Connect with us

FILIN FATAWA

Halascin Zubar Da Ciki Wata Biyu Saboda Tsoron Talauci

Published

on

Assalamu Alaikum DR. Ko yana halatta mace ta zubar da cikin da bai wuce wata biyu ba saboda tana shayarwa kuma batada cikakkiyar lafiya ga talauci sosai awurin mijinta baya iya cida ita, sai tafita tayi kwadago ta nemowa yaranta abinci?        

Wa’alaykumussalam, To dan’uwa Malamai sun yi ijma’i akan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai, idan ya kai wata hudu, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba. Amma sun yi sabani game da zubar da ciki kafin ya kai watanni hudu, wasu sun haramta, wasu kuma sun halatta wasu sun karhanta. Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin da bai kai wata hudu ba, idan akwai lalura. Idan aka zubar da ciki kafin ya cika wata hudu saboda matsalar da likita ya tabbatar yaron ko Uwar za su fuskanta, ko kuma tsoran tagayyarar yaron bayan ya fito, ba za’a ce kun yi laifi ba, tun da bai zama mutum ba, kuma ba za’a tashe shi ranar alkiyama ba.

Don neman karin bayani duba Ahkamu al-janin fil-fikhil islamy na Umar Ganam

“Babu wata rai face azurtata da abincinta yana wajan Allah”, Kamar yadda aya ta: 5 a Surat Hud ta tabbatar da hakan.

Kada ka taba fargabar arzikin yaronka saboda Allah ne yake azurta shi tun yana ciki, kamar yadda ayoyi da hadisai Suka tabbatar. Allah ne mafi sani.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: