Daga Rabiu Ali Indabawa
A Masar ‘yan sanda 54 ne aka kashe a lokacin da suka kai wani sumame a maɓoyar mayaƙan sa kai kusa da birnin Alƙahira, kamar yadda jami’an tsaron ƙasar suka yi bayani.
Jami’an da waɗanda suka nemi a sakaye sunayensu sun ce an yi wa jami’an tsaron kwanton bauna ne a daren jiya, bayan da suka hallara a mafakar ‘yan bindiga dake yankin Hamada a yammacin ƙasar da ake kira al-Bahriya.
Jami’ai 20 da kuma Kurata 34 suna daga cikin waɗanda suka halaka a harin. Ma’aikatar harkokin cikin gida a sanarwar da ta bayar ta ce wasu jami’anta sun yi shahada, sai dai bata bada ƙarin bayani ba.