Yusuf Kabir">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ADABI

Haduwar Jini

by Yusuf Kabir
December 6, 2020
in ADABI
5 min read
Haduwar Jini
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Sunanta na asali Fatima, amma ana mata lakabi da Munayya har ma shi ne sunan da aka fi saninta da shi kenan a garin. ‘yar kimanin shekara 4 ce a duniya.Tun sadda ta taso mutanen unguwarsu suka shaide ta da nutsuwa da rashin shiga kiriniya irin ta yara. Mahaifinta Mal. Kabir dattijo Malamin makaranta ne a daya daga cikin Makarantun Firamaren garin sannan yana yin sana’ar noma da kiwo. Mutanen unguwa suke a ganin kimarsa kuma ya kasance Malamin da yake jan mutanen unguwarsu ‘Kamsu salawat’ a Masallacin unguwarsu.
Ganin irin nutsuwar Malamin galiban idan an sami matsalar cinikayya ko auratayya shi ne yake warwarewa. Munayya tana da kanne guda biyu Munib da Nasir wanda su ne ‘ya’ya uku da Allah ya azurta Mahaifinta da Mahaifiyarta da su amma duk cikin su ya fi son Munayya domin kuwa sun shaku jininsu ya hadu sosai. A yayin da kuma Mahaifinsu yana da wata matar wacce ita ce uwargida. Amma Allah mai iko sai ya kaddara rashin samun haihuwa a tsakaninsu da Mahaifin Munayya hakan ya sa ma ya auro Mahaifiyar Munayya. A sadda ta kai shekara 5 a duniya sai ya saka ta a Makarantar Firamen garin domin ta samu ilimin zamani. Tun sadda Munayya ta shiga makaranta ta zamanto cikin dalibai masu hazaka musamman a sadda tana aji hudu na Firamare domin kuwa daga lokacin ta zamanto tana yin na daya, monitan ajinsu Nazir kuma yana yin na biyu. Son zo aji shida shekarar karshe ta kammala Makarantar Firamare,a dai-dai lokacin ne Hukumar Makaranta ta shelanta bayar da kyautar keken dinki ga duk wacce ta zo ta daya, haka ta yi alkawarin sayan keke na zamani ga duk namijin da ya zo na daya. Haka za a kai duk wanda ya zo na daya makarantar ‘sciences’ Tun sadda aka Hukumar Makaranta ta shelanta kyautar da za ba dalibai a karshe zangon karshe na karatu, dalibai suka shiga karatu a sadda suke makaranta da sadda suke gida. Munayya ta kasance cikin sahun daliban da suka kudiri niyyar zamantowa ta daya a cikin ajinsu. An fara jarabawa a yayin da dalibai 70 ‘yan ajin su Muneeba suka rubuta jarabawar karshen zangon na uku kuma a Makarantar. Malaman Makarantar sun yi aikin tattara sakamakon jarabawa na tsawon sati biyu. A ranar hutu Shugaban Makaranta da dukkanin Malamai sun halarci ‘Assembly’ na karshe a zangon karatun wanda a shi ne kuma za a raba sakamakon jarabawa. daliban kowanne aji suna cikin nutsuwa suna kasake suna sauraron jawabin da Headmaster ya ke yi musu. A yayin da ya kira Malamin da yake kula da shirya jarabawa na makarantar domin ya bayyana sakamakon jarabawa ga dalibai.Mal.Yunus ya fara gabatar da takaitaccen jawabi ga dalibai,sannan ya fara karanto sakamakon jarabawar ‘yan aji daya zuwa na biyar.A sadda ya fara karanto na ‘yan aji 6 sai Malamai da dalibai suka kara samun nutsuwa sun yi tsit suna sauraren Malam Yunusa a yayin da ya fara karanto sakamakon wanda ya zo na karshe (butal) har ya zuwa kan na biyu,daga bisani ya bayyana Munayya a matsayin wacce ta zo ta farko a ajin su. Da jin haka sai ta yi godewa Allah bisa wannan ni’imar da ya yi mata a zuci, sannan ta fita domin karbar kyaututtukan da aka yi mata.Shugaban Makarantar ya mika mata kyautar sabon keken dinki da manyan atamfofi guda biyar.Nazir ya sakwalta ran cewa, shi ne zai yi nasarar karbar kambun na daya a jinsu,domin har ya shaidawa iyayensa hakan,amma a sadda aka bayyana sunansa a matsayin wanda ya zo ba biyar a ajin su,sai ya ji wani irin kododon bakin ciki ya mamaye zuciyarsa. A ranar Hukumar Makaranta ta yi musu bayanin murnar kammala Makarantar kowanne dalibi ya koma gida.
A gefen iyayen Nazir kuma sai suka yi inkarin cewa, Hukumar Makaranta kawai ta nuna son kai ne. Alhaji Mansur shi ne Mahaifin Nazir,sannan ma’aikaci ne a karamar Hukuma don haka sai ya sha alwashin daukar mataki a kan shugaban Makarantar da Mal.Yunusa wanda yake lamarin shirya jarabawa ke hannunsa.Mahaifiyar Nazir ta rarrashe shi sannan ta nemi ka da ya dauki matakin cutar da Shugaban Makarantar da Mal.Yunusa,amma ya yi kunnen uwar shegu da ita.Daga karshe dai ya sa an yiwa Mal.Yunusa Tiransifa zuwa wata Makarantar Firamare da ke wata rugar Fulani nisan kilomita 10 daga garinsu.
