsayawa ba da sauransu. Ya kara da cewa, ana iya ganin cewa, wadannan dabaru sun dace da manufar da Sin ta dade tana dauka na gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban da hadin kai da cin moriya tare. Shi ya sa, a ka kai ga cimma nasara a wannan fanni.
Shugaban ya ce a halin yanzu dai, Sin da wadannan kasashe na kokarin magance cutar COVID-19 da farfado da tattalin arizkinsu, don haka ana matukar bukatar hadin kai a tsakaninsu. Ya ce takardun hadin kai tsakanin gwamnatoci 35 da takardun hadin kai a fannin kasuwanci 53 da kuma jadawalin Beijing na hadin kan Sin da kasashen gabas da tsakiyar Turai na shekarar 2021, dukkansu, ci gaba ne da aka samu a cikin wannan gaggarumin dandali. (Amina Xu)

SendShareTweetShare
Previous Post

Zimbabwe Za Ta Karbi Tallafin Rigakafin COVID-19 Daga Kasar Sin Cikin Mako Mai Zuwa

Next Post

Kotu A Kano Ta Tsare Uwar Gida Kan Kisan ‘Yar Aikinta

RelatedPosts

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

by CRI Hausa
10 hours ago
0

Daga Bilkisu Xin A ranar 8 ga wata, ma’aikatar kasuwanci...

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

by CRI Hausa
10 hours ago
0

Daga CRI Hausa Tsohon Jakadan Italiya a kasar Sin, Alberto...

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

by CRI Hausa
10 hours ago
0

Daga CRI Hausa Kwalajin nazarin harkokin Afirka na kasar Sin,...

Next Post
Kotu A Kano Ta Tsare Uwar Gida Kan Kisan ‘Yar Aikinta

Kotu A Kano Ta Tsare Uwar Gida Kan Kisan 'Yar Aikinta

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version