Hajj 2017: Gobara Ta Tashi A Wani Otal A Makka

A safiyar yau Litinin an samu rahoton tashin gobara a wani otal a Makka, wadda ta yi saurin jan hankalin mahajjata da kuma jamai’an tsaron kasar.

Jami’an tsaro sun tserar da dukkanin mutanen dake cikin otel din wanda ke tsakiyar birnin Makka.

A cewar kakakin jami’an tsaron Nayef al-Sharif, ya ce ba a samu wanda ya ji rauni ba, inda ya kara da cewa gobarar ta tashi ne sanadiyyar wata na’urar sanyaya daki da ta samu matsala. Wutar ta tashi ne a hawa na takwas na otal din da ke gundumar Aziziyah dake cikin Makka.

Exit mobile version