A bangaren Munayya kuma a sadda ta koma gida ta nunawa Mahaifinta sakamakon jarabawar da ta samu da kyaututtukan da aka bata a Makaranta,ya yi farin ciki sosai.A yayin da ya yi mata alkawarin sadaukar ma ta da dukkanin abunda ya mallaka domin ta yi karatu.Ummanta ta tambaye ta shin mi kike so ki zamanto ne diyata?Sai ta kada baki ta ce,Ummana ina so in zamanto Likita ne shi nike sha’awa.Jin lafazin Munayya ya sa Ummanta ta yi farin ciki sosai.
Lantana ita ce kishiya kuma uwar gidan wacce Mahaifiyar Munayya ta samu a gidansu,ita Mahaifiyar Munayya ita ce amarya.Tun sadda ta ji labarin nasarar da Munayya ta yi a Makaranta,ta ji wutar tsanarta ta kunnu a zuciyarta.Haka Shaidan na mata wahayin neman hanyar ta za cutar da ita ruwa a jallo.
Raihanat ita ce Mahaifiyar Munayya ta kasance mai halaye nagari da tausayawa mijinta,a duk sadda zai fita wajen aiki tana masa nasihar jin tsoron Allah a cikin lamuransa yana kuma jin dadin gwalagwalan nasihohin da take yi masa.A duk sadda mijinta Mal.Kabir ya kawo abinci tana karba ta sarrafa shi yadda ya kamata.
Ita kuwa Lantana ba ta san wani abu da ake kira kula da miji ba,domin kuwa tana da matukar son Duniya da kwadayin rayuwar jin dadi da bushasha.Duk abunda Mal.Kabir zai yi mata tana gwasalewa ne tattare da nuna rashin godiya ga hakan.Sam halayenta sun gunduri mijinta,uwa-uba ma kuma tsananin kishin da ta nunawa Raihanat a sadda take dauke da cikin Munayya.
Allah ya jarabi Raihanat da wani irin azazzabben ciwon ciki,yana taso mata lokaci bayan lokaci a duk sadda ya taso mata mijinta da ‘yan uwanta suna cire rai daga rayuwarta.Duk da haka a duk sadda matsalar ta ta so,Mal.Kabir yana yin iya iyarsa domin Raihanta ta samu lafiya.Allah mai yadda ya so,a wani talatainin dare,gari ya yi tsit,sawu ya dauke,ba a jin komai sai haushin karnuka,sai ciwon cikin Raihanat ya motsa.Cikin gaggawa Mal.Kabir ya dauki Raihanat a kan mashin domin ya kai ta asibiti.Cikin hanzari Likitoci suka yi mata kawanya domin ceto rayuwarta amma ina har ta suma.A sadda ta farfado sai ta rike hannun Mijinta ta yi masa wasiyya da ya rike mata ‘ya’yanta amana musamman ma Munayya.Haka ta nemi ya yi duk sadaukarwar da zai yi domin ta yi karatun da take so ta yi,daga karshe ta cika da kalmar shahada.
Mal.Kabir ya yi kuka mai tsanani a kan rasuwar matarsa,amaryarsa uwar ‘ya’yansa Raihanat,amma daga karshe ya tuna ce wa,rayuwa dama ta gaji tafiya da mutanen kirki masu halayen nagarta;sai ya fawwalawa Allah lamarinsa.
An yi addu’ar sharar makoki,daga a satin ne kuma jarabawar Makarantar su Munayya ta fito,ta ci Makarantar Computer Girls da ke Roni a Jihar Jigawa.Mahaifinta ya sayar da kwano 20 na geron da noma ya sai mata katifa,littafai,jakar makaranta,da dinka mata kayan makaranta.
Munayya ta fara wannan makarantar cikin sa’a domin kuwa da zaran an yi karatu ta ke ganewa ba tattare da shan wahala ba har ta kai aji karshe a Makarantar Sakandire duk cikin nasara da fahimtar karatu.A shekarar karshe na Makarantar ne kuwa Malamai suka zabe a matsayin shugabar dalibai na Makarantar a yayin da ta gudanar da mulkinta cikin tausayi da jinkai.Hukumar ilimi ta kawowa Makarantar kyautar jarabawar JAMB guda 50 hakan ya sa aka zabi Munayya cikin wadanda aka ba.A garin Kazaure Model pri,a nan ta rubuta jarabawar JAMB din ta,a yayin da ta sami 220.A yayin da a shekarar 2016 jarabawar WAEC da NECO ta yi jinkirin fita,amma a sadda ta fito ta yi nasara a dukkanin Subject din ta guda tara.Bayan wata uku Makarantar FUD-DUTSE ta saki admishin a yayin da aka ba Munayya aji Lebel One domin karantar ‘Medicine’

SendShareTweetShare
Previous Post

Yakamata Mu Tsaya Tsayin Daka Don Ciyar Da kasarmu Gaba – Sardaunan Bagadawa

Next Post

Yadda Ake Ajiye Lambar Waya a Email

RelatedPosts

Fitattun Littattafan Hausa A 2020 (2)

by Yusuf Kabir
1 day ago
0

Daga Adamu Yusuf Indabo, Kamar yadda muka faro bayani a...

Fitattun Littattafan Hausa A 2020

Fitattun Littattafan Hausa A 2020

by Yusuf Kabir
1 week ago
0

Masu iya magana suka ce 'komai ya yi farko zai...

Rayuwan Aurena

Sharhin Littafin: A Rayuwar Aurena: Abin Da Ba Zan Manta Da Shi Ba

by Yusuf Kabir
3 weeks ago
0

Na Adamun Adamawa Bauchi Daga Yusuf Kabir 09063281016 Sunan wannan...

Next Post
Yadda Ake Ajiye Lambar Waya a Email

Yadda Ake Ajiye Lambar Waya a Email

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version