A shekarun nan, wasu makiyan kasar Sin a yammacin duniya suna ta yada jita-jita kan batun jihar Xinjiang, a yunkurin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, da yaudarar kasashen duniya, da kokarin kawo cikas ga zaman lafiya da bunkasuwar jihar Xinjiang.
Masu iya magana na cewa, karya fure take ba ta ‘ya’ya. A don haka, duk wasu karairayi ba za su taba yin tasiri ba.
Batun jihar Xinjiang ba batu ne da ya shafi kabila, ko addini, ko hakkin bil adama ba, batu ne na yaki da ta’addanci da ‘yan a-ware. Yadda jihar Xinjiang ke ci gaba da samun kwanciyar hankali da bunkasuwa, da ma yadda mazauna jihar ke jin dadin zaman rayuwa da gudanar da ayyukansu, sun kasance makamai masu matukar karfi da za su karyata wadannan kalaman banza.
A ‘yan shekarun da suka gabata, yawan ‘yan kabilar Ugyur da ke jihar Xinjiang yana ta karuwa. Daga shekarar 2010 zuwa 2018, yawan ‘yan kabilar ya karu daga miliyan 10.17 zuwa miliyan 12.72, saurin karuwar ya kai kaso 25.04, wanda ya zarce karuwar yawan mazauna jihar na kaso 13.99.
Haka kuma daga shekarar 2014 zuwa 2019, saurin karuwar GDP na jihar Xinjiang ya kai kaso 7.2 a kowace shekara, yayin da karuwar matsakaicin yawan kudin shiga da mazauna jihar ke samu a kowace shekara, ta kai kaso 9.1. Ya zuwa yanzu, dukkan mazauna jihar masu fama da talauci miliyan 3 da dubu 89 sun fita daga kangin talauci, lamarin da ya sa aka samu nasara kan matsalar karo na farko a tarihi.
Ban da wannan kuma ana kiyaye hakkokin mazauna jihar Xinjinag na kabilu daban daban bisa doka. Karama ko babbar kabila, dukkansu na da matsayin daya bisa doka, wadanda ke da ‘yancin gudanar da harkokin kasa, bin addinai, samun ilmi, amfani da harsunansu, da yada al’adun gargajiyarsu.(Kande Gao daga sashen Hausa na CRI)
Sin Ba Ta Son Yin Babakere, Mutunta Juna Da Hadin Kai Sune Ginshikan Makomar Huldar Sin Da Amurka
Daga Amina Xu Kwanan baya, farfesa jami’ar Harvard Joseph S....