Umar A Hunkuyi" />

Hakkin Al’ummar Kaduna Ne Ba Gwamnati Goyon Baya – Aminu Ahmad

Manufar gwamnatin APC tun daga tarayya Jihohi zuwa kananan hukumomi shi ne kawo canji, a wani lokacin kuwa canji abu ne mai dan kaikayi ko dan zafizafi. Ko dakin ka ne kake son ka yi masa kwaskwarima, ballantana a ce kana son ka gina sabon gida a kan tsohon gidan da kila ka gada a wajen kakanka, ba mamaki ka ga wani a gidan yana son a ci gaba da zama a cikin wadannan tsaffin dakunan da aka gada na kakanni, amma kuma yanzun zamani ya canza bukatuwa sun taso watakila ‘ya’ya sun yi yawa a gida, don haka za ka ga akwai bukatar wannan gidan a yi masa kwaskwarima a rushe wani bangaren a tayar da wani bangaren da sauran su.
Wannan bayanin yana fitowa ne daga bakin Honorabul Aminu Ahmad, dan majalisar Jihar Kaduna, mai wakiltar mazabar
Makarfi. A sa’ilin da yake sharhi kan guna-gunin da wasu ke yi dangane da wasu gyare-gyare da gwamnatin ta Jihar Kaduna take aiwatarwa musamman a cikin garin Kaduna.
Ho n . A m i n u y a c i gaba da cewa: “Canji abin da gwamnatin APC ta zo yi kenan, canji ta kowane fuska, ta yanda yake tsaffin gine-gine za a mayar da su sabbi, tituna za a fadada su, kasuwanni tilas a fadada su. in ka ce za mu ci gaba da zama a yanda muke a halin yanzun, nan da shekara goma ai titunan nan namu ba za su ishe mu ba, ballantana nan da shekaru Ashirin ko Talatin. Yanzun yanda matasa suka taso, akwai bukatar a mayar da kantunan nan na zamani, ba ga shi nan ba a yanzun duk wanda Allah Ya huwace ma shi sai ya je ya sami wani tsohon gida ya rushe shi ana ta gina Plaza-Plaza, to ballantana gwamnati! Gwamnatin da ta yi alkawarin za ta raya karkara da birane.
Ai in za a yi gyara wani lokaci sai an dan ciza da zafizafi haka, amma za ka kalli mene ne manufar yin, an yi ne don a kuntata, ko kuwa an yi domin a kyautata? Na yi imanin gyare-gyaren nan da ake yi ana yi ne domin a kyautata. Yanzun titin da aka yi daga gadar Kawo zuwa cikin garin Kaduna, ana jin dadin abin ko ba a jin dadin sa? ai ka ga wannan ci gaba ne.
Gyare-gyaren da ake yi na kasuwanni da yanda ake fadada tituna, ai ya zama mana wajibi, dole mu yi wannan, domin mu yi wa ‘ya’yanmu da jikokinmu shimfidar da su ma za su zo su more rayuwar su. ba yanda za a yi a bar kasuwar Kaduna a cikin cinkoso domin karuwar mutane, ai mutane suna zuwa Dubai suna zuwa China, haka rayuwa take a can? Haka kasuwanni suke a Saudi Arabiya? Duk mutumin da ya je ya ga yanda kasuwa take a can, idan ya zo nan zai ji kunya. Kai ko nan Abuja ka leka ka ga yanda garin Abuja yake, ka zo nan Kaduna za ka yi fatan me zai hana mu ma mu zama kamar garin Abuja din. To kuma Allah Ya ba mu arzikin da za mu iya, to don me ba za mu yi amfani da wannan arzikin ba.
Duk mutanan da suke ganin an rushe masu wuraren neman abincin su, su dogara da Allah, kuma gwamnati tana da niyya, canza masu za ta yi da wanda ya fi nasu. Don haka ina mai imani da cewa gyare-guaren nan da ake yi ci gaba ne ba ci baya ne ba, kuma dole ne sai an yi su domin karuwar al’umma da kuma ci gaban ta.
Ga masu kukan cewa duk ina gwamnati za ta samo kudaden yin wadannan ayyukan? Sai na ce masu, ai mai daki shi ya san inda ruwa ke zuban ma shi. Gwamnatin Jihar Kaduna ta rigaya ta yi Magana da kungiyoyin Duniya masu niyyar su taimaka mana. Akwai Bankin Musulunci, akwai Bankin raya Afrika, duk sun yi alkawarin za su taimaka wa Jihar Kaduna. Don haka muna da kyakkyawar fatan za a sami wadannan kudaden.
A nan babban kiran da nake yi ga al’ummar Jihar Kaduna, mafiya yawanmu dai Musulmi ne da Kirista, duk mun yi imani da Allah, muna bautawa Allah, mu rika yin addu’ar Allah Ya kara azurtamu, mu rika hakuri da abin da muka samu kanmu a cikin sa, mu rika fatan alheri a tsakaninmu, tsakanin gwamnatocinmu, tsakanin shugabanninmu da tsakanin mu ya mu. Hakki ne a kan jama’ar Jihar Kaduna da su taimaka wa wannan gwamnatin. Allah kuma Ya yaye mana abubuwan da suka dame mu. Na yi imanin duk wadannan fituntunun da suka shafi tsaro za su zama tarihi nan ba da jimawa ba. Mu dai mu ba da hadin kai, mu yi wa gwamnati biyayya mu yi mata fatan alheri, duk inda gwamnati take neman ta kauce a ba ta shawara amma shawara na gaskiya.

Exit mobile version