Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Hafsat Ganduje Garkuwa Ga Mijinta A Fannin Shimfida Ayyuka

by
11 months ago
in FITATTUN MATA
3 min read
Hafsat
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Ko-kon-san……

Dakta Hafsat Umar Ganduje da aka fi sani da ‘Gwaggo’ ta kasance macen da ke tallafawa, taimakawa da agaza wa mijinta wajen gudanar da shugabanci na kwarai?

A yau filin namu na dauke da tarihin wata fitacciyar ‘yar siyasa, malamar jami’a kuma ‘yar gwagwarmar nema wa mata rayuwa mai inganci. Mamba ce a jam’iyyar APC wacce ta yi zarra a fagen taimaka wa kokarin mijinta na ganin ya kai ga inganta rayuwar al’umman Jihar Kano, Hafsat Ganduje mata ce ga gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje wacce take bashi gudunmawa dari bisa dari.

Labarai Masu Nasaba

Dakta Maryam Ibrahim Shettima: Sarauniyar Arewa ‘Yar Gwagwarmayar Kishin Kasa Da Al’umma

Bunkasa Rayuwar Al’umma Shi Ne Babbar Buri Na – Hon. Hajiya Kyari Joda

Wacece Hafsat Gwaggo?

An haifi Hajiya Hafsat Ganduje ce a jihar Kano. Ta halarci makarantar Firamare na Malam Madori, da kuma firamare na kwana ta Shekara, tare da halartar kwalejin koyar da malamai mata ta WTC. Ta kammala karatun digiri dinta ne fannin ilimin kimiyya da fasaha a jami’ar nan ta Bayero a shekarar 1981, ta cigaba da zurfafa karatunta inda ta samu digiri na biyu a fannin ilimin sanin halayyar dan adam a shekarar 1992 tare da sake neman wani Mastas din a fannin iya gudanar da harkokin kasuwanci a shekarar 2004, ba ta tsaya haka nan ba sake garzayawa jami’a inda ta samu shaidar Dakta abun da ke nuna alamar ta mallaki shaidar digiri na uku a fannin iya gudanar da mulki da tsare-tsare a shekarar 2015.

Tun kafin nan, Hajiya Hafsatu ta fara aikin gwamnati ce a matsayin malama kama kama har ta zama shugaban makarantar sakandarin da ta koyar. Ta zama malamar jami’a a tsangayar koyar da ilimi tsantsa a jami’ar Bayero da ke Kano. Bayan gogewarta da shahararta a fannin ilimi a shekarar 2019 ne aka nadata karamar Farfesa wato Associate Professor daga jami’ar Maryam Abacha Amerian da ke Jamhuriyyar Nijar.

Ita din mambar kungiyar a cibiyar gudanarwa ta Nijeriya (NIM). Dukka a shekarar 2019 din, ta samu wani lambar karamci mai dajara sosai wacce kungiyar Nigerian Association for Administration and Planning ta bada.

Hafsat, ta auri Alhaji Abdullahi Umar Ganduje wanda a yanzu haka shine gwamnan Jihar Kano. Duk da cewa Hafsat ba ta da ofis din matar gwamna da ake kira ‘First Lady’, amma ta himmatu a kashin kanta wajen fito da shirye-shirye da tsare-tsaren da suke samar wa mata ayyukan dogaro da kai, gangamin samar da tallafin kayan karatu, kekunan dinki, tallafin kudade domin mata su fara gudanar da ‘yan kananan sana’o’in dogaro da kai, dubban daruruwan mata ne suka amfana da kokarinta da azamarta wacce suke kiran hakan a matsayin jin kai a garesu.

Duk da an yi ta yada jita-jitan cewa Hafsat tana kaka-gida cikin sha’anin mulkin mijinta wanda ake cewa tana bayyana ra’ayinta ko lamunce ma wadanda take son a basu kwangila ko nadin mukamai, amma jami’an gwamnatin jihar sun sha karta wannan batun da cewa ba ta katsalandan wa gwamnan a sha’anin tafiyar da mulkin jihar Kano.

Matar gwamnan Allah ya albarkace su da ‘ya’ya tare ta kuma kasance fitacciya kuma gogaggiyar ‘yar siyasa a Jihar Kano. Mata da dama suna nuna mata kauna da soyayya sakamakon nuna damuwa da halin da suke ciki gami da taimakon da take musu, a bisa himmarta, ba ta bar rayuwar yara kanana ma cikin garari ba, ta sha taimaka musu ta fuskokin da rayuwarsu zai kai ga ingantuwa.

A matsayinta na tsohowar malamai jami’a, ta samu gabatar da takardu da makaloli da daman gaske wadanda ake amfani da su a fannin koyo da koyarwa, sannan ta samu dumbin lambobin yabo a ciki da wajen kasar nan wadanda ba za su kirgu ba.

A tausayinta ga talakawa, tana bada gudunmawarta sosai wajen ganin an fita daga kangin talauci, kana ta kasance mai yaki da cin zarafin mata da fyade wa yara mata da manyan mata a cikin al’umma.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (6): Bayanan Malamai Kan Tabbatar Da Azumtar Kwanakin (II)

Next Post

Iyaye Sun Nemi Gwamnati Ta Sa Ido Kan Makarantu Masu Zaman Kansu A Bauchi

Labarai Masu Nasaba

Maryam Ibrahim Shettima

Dakta Maryam Ibrahim Shettima: Sarauniyar Arewa ‘Yar Gwagwarmayar Kishin Kasa Da Al’umma

by
10 months ago
0

...

Hajiya Kyari Joda

Bunkasa Rayuwar Al’umma Shi Ne Babbar Buri Na – Hon. Hajiya Kyari Joda

by
10 months ago
0

...

Farfesar

Adenike Osofisan: Mace Ta Farko Farfesar Kimiyyar Kwamfuta A Nahiyar Afrika

by
1 year ago
0

...

Ekpo

Margaret Ekpo: Jarumar ‘Yar Siyasan Da Ta Shahara Kan Adawa Da Turawan Mulkin Mallaka

by
1 year ago
0

...

Next Post
Makarantu

Iyaye Sun Nemi Gwamnati Ta Sa Ido Kan Makarantu Masu Zaman Kansu A Bauchi

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: