Hana Sana’ar A Daidaita Sahu A Kano: Jita-Jita Da Gaskiyar Lamari

Wata guda da wasu kwanaki da suka gabata a jihar Kano, bayanan da ke fitowa daga bakunan da daman mutane, ciki har da masu sana’ar hayar Baburin A Daidaita Sahu shi ne, Gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje, na da wani shiri a karkashin-kasa, na binne sana’ar ta A Daidaita Sahun da ranta, duk da cewa dubban daruruwan jama’a ne a kullum ke samun na toshe-bakin-salati a cikinta.

Dalilan da al’umar garin Kano ke gabatarwa, wadanda ke nuna da gaske ne cewa, gwamnatin ta Kano, hada da hukumar Karota ta Kano, tuni sun kammala shirinsu na yi wa wannan sana’a ta A Daidaita kwaf-daya.

Sai dai, jita-jitar da ake gabatarwa kan banbanta da juna, abinda za a tashi da shi yau daban, na gobe ma daban. Babu shakka, zafafar  banbance-banbancen ra’ayoyin siyasa da a yau ake kan fuskanta, ko fama da su, na taka-rawa ainun, wajen kara hasa wutar duk wani rudu ko jita-jita da ke reto a kunnuwan jama’ar jihar ta Kano a yau, musamman ma a ce lamarin ya shafi hukuma ne kai-tsaye. Ka da a cika mai karatu da surutu, ga wasu daga manyan maganganun da ake rade-radin nasu a yau cikin kwaryar-kano da kewaye, game da tata-burzar da ake tunanin na wakana, tsakanin gwamnati da “yan a daidaitan kamar haka;

i- Akwai rade-radin da ke ishara zuwa ga cewa, gwamnatin Gwamna Ganduje, na gab da haramta sana’ar ta masu A Daidaita Sahu kwata-kwata a jihar Kano.

ii- Akwai yiwuwar dankarawa masu harkar A Daidaitan, harajin da a kullum sai mai baburin ya bai wa gwamnati naira dari daya, kafin a sahale masa cigaba da hayar tasa.

iii- Ba za a hana sana’ar ta A Daidaita Sahun ba, sai dai za a zaftare adadin masu haya da Baburan matuka, daga miliyan guda zuwa dubu biyu ne kacal.

Irin wadancan korafe-korafe da ke yawo a tsakanin jama’ar ta Kano, sai hakan ya dan tuka cikin zuciyar wannan marubuci, ya fara tunanin, shin, wai me zai hana ya tunkari Hukumar ta Karota gadan-gadan, tun da ba a sama ta bakwai (7) ne suke da zama ba, don jin hakikanin gaskiyar zance, game da irin wadancan korafe-korafe da a kullum suna dada yawo ne, tare da yin tasiri cikin zukatan al’umar Kano?.

Ba yabon kai ba, wannan marubuci, kan so yin abu ne da hujja, wanda wannan dalili, na daga ababen da suka tilashi zuwa ga jin ta-bakin hukuma game da rade-radin. Ko ba komai, jama’a za su kai ga fahimtar tartibin batu game da irin wannan gutsuri-tsomar da ta-ki-ci ta-ki-cinyewa game da sabgar ta “yan A Daidaitan a Kano!.

Wannan marubuci, ya gabatarwa da Hukumar Karota ta Kano, irin wadannan tambayoyi, don jin nasu lafazi game da dambarwar. Bugu da kari, ita ma hukumar ta Karota, ba ya ga amsa tambayoyin daki-daki, sun ma kara da yin wasu karin haske na daban. A sha karatu lafiya.

Marubuci; Jita-jita na ta kan yawo ciki da wajen Kano cewa wai, gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje, na kokarin hana hayar Baburan A Daidaita Sahu a Kano. Shin, menene gaskiyar zancen?.

