Abdulrazak Yahuza Jere" />

Hajjin Bana: Yanayin Zafi Ya Tsananta A Biranen Makka Da Madina

A yayin da maniyyata aikin Hajjin bana ke tururuwar isa kasa mai tsarki, rahotanni na nuna cewa yanayin zafi da ake ciki a biranen Madina da Makka na kara tsananta sosai.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa, a jiya Alhamis, yanayin zafin a Madina ya kai matakin digiri 44 a ma’aunin salshiyos, yayin da na Makka kuma ya kasance a mataki na 41.

Bisa yanayin zafin, Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Saudiyya, ta dukufa wayar da kan maniyyata Hajjin kan abubuwan da za su yi domin samun saukin yanayin da ake ciki. Daga cikin abubuwan da ta nemi Maniyyatan su rika yi akwai shan ruwa sosai ko wani abu mai dan-ruwa-ruwa, da yin amfani da lema yayin da za su shiga cikin rana.

Yanayin zafin a manyan biranen na musulunci masu tsarki, zai ci gaba har zuwa nan da kwana 10 a matakin digiri 43 a ma’aunin salshiyo, kamar yadda masana masu hasashen yanayi suka hango.

Zafin dai ya tilasta wa maniyyata Hajjin rage zirga-zirga a waje, in ba lokacin da ya zama dole ba kamar su zuwa masallaci ko cin abinci da sauransu.

A halin da ake ciki kuma, tawagar maniyyata Hajji ta sojojin Nijeriya ta isa kasa mai tsarki da safiyar Alhamis din nan.

Sojojin su 348, sun sauka ne a filin jiragen sama na Yarima Mohammed Abdul’aziz.

Sun bar filin jiragen sama na birnin Ikko ne a ranar Laraba da dare tare da wasu maniyyata Hajji su 150 daga Jihar Ogun.

Isar sojojin kasa mai tsarki, ta sa an samu nasarar jigilar maniyyatan kasar nan 33,000 a cikin sawu 67, kamar yadda kididdigar Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta nuna.

An yi wa sojojin masauki a yankin Elyas mai kunshe da gidajen zama da kuma cibiyoyin kasuwanci.

Exit mobile version