Daga Abubakar Abdullahi, Lafia
Ƙoƙarin kamfanin man fetur na nijeriya NNPC kan samun man fetur a yankin arewacin nijeriya ya koma tafkin ƙarƙashin ƙasa da ya ratsa jihohin Binuwai da Nasarawa.
Babban manajan daraktan kamfanin NNPC, Maikanti Baru ne ya sanar da fara binciken man fetur ɗin a lokacin da ya kai ziyara ga gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Al-Makura a Lafia.
A cewar babban manajan daraktan, ziyarar da ya kawo jihar ta yi daidai da umurnin da shugaban ƙasa ya bai wa kamfanin kan ya koma gudanar da ayyukan haƙo man fetur a wasu daga cikin tafkunan ƙarƙashin ƙasa dake faɗin ƙasar nan, ciki har da na Chadi da na yankin Binuwai da ya shafi jihar Nasarawa.
Ya ce, umurni da shugaban ƙasa ya bayar na binciken man fetur ya biyo bayan bukatar gaggawa da ake da shi na kara adadin yawan man fetur da ƙasa ke samu da inganta kudaden shiga da kuma samar da damar ayyukan yi ga ‘yan nijeriya.
Maikanti Baru ya fadawa gwamna mai cewa tawagar kamfanin man ƙasa NNPC ta kasance a jihar Nasarawa ne domin wayar wa gwamnati da jama’an jihar kai kan irin ayyuka da kamfanin zai gudanar a jihar.
In ji ta bakin sa “kan wannan aiki da zai gudana a jihar ina mai matukar farin da na kasance tare da manyan masu ruwa da tsaki a bangaren man fetur da zummar fara haƙar mai a jihar Nasarawa dake zama wani bangare na tafkin Binuwai mai dauke da man fetur a ƙarƙashin ƙasa”.
Ya tabbattar cewa kamfanin na NNPC zai yi dukan mai yuwa wajen gudanar da aikin sa cikin kwanciyar hankali a tsakanin mutane da kuma kula da hakin muhali.
Tuni dai babban manajan kamfanin NNPC ya sanar cewa sashin haƙar mai na kamfanin tare da hadin gwiwar bangaren tattara bayanai na kamfanin sun fara aikin tattara bayanai a tafkin na Binuwai inda suka fara a yankin Keana na jihar Nasarawa.
cewarsa “ina da amanar cewa nasarar da za a samu na wannan aikin bincike zai kai ga fara haƙar man fetur a yankin wanda muna fatan zai saka jihar Nasarawa cikin jerin jihohi masu samar da mai ga ƙasa”, Maikanti Baru ya jaddada.
Kan batun adadin man fetur da ake baiwa jihar Nasarawa babban manajan kamfanin man fetur din ya tabbattar wa mazauna jihar cewa samar da mai zai inganta da zarrar an kammala gyarar bututun da ke tura mai zuwa daffo na Makurdi wanda ya ke samar da mai ga jihohin Nasarawa da Binuwai.
Tun da farko a jawabin sa gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura wanda ya bayyana jin daɗin sa da fara aikin binciken man a jihar ya tabbattar wa babban manajan kamfanin da goyon bayan jama’ar jihar kan aikin.
Haka nan yayi yabawa ta mussamman ga babban mana kamfanin kan dorewa da samar da kuma rarraba man fetur a faɗin ƙasan nan.
In ji ta bakin gwamnan “tun da aka nada ka a mukamin babban manajan darakta na kamfanin NNPC, ba zan taɓa tuna ko a yaushe ne aka samu matsalar ƙarancin man fetur a ƙasan nan ba. Haka nan kowa ya san ka wajen tsayar da gaskiya da adalci wasu abubuwan da suke da muhimmanci ga kamfanin man ƙasa na NNPC”.
Gwamna Al-Makura yayi alƙawarin ba da umurni ga ma’aikatun filaye da na gidaje da sufuri kan su yi aiki tare da ta tawagar NNPC wajen tabbattar da nasarar haƙo mai a yankin da ake gudanar da binciken.