Munkaila T. Abdullah, Daga Makkah
Kimanin Alhazai sama da dubu 2,000 ne daga Jihar Jigawa wadanda ke fama da rashin lafiya daban-daban, likitoci suka duba a cikin makwanni biyu a yayin zamansu a kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajji a wannan shekara ta 2017.
Shugaban tawargar likitocin Jihar ta Jigawa a aikin hajjin na bana, Dakta Ibrahim Mika’il ne ya shaidawa wakilinmu a yayin zantawarsu jiya a Birnin Makkah.
Daktan ya bayyana cewa, daga fara aikin hajjin na bana zuwa yanzu, tawagar tasu ta likitoci ta yi nasarar duba kimanin Mahajjatan Jigawa Dubu 2,300 a cikin makwanni uku da suka gabata, tun daga saukarsu a birnin Madina, zaman Minna, Arafa da kuma zamansu a birnin Makkah bayan kammala aikin hajjin na bana.
Shugaban ya kuma bayyana cewa, duk da kasancewar ba a samu rahoton rasuwar wani Maniyyaci ko daya daga Jihar Jigawa ba, amma an samu yawaitar rashin lafiya akai-akai.
Dakta Mika’il ya ce, mafi yawancin cututtukan da suka fi addabar mahajjatan sun hada da cutar zazzabi, zazzabin mura, cutar gyambon ciki da kuma lalacewar ciki sakamakon sauyin yanayi da aka tsinci kai a ciki.
Sannan kuma ya ce, cikin mutane 39 kuwa da aka aike dasu zuwa manyan asibitocin Hukumar Alhazai ta Kasa da kuma Babban Asibitin Sarki Abdul’Aziz, wasunsu sun samu matsalar karaya da kuma cutar Sikila gami da sauran cututtuka masu zafin gaske.
Babban Likitan, ya kuma shawarci Alhazan da su kiyaye irin hadin gambizar abincin da zasu ci gami da tsaftace muhallin da suka zaune domin samun saukin yaduwar ire-iren wadannan cututtuka a yayin zaman ragowar kwanakin nasu a kasa mai tsarki.
Daga karshe shugaban likitocin ya kuma yaba wa gwamnan jihar ta Jigawa Alhaji Muhammad Abubakar Badara bisa cikakken goyon bayan da ya baiwa tawagar tasa domin tabbatarda Alhazan na Jigawa sun kammala aikin hajjinsu cikin koshin lafiya.