A kwanakin baya, an fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani a garin Gushi dake lardin Henan, inda sojojin ’yantar da jama’ar kasar Sin wato PLA sun jera buhunan rairayi don tare ruwa daga malala. Sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin dake lardin Henan Wang Guosheng ya je wurin da sojojin suke gudanar da wannan aiki tare da bayyana godiya da wannan namijin kokarin yaki da ambaliya. Ya ce, sojojin za su amsa kiran da ake yi musu a duk lokacin da irin wannan bukatar taso. Hankalin jama’a yana kwanciya a yayin da sojojin PLA suke tare da su. Don me jama’a ke bayyana hakan?
Bayan da aka kafa sojojin ’yantar da jama’ar kasar Sin a ranar 1 ga watan Agusta na shekarar 1927, sojojin sun tinkari wahalhalu da dama, da inganta karfinsu, da kara yawan membobinsu, don yin kokarin kasancewa sojoji dake kunshe da dakaru nau’o’i daban daban, kana sun yi ta iya kokarin samun ci gaba, don zama sojoji masu karfi dake da alamar musamman ta kasar Sin, da kasancewa tamkar babbar ganuwa mai karfi wajen kiyaye zaman lafiya da bunkasuwa a kasar Sin.
A ranar 15 ga watan Yuni na shekarar 1949, kwamitin aikin soja na sojojin jama’ar kasar Sin ya bada umurnin cewa, an maida kalmomin Sin “Ba Yi” wato daya ga watan Agusta da Hausa, a matsayin alamar tutar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin. Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, an maida wannan rana, wato daya ga watan Agusta a matsayin ranar murnar kafuwar sojojin ’yantar da jama’ar kasar Sin.
A cikin shekaru casa’in da uku da suka gabata, sojojin ’yantar da jama’ar kasar Sin, sun yi kokarin tabbatar da tsaron kasar da na jama’a. A yayin yake-yake, sun sadaukar da rai don ceton kasar da jama’ar kasar. A yayin zaman lafiya, sun yi kokarin tabbatar da zaman rayuwa na jama’ar kasar yadda ya kamata.
Alal misalai, a shekarar 1998, an samu babbar ambaliyar ruwa a kasar Sin, sojojin ’yantar da jama’ar kasar Sin sun tafi zuwa wurare masu fama da bala’in don ceton jama’a. A shekarar 2003, cutar SARS ta abku ta kuma yadu a kasar Sin, sojojin ne suka tafi zuwa wurare daban daban na kasar don taimakawa jama’ar kasar wajen tinkarar cutar.
A shekarar 2008, babbar girgizar kasa ta faru a Wenchuan na lardin Sichuan na kasar Sin, sojojin sun je Wenchuan ba tare da bata lokaci ba, don ceton mutanen dake wurin. Kuma a shekarar da muke ciki yanzu wato shekarar 2020, cutar COVID-19 ta bazu a kasar Sin, har ma da sauran sassan duniya baki daya, sojojin a nan ma sun tura tawagoginsu don bada jinya, da ceto ga mutanen da suka kamu da cutar cikin hanzari.
Kana a kwanakin baya, an samu ambaliyar ruwa mai tsanani a kudancin kasar Sin, sojojin ’yantar da jama’ar kasar Sin sun kuma tafi yankunan nan da nan, don taimakawa mutane masu fama da bala’in. Sun sadaukar da rai don tabbatar da tsaron rayukan jama’a da na dukiyoyinsu.
Lokacin da suka ji matukar gajiya ko barci, suna kwanciya kan kasa don yin barci, sannan nan da nan su sake koma aikin ceton jama’a ba tare da bata lokaci ba. Mai yiwuwa ne sojojin za su ji rauni ko rasa rayukansu, amma ba sa jin tsoro ko kadan, don haka ya kamata a nuna musu girmamawa.
Ranar murnar kafuwar sojojin ’yantar da jama’ar kasar Sin wato ranar 1 ga watan Agusta na zuwa, don haka ya kamata mu girmama sojojin dake kokarin ceton jama’a masu fama da ambaliyar ruwa a kudancin kasar Sin, domin sun zama tamkar wata babbar ganuwa mai karfi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron jama’ar kasar. (Zainab)