Karota; Gaskiyar magana akwai burbushin wannan magana tattare da gwamnatin Kano a farkon lamari. Sai dai akwai bukatar yin karin bayani. Akwai wani kakkarfan Kwamiti na tsaro da maigirma Gwamnan Kano ya kafa, wanda ma shi da kansa ne ke jagorantar Kwamitin. Cikin Mambobin Kwamitin, akwai Kwamishinan “Yan Sanda na Kano; akwai Daraktan masu tsaro na farin kaya, SSS, na jihar Kano; akwai ma MD na Karota na Kano da sauran manyan mutane cikin wannan Kwamiti na tsaro.

Bayan gabatar da zuzzurfan bincike ne, wannan Kwamiti na tsaro, ya yi kacibis da wasu gamsassun bayanan da ke tabbatar da cewa, cikin kashi dari (100%) na miyagun laifuka da ake aikatawa cikin wannan jiha tamu ta Kano, wadanda suka jima da zama barazana ga sha’anin tsaro na jihar, masu Baburan A Daidaita Sahu ne ke aikata kusan kashi casa’in da biyar (95%) na laifukan. Ganin haka ne ya sanya wancan Kwamiti numfasawa, gami da gano cewa, babu shakka, haramta wannan sana’a ta A Daidaita Sahu kacokan a Kano, za ta taimaka matuka gaya, wajen magance da daman afkuwar irin wadancan miyagun laifuka. Sai dai a yanzu kam, babu wannan magana ta yiwuwar hana gudanar da hayar Baburan a Kano, kamar yadda aka tasamma zartar da hakan a baya. Kowa ma yanzu shaida ne a Kano cewa, zai ga an bai wa wani adadi na masu Baburan A Daidaitan, na su je su yi rijistar ababen hawan nasu, don cigaba da sana’ar tasu, amma, cikin tsari, ba tare da yin la’akari da wani banbancin siyasa, ko wani abu mai kama da haka ba.

Marubuci; Daga cikin rade-radin da a yanzu haka ke yawo cikin jihar ta Kano shi ne wai, idan ma gwamnatin Kano ba ta haramta sana’ar ta A Daidaita Sahu gabadaya ba, akwai yiwuwar ta zaftare adadin masu yin sana’ar, daga Babura miliyan guda, zuwa Babura dubu biyu kacal.

Karota; To ai ma har kawo yin  wannan magana, babu wani mahaluki da ke da hakikanin adadin wadancan Babura na A Daidaitan da ke kai-kawo a Kano! Balle ma ya sani cewa, shin, sun kai adadin miliyan gudan? Shin, ko ma sun kai miliyan biyu ne? Ko duka-duka ba su kere dubu dari biyar ba? Mai yiwa ma dari biyu ne, to amma waye zai tabbatar da hakan? Ko ma duka zancen kanzon kurege ne?. Dole mu na da bukatar tattara bayanai matabbata, muddin mu na son cewa, ai wadannan masu Babura a Kano, sun kai adadin mutum kaza ne, amma ba ta irin sigar lissafin dokin-rano ba.

Matabbaciyar magana ita ce, babu shakka yanzu haka mu na kokarin warar Babura guda dubu dari biyu (200,000) ne, daga adadin wadanda ke yin sana’ar a Kano, sai su je su yi rijista, kamar yadda ma yanzu haka sun fara yin rijistar. Wancan adadi na mutane 200,000 da suka yi rijistar, to fa sune wadanda za su cigaba da yin sana’ar a Kano. Daga nan kuma, sai mu yi tunanin, to kuma menene abin yi na gaba da za mu yi?.

Marubuci; Da alamun, ko ku na son tsabtace harkar ne?

Karota; Ya ma wuce sontsabatace harkar kawai, kusan mu ce, za mu wajabtawa kanmu gyaran harkar ne. Mu yi duba mana zuwa ga kima da Allah Madaukakin Sarki Ya yi wa Dan’adam, Ya kuma bukaci a kare masa lafiyarsa da dukiyarsa hada da mutuncinsa, amma me ke faruwa yanzu? Sai aka wayigari cewa, a na amfani da irin wadancan Babura na A Daidaita Sahu wajen salwantar da rayukan al’umar jihar Kano, tare da dukiyoyinsu babu kakkautawa. Shin, ya dace mu kuma kawai sai mu kame hannuwanmu ne, mu zuba idanu, mu na kallo hakan na cigaba da wakana?.

