CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Hankaka Mai Da Dan Wani Naka

by CRI Hausa
February 3, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Hankaka Mai Da Dan Wani Naka
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A duk lokacin da aka ambaci batun dan kasa, ana nufin wanda aka haifa a kasa, mace ne ko namiji, ko wanda ya samu iznin zama a wata kasa a hukumance, ko bisa radin kansa, wato ya zabi zama a wata kasa, saboda dalilai na yin kasuwanci, ko nazari , ko wasanni, ko aikin kimiya ko dai wani tsari da kasar ta tanada na baiwa jama’a iznin zama ’yan kasarta kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.

Wasu kasashen sun yarda da tsarin mallakar fasfo na kasa fiye da daya, wasu kuma hakan ya saba doka. Haka kuma ba wata kasa da za ta tilastawa wasu zama ’yan kasarta. Yin haka ya saba doka.
Wani mataki da kasar Burtaniya take shirin bullo da shi na zama “Hankaka mai da dan wani Naka” ya sa, daga ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2021, kasar Sin ta sanar da cewa, ba za ta amince da fasfon da ’yan kasar Burtaniya da aka haifa a kasashen waje ba (BNO), a matsayin takardar da mafiya ke amfani da ita ko katin takardar shaidar zama dan kasa, kuma tana da ikon kara daukar matakin da ya dace kan wannan batu.
Ita dai kasar Sin ta dauki wannan mataki ne, bayan da gwamnatin Burtaniya ta sanar da cewa, za ta fara karbar takardun bukatun neman zama dan kasa da mazauna yankin Hong Kong na kasar Sin suka gabatar daga mata daga ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 2021
Burtaniya ta manta cewa, yankin Hong Kong ya dade da dawowa karkashin ikon kasar Sin, kuma yankin yana karkashin ikon kasar Sin ne, a don haka, bangaren Burtaniya ya keta alkawarin da ya yi, inda ya nace wajen samar da fasfo ga mazauna yankin Hong Kong, domin su zama ’yan kasar Burtaniya, har ma ta fafada tsarin gabatar da takardun neman bukatar fasfon.
Kafin yankin Hong Kong ya dawo karkashin ikon kasar Sin, Sin da Burtaniya sun cimma wata matsaya kan fasfon ’yan Burtaniya da aka haifa a kasashen waje (BNO), inda Birtaniya ta yi alkawarin cewa, mazauna yankin Hong Kong ba sa cikin wadanda za su amfana da wannan nau’i na fasfon, wanda dai za su samu damar zama a kasar Burtaniya..
Wannan mataki da Birtaniya ta bullo da shi a halin yanzu, tamkar shiga sharo ba shanu ne, kuma ya saba hadaddiyar Sanarwar da sassan biyu wato Sin da Birtaniya suka amince, a don haka, kasancewar yankin musamman na Hong Kong, wani bangare ne na kasar Sin, tana da izinin daukar martani idan bukatar hakan ta taso.
Sanin kowa ne cewa, irin wannan mataki, na neman mayar da al’ummar yankin Hong Kong tamkar rukuni na biyu na ’yan kasar Burtaniya, ya sauya tsarin ’yan asalin Burtaniya da aka haifa a ketare da aka cimma tsakanin bangarorin biyu. Haka kuma matakin ya keta ’yancin kasar Sin, kuma tsoma baki ne a harkokin yankin Hong Kong da ma na kasar Sin baki daya, sannan ya saba dokoki na kasa da kasa da muhimman ka’idojin hadin gwiwar kasa da kasa.
Duk wata kasa mai cikakken ’yanci ba kasar Sin kadai ba, dole ne ta yi Allah wadai matuka da ma adawa da wannan yunkuri na Burtaniya. (Ibrahim Yaya)

SendShareTweetShare
Previous Post

Zimbabwe Zata Karbi Riga-kafin COVID-19 Daga Kasar Sin

Next Post

Cin Kwallaye Da Yawa Yana Da Mutukar Amfani –Solkjaer

RelatedPosts

Sabon Nau’in Rigakafin Cutar COVID-19 Da Sin Ta Samar Zai Taimaka Wajen Yakar Cutar

Sabon Nau’in Rigakafin Cutar COVID-19 Da Sin Ta Samar Zai Taimaka Wajen Yakar Cutar

by CRI Hausa
3 hours ago
0

Daga CRI Hausa Shugaban cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka...

Yadda Shugaba Xi Jinping Yake Ba Da Jagoranci Ga Aikin Kula Da Lardin Qinghai

Yadda Shugaba Xi Jinping Yake Ba Da Jagoranci Ga Aikin Kula Da Lardin Qinghai

by CRI Hausa
3 hours ago
0

Daga CRI Hausa A jiya Lahadi, shugaba Xi Jinping na...

Shaidu Sun Karyata Jita-Jitar Da Ake Yadawa Game Da Alluran Riga-Kafin Cutar COVID-19 Na Kasar Sin

Shaidu Sun Karyata Jita-Jitar Da Ake Yadawa Game Da Alluran Riga-Kafin Cutar COVID-19 Na Kasar Sin

by CRI Hausa
3 hours ago
0

Daga CRI Hausa Jiya Lahadi, mamban majalisar gudanarwa kana ministan...

Next Post
Firimiya

Cin Kwallaye Da Yawa Yana Da Mutukar Amfani –Solkjaer

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version