Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Hadin Kan Dukkanin Sassa Ne Kadai Hanya Ta Kawo Karshen Cutar COVID-19

Published

on

A ranar Laraba 17 ga watan nan na Yuni ne, aka gudanar da taron musamman na Sin da kasashen Afirka, game da hadin gwiwar yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

A jawabin da ya gabatar yayin taron da ya gudana ta yanar gizo, wanda kuma kasar Sin ta karbi bakuncinsa, shugaban kasar ta Sin Xi Jinping, ya bayyana gamsuwa game da yadda kasar Sin da kasashen Afirka suka dage wajen tunkarar kalubale daban daban cikin hadin gwiwa, da kawance da amincewa da juna, a gabar da ake tunkarar wannan annoba ta COVID-19.
Ko shakka babu, kalaman shugaba Xi na kunshe da wasu muhimman sakwanni, dake tabbatar da fa’idar hadin gwiwar Sin da Afirka, duba da yadda ya jaddada aniyar kasar sa, game da ci gaba da tallafawa nahiyar a fannin yaki da wannan cuta. Ana iya kara fahimtar hakan, a gabar da shugaba Xi ya bayyana cewa, da zarar Sin ta cimma nasarar samar da alluran rigakafin cutar COVID-19, kasashen Afirka za su kasance a sahun gaba wajen cin gajiyar wannan rigakafi.
Hakika wannan labari ne mai faranta rai ga kasashen Afirka, musamman ganin cewa da yawa daga kasashen nahiyar na da rauni a fannin tsarin kiwon lafiya, wanda ke bukatar tallafin gaggawa, musamman a wannan lokaci da ake fama da yaduwar cutar a yankunan nahiyar daban daban.
Kari kan haka, Sin ta alkawarta yafewa wasu kasashen nahiyar basussuka marasa ruwa, wadanda bisa ka’ida za su biya a wannan shekara ta 2020, karkashin tsarin aiki na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC.
Har kullum, mahukuntan Sin na jaddada muhimmancin hadin gwiwar dukkanin kasashen duniya, wajen shawo kan kalubalolin dake addabar bil Adama, hakan ne ma ya sa a lokacin da yake jawabi yayin wannan taro na ran 17 ga wata, shugaban kasar Sin ya nanata gamsuwa game da yadda Sin da kasashen Afirka suka nace wajen yin aiki tare, ta yadda za a wanzar da hadin kai, da kawance, da kara yarda da juna, a gabar da COVID-19 ke zama “kadangaren bakin tulu” ga ci gaban kasashen duniya. Tallafin da Sin ta samar a wannan bangare ya isa misali na kudurin ta, game da tallafawa kasashen na Afirka wajen cimma nasarar wannan manufa.
A zahiri take cewa, kasashen duniya ba kawai masu tasowa kadai ba, har da ma manyan kasashe masu karfin tattalin arziki, na shan fama da cutar COVID-19, cutar da ta harbi sama da mutane sama da miliyan 8, ta kuma hallaka sama da mutum dubi 450. Ashe ke nan a irin wannan gaba, alkawarin da Sin ta yi na ci gaba da goyon bayan ayyukan hukumar lafiya ta duniya WHO masu nasaba da yaki da cutar, da tallafawa kasashen Afirka da kayan kariya, da na kandagarkin cutar, da tura tawagogin kwararru, zuwa ga sassan nahiyar, matakai ne da suka cancanci yabo.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, kasar Sin ta alkawarta samar da kudi da yawansu ya haura dalar Amurka biliyan biyu cikin shakaru biyu masu zuwa, domin tallafawa ayyukan hukumar ta WHO na yaki da wannan annoba. Wadannan kudade ko shakka babu, za su taimaka wajen cike gibin kudade da WHO ke bukata, wajen inganta ayyukanta.
Baya ga haka, karkashin manufofin hadin gwiwar Sin da Afirka, Sin ta alkawarta gaggauta ginin helkwatar cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka cikin wannan shekara, aiki da ake fatan zai taimakawa nahiyar cimma nasarar inganta tsarin kiwon lafiya, da dakile yaduwar cututtuka a dukkanin nahiyar, aikin da zai gudana karkashin kudurorin da Sin da Afirka suka amincewa, lokacin taron hadin gwiwar sassan biyu na FOCAC, wanda ya gudana a birnin Beijing. Kari kan hakan, Afirka za ta ci gajiyar asibitocin sada zumunta na Sin da Afirka, da hadin gwiwa tsakanin asibitocin Sin da na kasashen Afirka domin musayar kwarewa da kwararru.
Tun barkewar cutar COVID-19, Sin ta aike da tawagogin kwararru a fannin kiwon lafiya sama da 50 zuwa kasashen Afirka, kana kasashen nahiyar sun karbi tallafin nau’oin kayayyakin kandagarkin cutar daga Sin, karkashin inuwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, tare da bayyanawa kwararrun nahiyar irin kwarewa da dabaru da ta samu wajen kandagarki, da jinyar masu fama da cutar, yayin taruka daban daban da aka shirya ta kafar bidiyo.
A nasu bangare, jagororin kasashen Afirka da suka halarci taron na ran 17 ga wata, ciki hadda shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da na kasar Senegal Macky Sall da dai sauran su, sun bayyana gamsuwa game da sakamako mai armashi da ake samu, karkashin ayyukan dandalin FOCAC na hadin gwiwar Sin da Afirka, ciki hadda ayyukan tallafi na baya bayan nan, masu tarin yawa da Sin ke aiwatarwa, na agazawa nahiyar a fannin yaki da wannan cuta da ta addabi duniya.
Kalaman wadannan shugabanni na kasashen Afirka a wannan gaba, na dada tabbatar da irin kyakkyawan tasiri da hadin gwiwar sassan Sin da na Afirka ke haifarwa ga al’ummun su. Yana kuma kore zarge zarge da wasu kasashen yamma ke yadawa, cewa Sin na shiga kasashen Afirka ne domin cimma moriyar kashin kai. Idan ma muka yi duba na tsanaki kan wannan gajeren bayani, muna iya ganin cewa, kasashen Afirka ne ke kan gaba, wajen cin gajiyar tarin tallafi da Sin ke samarwa sassan duniya daban daban.
Baya ga shugabanni daga kasashen Afirka, babban sakataren MDD Antonio Guterres, da babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom, sun halarci taron ta kafar bidiyo.
Ko shakka babu, jagororin kasashen Afirka da al’ummun su, da hukumomin raya kasa na MDD, na da imani game da tasirin hadin gwiwar dake wakana tsakanin Sin da kasashen Afirka, da ma tsakanin Sin da sauran kasashen duniya, karkashin burin kasar Sin na tabbatar da cin moriyar juna, da raya al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da fatan a guda tare a tsira tare! (Marubuci: Saminu Alhassan Na CRI Hausa)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: