Hukumar lura da aikin Hajji ta Nijeriya wato NAHCON a ranar Alhamis ta bayyana cewa; ya zuwa yanzu ta yi nasarar jigilar maniyyata aikin hajji daga Nijeriya mutum dubu 32 da dari 402 zuwa birnin Madina dake kasar Saudiyya.
Ana sa ran dukkanin maniyyata aikin hajji ta bana a fadin duniya da su isa birnin Makkah daga Madina a ranekun 7 zuwa 8 ga watan Agustan domin isa Munnah domin fara aikin Hajjin bana.
A wata sanarwa da aka fitar a birnin Madinah, hukumar ta ce; sun yi jigilar maniyyatan a sahu 66, inda ya ce jirgin Flynas XY5491 ya kwaso maniyyata daga jihar Kebbi zuwa birnin Madinah da mutum 430 da jami’an hukumar biyu. NAHCON ta ce; maniyyatan sun hada da; maza 203, sai mata 227.
Alhaji Ahmed Maigari, Kodinetan hukumar a birnin Madinah a yayin ganawarsa da manema labarai ya tabbatar da cewa; za su kawo dukkanin maniyyata aikin hajjin bana birnin Madinah kafin kurewar lokacin da aka ba su.