Hadin Kan Sin Da Afrika Na Ingiza Zamantakewar Al’ummarsu Da Na Duniya Baki Daya

Sin Da Afrika

Daga Amina Xu,

Jama’a, albishirinku! A jiya ne aka bude taron ministoci karo na 8 na dandalin hadin gwiwar kasashen Sin da Afrika a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal, a yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron ta kafar bidiyo, ya gabatar da wasu shirye-shiryen hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika daga wasu fannoni tara, ciki hadda kiwon lafiya da kawar da talauci da tallafawa manoma da ingiza ciniki da zuba jari da kirkire-kirkiren harkokin zamani da samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da kara karfin gudanar da harkokin kasa da kuma kara yin mu’ammala ta fuskar ala’du da zaman lafiya.

A kwanan nan kuma, aka gano bullar sabon nau’in cutar Covid-19 da ake kira Omicron a kasar Afirka ta kudu da ma sauran wasu kasashe, lamarin da ke da alaka matuka da karancin karfin tinkarar cutar a kasashen Afirka da rashin daidaiton raba alluran rigakafi a fadin duniya. Babban darektan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a gun wani taron hukumar kwanan baya cewa, an samar da kashi 80% na alluran rigakafin cutar ga kasashen G20, yayin a kasashe masu karamin karfi wadanda yawancinsu kasashen Afrika ne, kashi 0.6% kawai na alluran suka samu.

Sin a nata bangare, bayan barkewar cutar, nan take sai ta yi iyakacin kokarin tallafawa kasashen Afrika wajen tinkarar cutar, wadda ta turawa kasashen Afrika 17 ma’aikatan lafiya da kuma samarwa kasashe 53 da AU tallafin kayayyakin magance cutar iri daban-daban cikin rukunoni 120, kawo yanzu, yawan rigakafin da Sin ta samarwa kasashen Afrika ya kai miliyan 200.

Ban da wannan kuma, a yayin taron da aka kaddamar a wannan karo, shugaba Xi Jinping ya sanar da kara samarwa kasashen Afirka alluran rigakafi biliyan 1 don biyan bukatun AU na yiwa kaso 60 cikin 100 na al’ummomin Afrika rigakafi kafin karshen shekarar 2022, daga cikinsu allurar miliyan 600 kyauta ne, ragowar miliyan 400 kuma kamfanonin kasar Sin da kasashen Afrika da abin ya shafa ne za su hada kai wajen samar da su. Dadin dadawa, Sin za ta taimakawa kasashen Afrika wajen aiwatar da shirye-shiryen kiwon lafiya 10 da tura ma’aikatan lafiya da masana 1500 zuwa Afirka.

Dalilin da ya sa Sin ta yi kokarin taimakawa kasashen Afrika ta fuskar yaki da cutar shi ne, Sin tana sane da cewa, makoma bai daya ce ga dukkan Bil Adam, Sin da Afrika aminan juna ne, kuma suna da makoma ta bai daya. A yayin da ake fuskantar wannan mummunar cutar, dole ne dukkan Bil Adam su hada kansu don baiwa kasashe masu karamin karfi taimako da samar musu isassun allurai, a matsayin hanya daya tilo da al’ummar duniya za su iya magance wannan cutar. In ba haka ba, to sabon nau’in cutar zai sake bulla a wadannan kasashe marasa karfi, har ma ya yaduwa zuwa sauran sassan duniya kamar yadda Delta da Omicron suke yi yanzu. Lamarin da zai sa kokarin da Bil Adam ke samu ta fuskar yakar cutar da samar da rigakafi, ya bi ruwa.

Ba shakka, bisa kokarin Sin da kasashen Afrika, wannan taro da ake yi, zai samu ci gaba mai armashi, zai kuma hada kan al’ummar bangarorin biyu da yawansu ya kai biliyan 2.7 ta yadda za su rungumi kyakkyawar makomarsu ta bai daya. Wadannan manyan shirye-shirye da za a gudanar a cikin shekaru 3 masu zuwa, ba ma kawai za su kyautata rayuwar al’ummar Afrika daga fannonin 9 ba, hatta ma za su zama abin koyi wajen kafa sabon salon dangantakar kasa da kasa da zai kai ga gina kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya. (Amina Xu)

Exit mobile version