Munanan laifuka irin su fashi da makami; sace kananan yara; yin garkuwa da mutane da ma sauran miyagun ta’adu, sai ya zamana cewa, a na yin amfani ne da irin wadancan Babura na A Daidaita Sahu a Kano wajen aikata su!.

Ai duba da irin wadancan miyagun ayyuka ne, babban Kwamitin tsaro da maigirma Gwamna ya kafa, ya fara tunanin alfanun da ke tattare da ruguje sana’ar ta A Daidaita Sahun gabadayanta a Kano. Amma sai wasu manya suka nazarci cewa, akwai sama da mutane miliyan biyar (5,000,000) a Kano, wadanda ke cin-abinci karkashin wannan sana’a ta A Daidaita Sahu.

Daga cikin masu cin-abinci cikin sana’ar, faro tun daga wadanda ke siyen Baburan su ba da haya; ga masu karbar hayar baburan; ga masu gyaran baburan; ga masu sayar da sassan baburan, “spare parts”; ga manyan dilolin baburan da makamantansu. Wannan nazari ne ya kara bukatar da gwamnati, zuwa ga kara yin karatun ta-natsu cikin sabgar.

Marubuci; Akwai masu tunanin cewa, akwai wasu da za a iya kira da bakin-haure, wadanda suka taimaka ga kara dagulewar harkar hayar Baburan na A Daidaita a Kano.

Karota; Dole ne ai hukuma ta fitar da wani sahihin tsari, wanda zai gyara gari. Bai dace ba a ce an bar abubuwa haka na tafiya sakaka. Ga gari ya cika makil da mutane gami da ababen hawa, saboda an bar abubuwa kara-zube, kawai sai mutum ya sayi A Daidaita Sahu, ya buga ya tafi. Ka ce da mutum ya kai ka Magwan ko Gwammaja, amma wai sai ka ji yana tambayar ka, shin, wai ta ina ne za a bi a je? Ba Dan garin ba ne, bai ma san garin ba. Kai hatta nan nan da Kofar Nassarawa, wanda duk gidadancin mutum ya kamata a ce ya san ta, nan ma sai ka ji mutum na cewa da kai, ta ina ne za a bi a je Kofar Nassarawan?. Ko ka san ma kusan za a iya cewa wadanda suke ba “yan wannan jiha ta Kano ba, sun kere jama’ar Kano yawa a harkar?

Na’am, kowace jiha ce kake a Nijeriya, ya halatta ka zo Kano ka yi sana’arka. Kai! Ko ma daga wata Kasa ne kake, cikin jerin Kasashen Afurka ta Yamma, ” West Africa”, za ka iya zuwa nan jihar Kano ka gabatar da sana’arka, duba da yarjejeniyar da aka jima da kullawa a tsakanin wadannan Kasashe. Ballantana kuma a ce Dan Nijeriya a Kano, ko Dan Nijeriya a Lagos, ko Dan Nijeriya a Katsina da sauran jihohin wannan Kasa tamu. Sai dai, Dole ne sai mun san waye mutum? Daga ina ne ya ke, kuma me yake yi?.

Marubuci; Maigirma sabon MD, Hon. Dr Baffa Babba Dan’agundi, na wannan Hukuma ta Karota ta Kano, shin, yana daga masu goyon bayan cigaba da sana’a A Daidaitan a Kano, ko sabanin haka ne?

