Hakkin Naira Biliyan 45: Tsofaffin Ma’aikatan Kamfanin Jiragen Sama Na Nijeriya Sun Yi Zanga-zanga

Mutum uku daga cikin tsofaffin ma’aikatan   rusasshiyar hukumar zirga-zargar jiragen sama ta kasa(Nigeria Airways), sun yanke jiki sun fadi ayayin da suke gudanar da zanga-zanga ta lumana a fikin tashi da saukar jirage na kasa da kasa na Murtala Muhammed dake jihar Legas akan abinda suka kira a zaman ci gabada da kin da gwamnatin tarayya ta yi na biyansu hakokin su har naira biyan arba’in da biyar na shekaru sha uku bayan da kamfanin ya durkushe.

Tsofaffin ma’aikatan sun fito gudanar da zanga-zangar ce da misalign karfe 9.00 na safiya, inda sai da suka taro a a gefen filin jirgin kafin su fara yin tattaki zuwa tashar ta jirgin saman,inda hakan ya haifar da tsagwaron cunkoson ababen hawa masu wuciwa har wasu fasinjoji da dama suka rasa jiragen da suka yi dako don  yin tafiya.

Ukun daga cikin tsofaffin ma’aikatan da sun fadi ne a tsakanin rundunar Soji ta sama  da inda tashar jirgin take amma sauran masu zanga-zangar da wasu masu amfani da tashar suka kawo masu dauki.

Tsofaffin ma’akatan sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yiwa ministan kudi Kemi Adeosun magana don ta sakar masu hakokinsu, sun kuma zargi Kemi akan danne masu hakokin nasu da gangan inda take ta biyan sauran mutane amma su ta share su.

Wasu bayanan da masu zanga-zangar suka rubuta a kwalayen sune kamar haka, “Shugaba Buhari ka cece mu daga hannun Kemi Adeosun,”

Adeosun tana son ta bata maka kyawawan ayyukan ka, Shugaba Buhari ya fara yin dubi akan hakokin mu,” Adeosun ina kika ajiya kudin mu na fansho”

“Madam MOF ko kin yi kwanciyar magirbi ne akan hakokin? Da suke yiwa manema labarai jawabi tsofaffin ma’ikatan sunyi barazanar zuwa Ma’aikatar kudi  don su rufe ma’aikatar,I in har daga yau Laraba majalisar zattarwa ta kasa ta gaza yin wani abu akan maganar.

Tsofaffin ma’aktar ta hanyar Mista Andrew Inalegwu dake sashen zirga-zirga ta kungiyar manyan ma’aikata ta kasa (ATSSSAN) ya ce, suna neman hakokin nasu ne daga gun ministan kudi Kemi Adeosun akan cewar me yasa tun lokacin da aka amince da a biya su tun a watan Mayu na shekarar data wuce amma ba a basu ba.

Wasu daga cikin shugabannin tsofaffin ma’aikatan da suma suka yi jawabi a wurin zanga- zanagar sun hada da shugaban reshe na Jirgin na ‘yan fanshi (NUP), Kwamarade Sam Ezene da Injiniya Lukman Animashaun.

Sun zargi Kemi akan yi masu wasa da hankali da hakokin su kamar yadda take gaya masu cewar Fayal dinsu na hakokinsu na gaban majalisar kasa wanda kuma ‘yan majalisar suka karyata hakan.

A cewar tsofaffin ma’aikatan, idan Adeosun tana jiran amincewar majalisar ne, me yasa aka biya jami’an Soji da suka yi ritaya kuma me yasa ta fara biyan ‘yan kwangila da suka yiwa gwamnatin tarayya aiki?

Sun zargi Kemi akan yin tubka da warwarewa akan hakokin su, musamman ganin tuni wasun su mutu ba tare da sun karbi hakokinsu ba.

 

Exit mobile version