Abdullahi Muhammad Sheka" />

Hana Karatun Allo: Alarammomi A Kano Sun Fara Ruwan Kula-Kuzai

Musulmi

A sakamkon matsin lambar da wasu Gwamnonin kasar nan ke yi na ganin bayan harkar Makarantun allo da almajiran tsangayu, Majalisar Mahaddata Alkur’ani a Jihar Kano sun gudanar da addu’o’i tare da yin ruwan kula-kuzai domin rokon Allah ya shiga tsakanin alarammomin da Masu niyyar Hana tsarin karatun Tsangaya a fadin kasar nan.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai Jim kadan da idar da sallar da aka gudanar a Kano, Shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani na Jihar Kano Goni Sunusi Abubakar wanda kuma shi ne ya Jagoranci taron addu’ar, ya bayyana cewa alarammomi na cikin damuwa kwarai da gaske, musamman yadda wasu Gwamnonin suka kaddamar da kwasar almajirai kamar dabbobi ana mayar dasu garuruwansu, wannan ke ta haddi ne kuma cin zarafi ne kwarai gaske. Yace kundin tsarin mulkin Nijeriya ne ya baiwa kowane dan kasa damar zama aduk inda ransa ke bukata tare da zabar addini da kuma ilimin da yake da yakinin zai zama alhairi agareshi duniya da lahira.

Duk da wannan dama da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya baiwa kowane dan kasa, sai gashi ba kunya ba tsoron Allah an fakaice da annoba Korona ana musgunawa almajiran tsangayu, duk da cewa ga makiya son zaman lafiya suna Kashe al’umma, Amma sai almajiri shi aoa sawa Karan tsana. Don Haka sai ya bukaci jama’a aduk inda suke domin su ci.

Haka zalika shugaban Mahaddata Alkur’ani na Jihar Kano Goni Sunusi Abubakar ya bukaci ‘yan uwa Alarammomi a duk inda suke a kara himmatuwa wajen addu’o’i domin ganin duk Wanda ke da hannu cikin musgunawa almajirai to Allah ga ga sunan. Yace muna Kira akalla asamu saukar Alkur’ani 1.111 duk mako domin neman taimakon Allah Kan wannan mummunan tanadi da wash ke yiwa Alkur’ani da ahlinsa

Exit mobile version