Connect with us

Madubin Rayuwa

Hajiya Hajara Danyaro:  Mace Ta Farko Da Ta Zama Kwamishinar Zabe A Nasarawa

Published

on

A wannan makon, wannan filin namu ya dauko rayuwar wata gogaggiyar ‘yan siyasa wacce ta fara siyasa tun daga matakin kasa, Allah kuma ya albarkaci siyasan nata da taka matakai daban-daban, fitacciyar ‘yar siyasa ce gaya. Ta kasance mai rike da sarautun gargajiya da dama, shi wacece wannan ku biyo ni.

Wace ce Hajiya Hajara Danyaro:

Sunanta dai Hajiya Hajara Danyaro Ibrahim, An haife ta a garin Nasarawa a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa. ta yi karatun Firamare dinta a kofar Kudu a Nasarawa, daga nan ta garzaya zuwa sakandaren Kwalejin GSS, da ke Nasarawa, bayan da ta kammala ne kuma ta garzaya zuwa kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Tarayya da ke Nasarawa inda ta samu babbar Diploma.

Danyaro ta yi aikin Banki na dan wasu lokuta a Nasarawa wanda har Allah ya kaita matsayin Akanta, daga nan sai ta shiga harkar siyasa inda ta tsaya takarar Kansila a karkashin  jam’iyyar UNCP inda aka ba ta lakabin “fatari mai ba wando kashi.” Duk da Allah bai nufa ta samu nasara a zaben ba sakamakon magudin zaben da ta yi zargin an yi mata, inda kuma a wancan lokacin aka bata shugabar Mata ta Jam’iyyar UNCP gaba daya. Wanda ita ce ta kasance mace ta farko da ta rike mukamin shugabar mata ta Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa inda bayan kammala wa’adinta aka sake zabanta a karo na biyu a shekarar 2000. ta kuma kasance mace ta farko da tsohon Gwamna Sanata Abdullahi Adamu ya nada a matsayin Kwamishinar hukumar zabe ta Jihar Nasarawa.

Sharar jarumar bai tsaya haka nan ba, ta kuma taba shugabantar cibiyar yaki da jahilci ta jihar. ta kuma shugabanci wata kungiya mai zaman kanta da ake kira “Project 50” wacce ke tabbatar an samu Gwamna da bai wuce shekara 50 ba a jiharsu. A lokacin da Gwamnan jihar nan na yanzu ya fito takara karo na farko, ya nada ta a matsayin Daraktar wayar da kan Jama’a na Kwamiti kamfen dinsa, bayan da gwamnan ya sake samun nasara a karo na biyu ya sake nadata matsayin mai bayar da shawara ta musamman kan harkokin jam’iyyun siyasa. ta kuma kasance Amirar Hajji zuwa kasar Saudiyya sau biyu a shekarar 2012 zuwa 2013. A yanzu dai ita c eke rike da mukamin babbar mai bai wa Gwamna Umaru Tanko Al-Makura shawara a kan daidaita Jinsi.

Hajiya Hajara Danyaro ta samu sarautar gargajiya wadanda suka hada da ‘Garkuwar Matan Nasarawa’ da ‘Tauraruwar Matan Loko’ da Jarumar Matan jihar Nasarawa dadai sauransu. A fagen lambobin yabo kuwa, akwai lambar yabon da ta taba samu na Jarumar Matan Afirka Masu gina kasa da Jakadiyar Zaman Lafiya ta kungiyar Unibersal Peace Federation ta shekarar 2008 da Maman Afirka wacce kungiyar Election Communication Limited ke bayarwa da sauransu.

Babban burin jarumar a fagen siyasar shi tana da muradin ake tunawa da ita a matsayin macen da ta yi tsayin daka wajen tallafa wa mata musamman wadanda suka rasa mazajensu da nakasassu da kuma marasa galihu a cikin al’umma. Domin ta lura cewa wadannan mutane suna matukar bukatar taimakon kowa cikin al’umma.

Da wannan filin ya tambayeta shawararta ga mata ’yan uwanta:

“Shawara ta gare su ita ce su tashi su nemi ilimin addini da na zamani domin su ne ginshikan zaman duniya da samun sa’a a Lahira. Idan ba su da halin yin haka, sai su rungumi sana’a.  Kada mace ta dogara da mijinta kawai a wannan zamani domin idan ta yi haka za ta fuskanci wulankanci. Haka kuma dole ’yan uwana mata su tabbatar suna bai wa ’ya’yansu kwakkyawar kulawa ta wajen samar musu da ilimi mai inganci don ya taimaka wa rayuwarsu ta gobe,”

Allah dai ya azurta Hajiya da auren Alhaji Abubakar Sadik Ubandoma, wanda har kuma Allah ya albarkace su da ’ya’ya.

 

Advertisement

labarai