Hukumar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta ce ta fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana a Nijeriya inda alhazai suka fara tashi daga shiyyar Abuja a ranar Lahadi.
Shugaban hukumar NAHCON Abdullahi Muktar ya bayyana wa manema labarai cewa “an yi sahun farko daga Abuja inda aka kwashe alhazai 460.
Abdullahi Mukhtar, ya ce, ana ana saran kammala jigilar mahajjatan kasar a ranar 20 ga watan Agusta, ‘akwai kimanin alhazai dubu 60 da za su je Kasa-Mai-Tsarki don sauke farali a bana’ inji shi.