Karota; Babu shakka sabon MD na wannan gida Hon. Dan’agundi, na daga masu son dorewar wannan sana’a ta masu A Daidaita Sahu a Kano, amma bisa bin tsarin Doka da Oda. Bugu da kari, duba da tarin mutane da ke ci da sha a sana’ar, hakan, ya taimaka ga mara-baya da sabon MDn ya yi, don mikewar harkar. Da farko, ya nemi zama ne da daukacin Kungiyoyin masu hayar Baburan da ake da su a nan Kano. Yayin zaman, ya bukace su da su zo da wasu ingantattun ka’idoji gami da nagartun tsare-tsare, wadanda za su dabbaka su da kansu a aikace, wajen cigaba da gudanar wannan sana’a tasu ta A Daidaita Sahu a Kano.

Bayan sabon MDn ya zauna da wadancan Kungiyoyi an daddale, daga nan, sai ya je wajen Gwamna, tare da nemawa masu Baburan alfarmar a bar su su cigaba da aiwatar da sana’ar tasu, bisa sharadin da suka yi yarjejeniya a kansa, na dabbaka kyawawan ka’idoji da tsare-tsare, domin tsabtace sabgar.

Daga cikin Kungiyoyin “Yan A Daidaita Sahun da aka yi wancan zama da su, akwai Kungiyoyir Toakan, da Toan, da Acomoron, da Naktamaros, da Kungiyar masu Koren Baburin A Daidaita Sahu, da kuma Kungiyar wadanda ke sayen Baburan na A Daidaita Sahu suna badawa haya. A zaman, an bukaci Kungiyoyin, da su cure su dunkule a karkashin inuwa guda.

Bayan nazarin wancan zama da Kungiyoyi da sabon MDn ya yi ne, tare da jin bayanin sabbin ka’idoji da sauran tsare-tsare da masu sana’ar ta A Daidaita suka hakkake dabbaka su, sai ya zamana Gwamna ya gamsu, tare da tabbatar musu da cewa, muddin za su cika alkawari wajen bin sabbin ka’idojin sau-da-kafa, gwamnati a shirye take ta bar su su cigaba da mirginawa.

Marubuci; Akwai daga cikin kashin-bayan irin jita-jitar da ake yi cewa, gwamnatin ta Kano, na gab da wajabtawa masu Baburan na A Daidaita biyan harajin naira dari guda a kullum, muddin suna so a bar su, su cigaba da gudanar da sana’ar tasu a Kano.

Karota; Batun za a sanya musu harajin naira dari gaskiya ne. Amma fa yana da kyau mu sani cewa, shi fa haraji Doka ne, kuma naira dari ne kacal. Da irin wadannan “yan kudade na haraji ne gwamnati ke samun sukunin gabatar da daman ayyuka ga al’uma. Misali, yanzu haka akwai wani shiri da gwamnati ke yi, na yunkurin samar da na’urar bibiya, ” tracker” cikin wannan harka ta masu A Daidaita. Wannan na’ura, ta kai tsabar kudi har kimanin naira dubu takwas, kuma za a samar da ita ne kyauta.

Da taimakon irin waccan na’urar tiraaka ne za a gano, shin kuwa, wannan Baburi na A Daidaita Sahu, yana aiki ne, ko ba ya yi? Sannan kuma a ina ne yake? Wane irin abu ne aka aikata da Baburin A Daidaita Sahu kaza, mai irin lamba kaza? Duka irin wadannan abubuwa masu amfani da muhimmanci, ai da wannan naira dari ce da aka amsa daga gare su ne a matsayin haraji, ake gabatar musu da irin wadannan aikace-aikace.

Harajin gwamnati, ba wani abu ba ne sabo, gashi gwamnati na yi maka Titi kana hawa. A sanya maka fitilu bisa tituna, da daddare kana ganin hanya tartar. Kana yin sana’arka saboda an samar da tsaro. To shin, kai kuma idan ba ka bayar da haraji ba, wace irin gudunmuwa ce ke nan za a ce kana bayarwa? Idan ka je jihar Delta, ai naira dari uku ne suke biya a can. Ka je Abuja, naira dari biyu ce suke biya. Satin da ya gabata, mun yi gani da MD-MD na jihohi kamar na Karota, sun tabbatar da hakan.

