Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa hakkin kowa ne a kungiyar ya dinga zura kwallo a raga kamar yadda yake hakki akan ‘yan wasan gaba na kungiyar.
Zidane ya bayyana hakane bayan da Real Madrid da ziyarci kungiyar Elche domin buga wasa na 16 a gasar cin kofin La Liga ranar Laraba kuma na karshe a shekarar 2020 sannan aka tashi 1-1 bayan dan wasa Luca Modric ya zurawa Real Madrid kwallonta ta farko a minti 20 kafin kuma Fidel ya farke a bugun fanareti a minti na 52.
Wannan shi ne wasa na takwas da Real Madrid ta buga a cikin watan Disamba kuma na karshe a shekarar 2020 har da rashin nasarar da ta yi a hannun kungiyar Shakhtar a gasar kofin zakaru na Champions League.
Ranar 1 ga watan Disamba Real Madrid ta yi rashin nasara a gidan Shaktar da ci 2-0, tun daga nan ta yi fafatawa biyar a La Liga da Champions League a jere ta kuma yi nasara a dukkan karawar.
Real Madrid Ta fara da doke Sebilla da ci 1-0 ranar 5 ga watan Disamba, sai kuma ta yi nasara a kan Borussia Munchengladbach 2-0 ranar 9 ga watan Disamba sannan daga nan ne Real Madrid ta doke Abokiyar hamayya Atletico Madrid da kuma Athletic Bilbao da Eibar da kuma Granada duk a gasar La Liga a cikin watan Disambar.
Bayan tashi daga wasan ne mai koyarwa Zidane ya bayyana cewa yakamata ‘yan wasan kungiyar su gane cewa ba kawai ‘yan wasan gaba bane suke da hakkin zura kwallo a raga saboda haka kowa sai y adage yana kokarin ganin yana taimakawa tawagar da kwallaye.