Khalid Idris Doya" />

Halima Adeh: ‘Yar Amurka Da Ta Fara Lashe Gasar Sarauniyar Kyau Da Lullubi

Halima Adeh matashiya ce da ta yi fice a duniyar nan musamman ta fuskacin yin ado da hijabi da mayafi, wacce ta shiga gasa daban-daban na ado da kyau kuma tana cinyewa tare da sanya hijabi da mayafi, ita ce ‘yar Amurka ta farko da ta fara shiga gasa da hijabi da kuma ci ba tare da wani yanayi ba.

Wace Ce Halima Adeh?
Halima Adeh an haifeta ne a ranar 19 ga watan Satumban 1997, bakar fata ce wacce ta taso da son sanya hijabi da mayafi da hakan kuma ya zama sanadin ficenta a duniya, wacce ta samu nasarar lashe gasar Sarauniyar kyau tare da sanya hijabi da mafiya.
Ta kasance mace ta farko a tarihin rayuwarta da ta fara sanya hijabi ta shiga gasar Sarauniyar Kyau a Miss Minnesota ta kasar Amurka. Bayan da ta samu tauraruwa a kasa ta sake zama tauraruwa da a duniya ake kallonta a jinjina mata bisa zarrar da ta yi da fito da salon salon shiga gasar Sarauniyar kyau.
Adeh an haifeta ne sansanin ‘yan gudun hijira ta Kakuma da ke kasar Kenya. Ta zauna a kasar Somali da ta kai shekaru shida ta koma zuwa kasar Amurka, inda ta zauna a St. Cloud, da ke Minnesota. Ta halarci makarantar Apollo High Scholl a yayin da abokan karatunta suka zabeta a matsayin Sarauniya. Ta kuma zama dalibar jami’ar St. Cloud State University.
A shekarar 2016, Aden ta janyo hankalin kafafen sadarwa bayan da ta samu nasarar lashe gasar Sarauniya ta kyau na Miss Minnesota ta Amurka, bayan gasar farko na Sarauniyar kyau wacce ta sanya mayafi da hijabi a yayin gasar. Wasu kuma sun nazari wannan matakin nata a matsayin hanyar tallata kayan da ta sanya da fitowa da su gasar wadanda kaya ne na zamani masu saukar hankali.
Bayan shekara da wannan gasar, Aden ta sanya hannu kan yarjejeniyar aiki da IMG Models na tsawon shekaru uku. A watan Fabrairu 2017, ta  halarci makon kwalliya New York Fashion Week na Yeezy Seoson 5.
Daga bisani ta zama Alkalin gasar Sarauniyar kyau na Miss USA na 2017.
Ta yi aiki a sharararren wuraren zane da ado na Madmara da Alberta Ferretti. Har-ila-yau, a shekarar 2016 ta halarci makon gasar kyau na Milan Fashion Week da London Modest Fashion Week.
Halima Adeh ita ce mace ta farko da ta fara sanya hijabi a gasar ado na kasa da kasa da manyan gasar kyau daban-daban. A watan June na 2017, ita ce mace ta farko da ta zama taurarurwar kyau da ta sanya hijabi na bogue Arabia, Allure da kuma British bikue.
A shekarar 2018, Halima Aden ta zama jakadar UNICEF. Aiyukanta ta maida hankali ne kan kare ‘yancin yara da mutuncinsu. A kuma shekarar 2019, ta sake zama mace ta farko da ta sanya hijabi da mayafi, Burkini a gasar wasanni ta Sportes Ullustrated Swimsuit.
Ta yi kokari sosai wajen kara wa mata musulmai kumaji da himmar sanya hijabi a sassan duniya. Ta kan sanya kaya masu rufi da lillibi da hijabi a shafinta na Instagram wanda hakan ya kan jawo ra’ayin mata da dama da su yi koyi da salon kayan da ta sanya. Ta kuma sake zama mace bakar fata ta farko sanya da hijabi da aka manna ta a jikin mujalar Essence na Janairu/Fabrairu, 2020.
A yanzu haka, Halima ta zama tauraruwar da take da kyakkyawar dangantaka da kamfanonin hada kayan ado da zane da take iya basu samfurin dinkin da take son a zana mata kuma a fitar mata da hakan ya kara daukaka lifafarta a duniyance.

Ta kuma sha alfahari da kasancewarta mai sanya hijabi da baiwa mata da dama sha’awar hakan a kowani lokaci.

Ta kuma zama mace mai daga muryanta a duk wurin da ta ga ana kokarin kankantar da hijabi ko kyamatar masu sanyawa, wacce ta zama madubi ga mata da dama musamman ga musu sha’awar sanya hijabi.
Ta samu kwarewa matuka kan hidimar zanen kaya a lokacin da take aiki da Madmara, wanda ta samu zarafin tsara kayan da za ta sanya ta kuma zana har zuwa ga dinkawa.

Exit mobile version