Hana Tiwita: Wainar Da Aka Toya A Taron Nijeriya Da Jakadun Kasashen Turai

Tiwita

Daga Abdulrazak Yahuza Jere

A ranar Litinin, Jakadun Amurka, Ingila, Kanada, Jamhuriyar Ireland da Tarayyar Turai a Nijeriya, sun dage kan cewa dakatar da shafin Tiwita a kasar da ke Afirka ta Yamma ya saba wa ‘yancin fadin albarkacin baki.

Jakadun sun bayyana hakan ne a wata ganawa da suka yi da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Geoffrey Onyeama, a jiya a Abuja.

Ministan ya gayyaci jakadun zuwa taron ne kan maganganun da suka yi kwanan nan game da dakatar da shafin a Nijeriya.

Da take magana a madadin wakilai biyar din a wata ganawar sirri da Onyeama a ranar Litinin, Jakadiyar Amurka a Nijeriya, Mary Beth Leonard, ta ce suna nan a kan bakansu cewa haramcin da gwamnatin Nijeriya ta yi wa shafin Tiwita ya keta ‘yancin fadin albarkacin baki na ‘Yan Nijeriya ba tare da la’akari da damuwar da gwamnati ke nunawa cewa ana amfani da dandalin don aikata kalaman nuna kiyayya da aikata laifi ba.

“Mun amince da matsayin gwamnatin Nijeriya a hukumance kan yadda ake amfani da shafukan sada zumuntan amma muna nan daram a matsayarmu cewa samun damar samun bayanai na da matukar muhimmanci kuma watakila ya fi muhimmanci a lokacin da ake cikin wahala,” in ji ta

“Mun kasance a nan a matsayin abokan aiki kuma muna son ganin Nijeriya ta yi nasara. Ya bayyana a sarari cewa mu manyan abokan tarayyar Nijeriya ne kan lamuran tsaro kuma mun fahimci lokutan da suke fuskantar kalubalen tsaro da ke fuskantar Nijeriya. Duk da yake suna da ban tsoro, ba za a iya shawo kansu ba kuma wani bangare na hanyar da za a shawo kansu shi ne hadin gwiwar mutanen da kuke ganin an wakilta a nan, ”in ji Leonard.

Jakadun sun kasance masu kyakkyawan fatan ganin Gwamnatin Tarayya ta cimma matsaya guda a tattaunawa da Tiwita.

A nashi bangaren, Minista Onyeama ya tabbatar da cewa gwamnatin Nijeriya na tattaunawa da Tiwita kan ingantattun hanyoyin magance matsalar.

Ya shaida wa jakadun cewa gwamnatin Nijeriya ba ta adawa da amfani da shafukan sada zumunta, amma tana son ganin an yi amfani da ita don kyakkyawar duniya da sadarwa mai amfani.

Ya ce, “Mun san karfin magana da kuma lokacin da kuke da irin wannan ikon na sarrafawa da saukaka hanyoyin sadarwa ga mutane sama da biliyan. Don haka, muna daukar wannan matakin ne don ganin yadda za mu iya daidaita wannan kafar watsa labaran domin nuna kyawawan halaye da kuma dakatar da amfani da su a matsayin wani dandamali na wargazawa da kuma taimakawa aikata laifuka. ”

Kamfanin na Tiwita sun goge wani rubutu na yakin basasa da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi. Daga baya gwamnati ta dakatar da dandalin, saboda “ci gaba da amfani da dandalin don ayyukan da za su iya lalata kasancewar Nijeriya”.

Kodayake mahukuntan kasar sun hana kwastomomin tiwita yin amfani da shafin, akwai wasu ‘yan Nijeriya da dama da suka koma amfani da hanyoyin sadarwa masu zaman kansu don tsallake shingen.

Nijeriya, da ke da mutane sama da miliyan 200, tana da masu amfani da kafar sada zumunta ta Tiwita kimanin miliyan 33 ya zuwa watan Janairun 2021. WhatsApp shi ne dandalin da aka fi amfani da shi a kasar, tare da masu amfani da miliyan 90 a cewar wata kididdiga. Har ila yau a cewar kididdigar, kusan kashi 61.4 na masu amfani da shafukan sada zumunta na Nijeriya suna amfani da Tiwita, kashi 86.2 na amfani da Facebook, kashi 81.6 na amfani da YouTube, kashi 73.1 na amfani da Instagram, kuma kashi 67.2 na amfani da Facebook Messenger.

Exit mobile version