Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTON MUSAMMAN

Halin Ƙunci A Neja: Wa Zai Kawo Wa Jama’a Ɗauki?

by Tayo Adelaja
October 7, 2017
in RAHOTON MUSAMMAN
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ganin irin halin ƙunci da jama’a ke ciki a jihar Neja, wanda wasu da dama na fuskantar barazanar abinda za su saka a bakin Salati, wakilinmu MUHAMMAD AWWAL UMAR ya samu zantawa da wasu da jin ra’ayoyinsu.

Alhaji Yawa Siraja ma’aikacin gwamnatin jihar ne, ya ce maganar gaskiya halin da ma’aikatan jihar nan ke ciki ba sa ganin laifin gwamnati domin laifin ƙungiyar ƙwadago ne. a cewarsa duk lokacin da gwamnatin jiha ta fara tantance ma’aikata da nufin kawo daidaito, ƙungiyar ƙwadago ce ta yi wa lamarin ƙafar ungulu inda suka nuna cewar yadda ake aikin tantance ma’aikatan ba su gamsu da shi ba.

samndaads

Siraja ya ce, “tun bayan da aka dawo da aikin tantance ma’aikatan hannun ita ƙungiyar ƙwadagon, ma’aikata suka faɗa garari, domin har yanzu ba su iya bada sakamakon aikin nasu ba saboda abinda suke samu a hannun gwamnati. Yanzu haka rahotanni sun tabbatar mana cewar dukkanin mambobin kwamitin tantancewar nan suna karɓar naira dubu biyar daga hannun gwamnati. Ka dubi halin da tsaffin ma’aikata ke ciki a jihar, nan sai dai lahaula wala ƙuwwata, domin maganar albashi kam gwamnati na biya a lokacin da ya dace, saɓanin halin da wasu jahohi ke ciki, amma waɗanda suka yi riyata da aiki yau kimanin shekaru biyu baya idan ka ga halin da suke ciki sai ka tausaya masu domin ba fansho ba giratuti wannan ai zalunci ne kuma ‘yan ƙwadago ba su ce komai ba, idan ma ba za ka iya kyautatawa mutum ba ya kamata ka ba shi haƙƙinsa mana.”

Labaran Sarkin Kaji da ke kasuwar Kure a Minna ya ce, “maganar gaskiya gwamnati kam ta kwafsa, domin canjin da jama’a suka yi ba su gan shi ba, jihar nan ta dogara ne da aikin gwamnati, dole sai ma’aikata sun samu walwala sannan mu ‘yan kasuwa za mu amfana, amma su suna kuka, yaushe mu ‘yan kasuwa za mu dara.

Sarkin Kaji ya cigaba da cewar, “ba mu da wani abu illa roƙon Allah ya kawo mana sauyi a wannan tafiyar, sai ka wuni a kasuwa ba wani cinikin kirki kuma mun ta’allaƙa ne da ɗan abinda ma’aikata ke samu sai ya watsu a hannun jama’a a hakan yake zuwa hannun mu tunda dai nan jihar ba kamfanoni ke gare mu ba. Ya kamata gwamnati ta ji tsoron Allah ta dawo ƙasa ta yadda mu ƙananan ‘yan kasuwa za mu samu sauƙin rayuwa kuma ita ma gwamnatin ta amfana. Ina nufin a ƙirƙiro ayyuka ga jama’a, idan aka yi haka kuɗi zai yalwatu a hannun jama’a wannan shi ne ribar dimukuraɗiyya.