A zangon mulkin Dr Abdullahi Umar Ganduje na farko, sai ya zamana an fara karbar naira dari a duk rana a matsayin haraji, sai hakan ya nemi afkar da husuma. To shi ne a wannan karon a ka yi tunanin cewa, maimakon a rika amsar harajin a duk rana, sai gwamnati ta nemi masu Baburan, na su rika hade harajin Shekara guda suna biya, maimakon karbar kullum, ka iya haife Da-maras-ido!

Yana da matukar muhimmanci mutane su fahimta cewa, dukkan wata Kasa ko jiha da aka ga ta cigaba, hakan na faruwa ne gwargwadon irin harajin da take tarawa. Kuma ko da a nan Kano, mutane shaida ne game da irin katafaren ayyukan da za a ga gwamnati ke gabatarwa da al’uma.

Gadar Alhaji Aminu Alhassan Dantata da ke a Bata, wadda ba ma wai a nan cikin gida Nijeriya ba, hatta a Afurka a bar alfahari ce, ai za a iske daga irin wadancan kudade na haraji da ake amsa ne daga al’uma, ake samun sukunin samar da su. Sannan, ga Gadar Bukabu da aka gina ta da biliyoyin kudade. Ga Gadar Dangi, wadda take hawa uku, yanzu haka an kammala kashi casa’in (90%) na aikin.

Mutane su sanya ransu-a-inuwa, su kwana da sanin cewa, irin wadannan kudade fa da ake cazar su, suna wucewa ne kai-tsaye zuwa ga Asusun Bai-daya da ake kira da TSA, “Treasury Single Account”.

Marubuci; Rijistar da a yanzu haka gwamnati ke yi wa masu Baburan A Daidaita Sahu a Kano, shin, daukacin Baburan ne za yi wa rijistar, menene hikimar yi musu rijistar, sannan zuwa wane lokaci ne za a yi a na yi musu rijistar?

Karota; Adadin masu Baburan A Daidaita dubu dari biyu cifcif ne za a yi wa rijistar.

Hikimar yin rijistar shi ne, iya wadanda suka hanzarta zuwa suka samu damar yin rijistar, wato suka sami kansu cikin wancan adadi na 200,000 da aka iyakance, to sune kawai wadanda gwamnati za ta yarjewa cigaba da gudanar da sana’ar ta A Daidaita Sahu a Kano. Wannan, na daga hikimar yin rijistar. Bugu da kari, yin wannan rijista, zai taimakawa gwamnati ainun, wajen iya tafiyar da aikace-aikacen Kungiyar zuwa ga dabbaka Doka da Oda cikin sauki, sabanin yanayinsu na baya na cunkoso. Harkar tsaron jiha ma zai samu ainun-ainun, duka ta hanyar yi musu rijistar cikin tsari. Akwai hikimomi birjik, cikin ware wannan adadi na “Yan Baburan, a yi musu rijista.

Daga tara ga Watan Disamba na wannan Shekara (9th December, 2019) ne aka fara aikin yin rijistar. Sati biyu ne aka ware musu cewa, za a fara aikin rijistar, tare da kammalawa.

Ranakun farko na yin rijistar, an ware wasu kafe-kafe, ” Cafe” ne kididdigaggu, da a wajensu ne kawai za a yi wa masu Baburan rijista. Duba da matsanancin cunkoso da aka rika samu ne, sai gwamnati ta lamunce kowane mai Baburi ya je kowane kafe, ya yi rijistar.

Ta tabbata cewa, daga ranar 9 ga Watan Disamba na Shekarar 2019, zuwa 11 ga Watan dai na Disamba, 2019 (misalin kwanaki uku ke nan), an sami nasarar yi wa masu Baburan rijista, na adadin mutum dubu biyar da dari hudu da doriya (5,400…) a fadin jihar Kano.

