Connect with us

LABARAI

Hana Bakin Makiyaya Tashi Zuwa Neja Ya Yi Tasiri – Ardo Babayo

Published

on

An yabawa majalisar sarakunan gargajiya a Neja, musamman na kokarin su wajen baiwa gwamnatin jihar kan matsalar tsaro.

Babban darakta mai kula da ilimin ‘yayan makiyaya da inganta rayuwar su, Ardo Abdullahi Adamu Babayo ne ya yi yabon kan nasarorin da gwamnati da jami’an tsaro ke samu kan dakile ayyukan mahara masu dauke da makamai da ke kai hare-hare ga mutanen karkara.

Ardo Babayo, ya cigaba da cewar “hakimai da dagattai a jihar sun taka rawar gani wajen warware matsalolin da ke tasowa tsakanin manoma da makiyaya a baya, gwamnati ta zauna ta nuna masu abinda ya kamata musamman kulle labi da makiyayan da ba su san ciwon kan su da ke tura dabbobi su nai wa manoma barna a gonakin su, gwamnati ta nunawa sarakunan mu illar sa da barnar da hakan ke janyowa ga arzikin kasa.

“Tun daga shekarar da ta gabata, sarakunan gargajiya bisa jagorancin shugaban majalisar sarakunan jiha, mai martaba Etsu-Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar ta taka rawar gani domin an samu saukin matsalolin sosai, saboda haka ganin ruwa ya fadi yayin da manoma ke kokarin komawa gona ba na tunanin hannun agogo zai koma baya a bana, domin mu ma a gwamnatance muna bi muna dubawa irin nasarorin da ake samu.

“Saboda haka ina jawo hankalin ‘yan uwana makiyaya musamman baki da ke shigowa jihar nan da sunan kiwo daga wasu sassa da su sani mu a jihar Neja, gwamnati ta sanya dokar hana kowani bako shigowa jihar nan da sunan kiwo ko ratsowa da dabbobi da nufin tafiya wasu yankuna sai da tare da sanya idanun jami’an tsaro, domin mu Fulanin da aka sani a kasar nan zaunannu ne da kowa ya san su da matsugunnan su kuma al’ummar fulanin mu al’umma ce da aka sani da zaman lafiya. Dan haka a karkashin jagorancin maigirma gwamna, Alhaji Abubakar Sani Bello tunda aka fara rigimar satar shanu da garkuwa da mutane ya hana wa bakin makiyaya ratsowa ko shigowa jihar kuma mun ga alfanun haka, domin ko daga wata karamar hukuma za ka tashi zuwa wata karamar hukumar a cikin jiha za ka tashi sai mun sani mun san dalilin da ya sa za ka tashi, kuma me zai kai ka wannan wajen.

“Dan haka maganar tashin fulani daga inda suke zama zuwa wani wurin gwamnatin Neja ta ja mai layi, dole sai da sanin gwamnati da kuma jami’an tsaro na jihar. Kuma gaskiya tun fara bin wannan tsarin mun ga tasirin shi a jihar nan,” in ji shi.

Ardo Abdullahi ya kuma jawo hankalin al’ummar fulani da su bi dokokin gwamnati sau da kafa domin cigaba da samun zaman lafiya a jiha. Ya ce yanzu ana cikin wani yanayi da annobar Korona ta zama barazana a kasar nan, don haka akwai bukatar kowa ya kiyaye shawarwarin masana kiwon lafiya na guje wa shiga cinkoso da tsaftar muhalli musamman daure dabbobi da yawaita wanke hannu a kan kari, “wadannan hanyoyi ne da aka bada shawarar amfani da su wajen kare lafiya da rayuwa, wanda ya sa muka baiwa sarakunan fulani shawarar su sanya idanu wajen takaita taruwar mutane a lokacin bukukuwa da takaita ziyarce-ziyarce domin ba a sanin mai dauke da cutar ko inda za a same shi, amma idan an kiyaye wannan Allah zai kawo mana dauki ta hanyar kariya,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: