Hana Kabu-Kabu: Neja Ta Kaddamar Da Jami’an Tsaron Da Za Su Aiwatar

Gwamnatin Neja

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

 

Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya kaddamar da jami’an tsaron hadin guiwa dan tabbatar da dokar hana sana’ar kabu-kabu wadanda da aka fi sani da ‘yan Okada a Minna babban shalkwatan jihar.

Gwamnan da ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Ahmed Muhammed Ketso a lokacin kaddamarwa da ya shafi ‘‘yan sanda, jami’an sibul difensi da soja da jami’an sintiri da wasu masu damara da ya gudana a filin kasuwar baje koli da ke Minna.

Yace kaddamarwar, da gwamnan ya bayyana cewar shirin na tabbatar da tsaron rayuka ne da dukiyoyin jama’ar jihar dan daukar matakan gaggawa akan abubuwan da ke faruwa na rashin tsaro saboda anfani da ‘yan kabu-kabun wajen miyagun ayyuka a jihar.

Gwamnan ya jawo hankalin jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukan su kamar yadda doka ta tsara.

” Ina jawo hankalin ku, ban da cin zarafi a lokacin gudanar da aikin, ku yi anfani da ka’idar da doka ta tsara maku”, a cewarsa.

Gwamnan yace duk wanda ya karya dokar a hukunta shi daidai da laifinsa gwamnati na tare da ku.

” Duk wanda yayi tsaurin kai wajen taka dokar nan, kowaye zai fuskanci hukuncin da aka tanadar. Ba za mu sanya ido ana take dokar ‘yancin dan Adam ba, za mu tabbatar mun kare rayuka da dukiyoyin jama’a kuma dole kowa ya bi wannan dokar,” a cewarsa

Da yake bayani, kwamishinan ‘‘yan sandar jiha, Adamu Usman ya baiwa gwamnatin jiha tabbacin jami’an sa za su yi aiki ba kama hannun yaro wajen ganin dokar tayi aiki kamar yadda aka tsara.

Gwamnatin Neja dai ta shelanta haramta sana’ar kabu-kabu a shalkwatan jihar kan matakan da ta ke dauka kan matsalar tsaro a jihar.

Masu mashunan hawa da ba na haya ba, suna damar hawa mashunan su daga karfe shida na safe zuwa tara na dare. Dokar da fara aiki tun ranar alhamis din makon jiya, tana cigaba da janyo cecekuce ga mazauna cikin garin Minna ganin yadda jama’a ke shan wahalar rashin abin hawa duba da wasu unguwanni na nesa da bakin hanya.

Exit mobile version