“Babban abinda talaka zai gani ya faɗa shi ne samun sauƙi a rayuwa wanda yanzu dai babu shi, kuma muna jin Gwamnatin Tarayya ta tabbatar mana da cewa ta bawa gwamnatin jiha kuɗaɗe don samun sauƙin halin da muke ciki amma ba za mu iya nuna inda aka kashe kuɗaɗen nan ba, na tabbatar da yau an biya ƙananan ‘yan fansho mu ma ‘yan kasuwa zamu anfana, amma maimakon hakan sai ana ƙarawa masu ƙarfi, ƙarfi; an kasa biyan ɗan fansho mai naira dubu ɗari biyu zuwa biyar wanda idan ka biya shi zai iya zuwa kasuwa don sayen abinci. Amma mun ji an biya manyan ma’aikatan fansho da ba su daɗe da barin aiki ba masu shekaru uku zuwa huɗu har sama sunan nan a cikin ƙunci ba a saurare su ba, gaskiya ya kamata gwamnatin jiha ta sani wannan tafiyar ba ta jari hujja ba ce, tafiya ce da talakawa suka nema kuma ya kamata a saurare su.”

Yunƙurin jin tabakin masu sana’ar Kabu-kabu da tuƙin Keke-Napep ya ci-tura sakamakon zargin da suke cewar a kowani lokaci suna magana da kafafen yaɗa labarai, amma ba wani mataki da suke ganin an ɗauka sai ma ƙaruwar matsalar da suke samu daga jami’an karɓan haraji da hukumar kiyaye haɗurra FRSC da kuma jami’an VIO.

Duk da haka, wakilinmu ya nemi jin tabakin shugaban ƙungiyar masu tuƙa Keke-Napep ta jiha, ya ce ba zai yi riga malam masallaci ba, domin gwamnatin jiha ta kafa kwamiti don sauraren koke-kokensu, saboda haka sai sun kammala zaman kwamitin kafin ya ce wani abu akai.

Malam Bilyaminu Haruna wani mai tuƙin Keke-Napep da bai yarda an ɗauke shi hoto ba, ya ce su, “Mu kam mun bar komai a hannu Allah, ba wanda ake cuta irin talaka, yanzu an ce mu yi rajista da gwamnati mun yi, an kawo jaket mun saya, an kawo sitika mun saya, sannan jami’an FRSC da jami’an VIO ba su bar mu ba.

“Kan safaya taya idan an kama ka sai ka biya tarar dubu biyar, sannan kullun ana bin mu da risiti na haraji muna kashe N300 a yini a ƙalla ke nan. Ba kuɗi a hannun fasinja, wajen da ya kamata ka karɓi naira N100 sai ka ga ana haɗa ka da Allah a baka N50. Mu dai mun kori PDP a kan mulki amma ba mu san irin wannan canjin da muka yi ba.

Yanzu a cikin garin Minna a buge ka a karɓe ma Keke-Napep ko Mashin duk yana faruwa da mu ‘yan kabu-kabu, amma ba wani ɗauki da muke samu daga gwamnati sai takura.

“Misali ni sana’ata yin ƙawa ga ɗunkunan mata, yau sai mu wuni mu kwana ba a yi ɗinkin ba ma balle mu samu abin kai gida, kuma wata na ƙarewa ka ga malaman haraji sun ɓullo, ga biyan kuɗin wutan lantarki to ta ina zamu fara yanzu. Mun ji Gwamnatin Tarayya ta bada kuɗin faris-kulub don a samu sauƙi ta hanyar biyan ‘yan fansho da yin wasu muhimman ayyukan da kuɗi zai yalwatu a hannu jama’a, amma har yanzu ba mu ga ayyukan ba balle ma talaka ya ce ya samu wani abu da zai iya cin abinci har ya ɗunka sutura.

“Gaskiya idan abubuwa suka wuce haka a jihar nan lallai zai zama an watsa wa talakawa ƙasa a ido ne, domin abinda suke tunanin samu ba su same shi ba, ina bawa gwamnatin jiha da duk wani da ke kusa da ita, da su ji tsoron Allah su sanar da gwamnati halin da jama’a ke ciki.

“Maganar da ake na cewar gwamnatin baya ta saba kashe kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba ban gamsu da shi ba, yanzu kuɗaɗen faris-kulub me aka yi da su, ina aka kashe su ko kuma ana nufin an yi abinda zai amfani talaka da su ɗin ne? Ba za mu iya nuna aikin biliyan ɗaya da talaka zai ce madalla ba, ko dai asibiti ne gara baya da yanzu saboda kuɗaɗen da muke kashewa a asibiti yanzu abin sai dai addu’a.

“Ina kira ga maigirma gwamna da ya taimaka ya tausayawa ƙananan ma’aikata da ‘yan fansho wajen kawo sauƙi a rayuwar talakawa.” In ji Malam Abubakar.

Dakta Isah Adamu, ma’aikaci a jami’ar Ibrahim Babangida mallakin Gwamnatin Neja kuma mai nazari akan al’amuran yau da kullun ya ce, “dole mutane su koka saboda yadda abubuwa ke tafiya, a baya an saba satar kuɗin gwamnatin ana kashewa ba bisa ƙa’ida ba. Domin idan ka duba ba a taɓa samu gwamnatin da tai aiki ba kamar wannan gwamnatin Dakta Abubakar Sani Bello, domin ayyukan da ya yi na inganta rayuwar mutanen karkara, an samar da hanyoyi don sauƙaƙawa al’ummar karkara, an gyara makarantu.

“Maganar fansho kuma akwai tsare-tsaren da ake bi wajen tantancewa kuma akwai lissafi komai dole sai an bi a hankali sosai, domin lokacin mulkin Janar Obasanjo ya kawo wani tsari da ma’aikaci zai bada wani abu ita kuma gwamnati ta sanya wani abu a cikin asusun ma’aikacin, amma gwamnatin da ta gabata an samu wasu sun wawure kuɗaɗen mutane wanda bayan zuwan wannan gwamnatin ta yi tsaye sosai wajen ganin an dawo da kuɗaɗen da aka kwashe ɗin.

“Amma maganar an biya wasu manyan sakatarorin gwamnati da suka bar aiki a ɗan wannan lokacin, indai har labarin ya inganta to akwai kuskure sosai, domin bai yiwuwa mutumin da ya bar aiki kuma ƙaramin ma’aikaci da kuɗin shi bai ta ka kara ya karya ba aka sa biyan shi, amma a biya wani mai kuɗi da yawa.Lallai indai har hukumar fansho ta yi hakan lallai akwai kuskure sosai, kuma ya zama dole a gyara.

“Maganar ƙunci da zafin da jama’a ke fuskanta a yanzu dole a fuskanci hakan saboda yanayi, amma da yardar Allah komai ya kusa daidaita, abu ne da ke buƙatar juriya da ƙarin haƙuri ba da jimawa ba jama’a za su yi na’am da muradun gwamnatin.”  A cewar Dakta Isah.

SendShareTweetShare
Previous Post

Babban Burina Duk Bayan Wata Biyu Na Ƙera Sabbin Na’urori — Adamu Husawa

Next Post

SOYAYYA DA SHAƘUWA: Hanyoyi 8 Na Sace Zuciyar Budurwa

RelatedPosts

Gwamna Masari

Satar Mutane Ta Zama Harkar Kasuwanci – Gwamna Masari

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Satar mutane, musamman ta bangaren yin garkuwa da mutane, ta...

Ba Mu Taba Samun Kowane Irin Tallafi A Kebbi Ba – Manoman Kankana

Ba Mu Taba Samun Kowane Irin Tallafi A Kebbi Ba – Manoman Kankana

by Sulaiman Ibrahim
4 weeks ago
0

Duk da irin gagarumar rawar da manoman kankana ke takawa...

JIBWIS-FCT

Kwamitin Tallafa Wa Marayu Na JIBWIS-FCT Ya Gudanar Da Taron Karshen Shekara

by Sulaiman Ibrahim
1 month ago
0

Kwamitin tallafawa marayu na Jama’atu Izalatul Bid’a Wa’ikamatis Sunnah dake...

Next Post

SOYAYYA DA SHAƘUWA: Hanyoyi 8 Na Sace Zuciyar Budurwa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version