Daga Yusuf Abdullahi Yakasai, Legas
Koda- yaushe cancanta da rashinta duk, ita ce ke sa ayi wasu abubuwa da suke mabambanta, wannan karon sai aka yi sa’a yadda cancantar ce ta sa Dakta Haruna mai Yasin Sasa, ya ce suka duba suka nada sarauniyar jihohin yamma.
Ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya nada ta, a mukamin na gargajiya inda ya bayyana dalilan da suka nadatan, wadanda suka hada da mace ce mai kokarin samar da zaman lafiya, hadin kan al’umma, da kuma taimakawa marayu.
Wadannan abubuwan sune halayaen da suka ya ga cancantar ta, matsayin sarautar sarauniyar ‘yan mata ya nada Hajiya Ummi Muhammed, a matsayin sabuwar sarauniya na jihohin yamma shida. Ya kuma yi mata addu’ar fatan alkahairi, da ya taya ta riko.
Ita ma a nata jawabin Hajiya Ummi Muhammed ta nuna farin cikin ta kan shi matasayin da aka bata, inda ta nuna godiyarta, ga Allah bata damar daukar nauyin tafiyar da sarautar da aka bata, wadda kuma mai tarihi ce wurinta, shi kuma Dakta Haruna mai Yasin Sasa ta bayyana cewa Uba ne a gare su inda tace Allah ya kara masa lafiya da tsawancin kwana da lafiya da abinda zata ci.
Ta kara jaddada cewa “Mu kuma masu biyayya ne a gare shi a kullun, daga cikin mutane wadanda da suka halarci bikin sun hada da manyan baki daga yammaci da kuma manyan baki daga Kudanci Nijar, Kwatano, da da kuma Ghana. Akwai wasu sauran jama’a masu yawa daga sassa daban- daban.