Tare da Kwamared Sunusi Mailafiya
Maganar da Mai Girma Shugaba Buhari yayi kan rashin ƙin biyan Albashi ga wasu Gwamnonin kasar nan, yanuna kiri-kiri yanda Gwamnonin Kasar nan ke wasa da haƙƙoƙin jama’ar su, yanda basu dauki ma’aikatan dake aiki a karkashinsu da mahinmancin dahar zasu shiga damuwa idan har albashin wannan ma’aikatan yasamu tangardar da har yawuce lokacin ɗaya kamata abasu ba.
Abin da mamaki yanda zakaga karamin ma’aikaci yashafe kwanaki 30 ba tare da Albashinsa yashigo gareshi ba, a wasu garuruwan har akan shafe wata daya da kwanaki batare da sun samu Albashin suba, hakan kuma yama fi faruwa ga kananun ma’aikata waɗanda dama albashin nasu bai taka kara ya karya ba. Duk Albashin dazai wuce kwanaki 30 cif-cif, dole kananun ma’aikata su shiga cikin takura, ɗimuwa da tashin hankali, dole ne su shiga cikin halin ƙaƙanikayi wanda za ka ga wasun su har suna kunyar iyalansu, saboda da wannan Albashin kaɗai suka dogara, shine kaɗai abinda suke dawainiyar iyalansu da ‘yan uwansu makusanta.
Da yawan kananun ma’aikata da Albashinsu bai wuce dubu 18,000 ba, sun fi kowa damuwa, idan har zaka ƙissima dubu 18,000 a matakin magidanci mai yara biyu, tayaya dubu 18,000 zata riƙe shi, da kuma iyalinsa na tsahon wannan kwanakin? Duk da wannan albashin zakaga
Maganar da Shugaba Buhari yayi cewar in shine yaƙi biyan ma’aikata ba zai iya bacci ba, wannan magana itace ainihin gaskiya, idan har muka dauketa domin fassarata zamuga cewar lalle haƙƙi ne akan dukkanin wani Shugaba daya biya ma’aikacin dake karkashinsa alokacinda ya kamata, domin wannan ma’aikacin bayada wata madogara daya wuce wannan aikin, dasu yake daukar dawainiyar yaransa, ciyar dasu, ya kuma tufatar dasu, lafiyarsu da kuma kudaden makarantarsu, da sauran lalurori da za su iya zuwa akowane lokaci, wasun su dayawa ahaka suke gagganɗawa su biya kudin hayar gidajensu, duk fa acikin wannan Albashin, kuma duk acikin wannan yanayin na tsadar kayan masarufi, hakan ke nuna da yawan iyalai basu iya dawainiyar da iyalansu kaso 50 ma, ballantana ayi tunanin mutum zai wuce iyakar da lalurorinsa zasu zama wasunsu basuda amfani, to amma sai yakai an kasa cike farillan ma ballantana har a taɓa
sauran lalurorin, dole akwai tausayi idan har akwai tausayin, a kuma duba yanda yanayin rayuwa ya canza, da kuma yanda iyali suke da mahimmanci a rayuwa, dauke musu dukkanin lalurorinsu shine aure, kuma shine ke zamar da dawwamammen aure.
Dole ne Gwamnoni suji tsoron Allah, su kuma duba nauyin daya hau kansu, su kuma duba idan sune acikin irin wannan halin, ya za su yi da iyalansu, dolene sai sunji a zuciyarsu cewar dukkanin wani ma’aikaci dake karkashin su, haƙƙin sune su biyashi Albashinsa kuma akan lokaci, idan kuwa har wata lalura tashigo wacce takawo rashin biya akan lokaci, lalle ne su nemi gafarar waɗannan ma’aikatan, domin in basu ba su ba, sata zasuyi su dauki dawainiyar iyalansu ? Tunda har suka zage damtse suke bautawa kasar su, kuma suke neman halaliyar su, to dole ne
abasu haƙƙinsu alokacinda yakamata batare da sai sun dinga roƙon gwamnati tamkar sunayin roƙo ba. Wannan shine babban dalilin daya ƙirƙiri aikata laifuffuka da yawa, wannan itace dalilin dayasa dayawa kananun ma’aikata ke aikata laifin karɓar rashawa, wannan dalili ya sanya saboda kunyar iyalansu, da kuma rashin madogara sun gwammace suyi ‘yar murya abasu rashawa, sun gwammace su aikata laifi don tsira da mutuncin su agurin iyalansu, wannan ta sanya dayawan su suka zama ‘yan maula, suka zama tamkar almajirai saboda yanda suke bi lungu kwararo-kwararo suna roƙo domin dauke dawainiyar iyalansu, wanda kuma Gwamnatin ce silar tsundumar
kansu cikin wannan ibtila’in.
Ina kira da Gwamnonin Kasar nan, dasuji tsoron Allah, su kuma tuna cewar kuri’un waɗannan ma’aikatan sune suka kaisu wannan gurin, ta dalilin waɗannan ma’aikatan suka samu duk wata dama dasuke kai ayanzu, don haka dole ne su kyautata musu, dole ne su san cewa haƙƙoƙin su yafi komi mahimmanci agunsu, babu maganar jam’iyya ko yare, babu maganar wane ya zaɓeni, wane bai zaɓe ni ba, wannan haƙƙinsu ne a matsayinsu na ma’aikatan kasa, haƙƙinsu ne amatsayinsu na waɗanda suka ba da lokacinsu da rayuwarsu don ci-gaban kasa, don haka dole ne
gwamnati ta lura dasu, kafin sufara bijirewa gwamnati akan albashin da aikinsu ya cancanci abinda yafi haka, gwanda suyi abinda ya dace, a kuma lokacin daya dace.