Marubuci; Akwai daga cikin mutanen gari da ke zargin “yan wannan hukuma ta Karota, da tamkar suna danawa jama’ar gari tarkon son ganin sun kama su da laifi, yayinda suka fito bakin-aiki. Ko me ya sa hakan ke faruwa?

Karota; Idan mutum yana yin abu daidai, ko kadan “yan Karota ba za su kama ka ba. Hanzarin mutane na rashin son bin ka’idar danjar titi, shi ke jawowa a kama su. Su kuma (“yan Karotar) saboda rashin adalcinsu, na son ganin sai sun kama mai laifi. Abu biyu ne ke haduwa, ga wadanda ba su da kokarin su yi adalci, mu na da su. Sai kuma bangaren masu ababen hawa, wadanda ba su da da’ar fadawa kansu gaskiya. Duka-duka mutum hakurin minti biyu ne zai yi, ko uku ko biyar, danja ta ba shi hannu ya wuce. Wannan rashin hakuri na “yan mintina da mutum zai jira, sune za su hana shi bata lokacin kusan awanni uku. Saboda daga inda za a kama ka, zuwa inda za a kai ka, zuwa inda za ka je ka biya tara, dole sai ka kashe awa uku zuwa hudu.

Duk mutum mai hankali da zai tuka A Daidaita Sahu, ya kamata ya san bin Doka da Oda. Babu bukatar har sai an rika rokon mutane, na su kiyaye dokoki da ka’idoji da gwamnati ke gabatarwa, don son cigaban al’umar Kasa.

Marubuci; Ko akwai wasu abubuwa da Hukumar ta Karota za ta kara, ba ya ga  wadanda aka yi tsokaci a kansu a baya?

Karota; Wasu misalai biyu da zai yi kyau a gabatar, wadanda za su kara tabbatar da babbar bukatuwa da ake da ita, wajen gaggauta kawo gyara ga wannan harka ta A Daidaita Sahu a Kano.

Misali na farko, wani fasinjan A Daidaita ne dauke da wata katuwar Talabijin, ya hau Baburin, daga BDB Road zuwa Post Office Road. Saboda girman Talabijin din da yake dauke da ita, sai ya zamana sai dai a sa ta cikin Babur daban, shi ma ya hau wani daban.

Bayan wancan fasinjan sun fara tafiya, daga lokacin da aka shiga gargada, sai mai Baburin da ke dauke da Tibin tasa ya arce. Allah Ya sa wannan Fasinja ya haddace bakar lambar da ke rubuce a jikin Baburin. Saboda haka, ko da ya zo Hukumar Karota ya gabatar da korafinsa, nan take ya karanto lambar Baburin Barawon Talabijin din tasa.

A kwana a tashi, sai mutanenmu suka kama Babur, mai irin wannan lamba da mai Tibi ya ba da. Wani abin takaici kuma abu mai rikitarwa shi ne, sai da muka kama Babura daidaidai har guda goma sha-tara (19), duka lambobinsu iri guda ne. Ke nan, waye Barawon Talabijin din a cikinsu? Dolen dole ne a zo a samu gyara na baidaya cikin harkar masu Baburan.

Misali na biyu, har yau har gobe, akwai Baburan A Daidaita Sahu da ke da lambobi iri guda. Ta yaya ne za a magance lamarin ta’addanci a haka cikin jihar, ba tare da daukar sabbin matakai ba?.

A karshe, ta tabbata, yayinda aka ba mu dama, muna yin iyakacin-iyawarmu, wajen kawo gyara. Shigowar sabon MD, Dr Hon. Baffa Dan’agundi cikin wannan gida na Karota babu jimawa, sai ya tsinci kansa cikin guda daga “yan Kwamitin Hana-sha, na jihar Kano. Cikin kankanin lokaci, wannan gida na Karota, ya sami nasarar kame jabun magunguna, wadanda suka kare amfani, amma aka sauya musu fakiti, a ka mayar da su sabbabi, na sama da naira miliyan dubu shida ((6000,000,000m).

Kammalawa. Bissalam.

Exit mobile version