Mukhtar Anwar" />

Hannunka-Mai-Sanda: Kagaggen Labari: Ramin Karya…!

Mukhtar Anwar 0803 667 9084

Majalisar Kabiru Kartabiya Maishayi da ke unguwar Kaigama, za a ga cewa majalisa ce da ta kunshi jama’a iri daban-daban da ke dandazon zuwa shan shayi a kullum, musamman daga bayan Sallar Isha’i har zuwa tsalawar dare.

Zafafan muhawurori da kan tashi daga lokaci zuwa lokaci a majalisar maishayin, sai a zaci akwai yi wuwar ma a yi sare-sare, amma fa kan da yawa sai lamarin ya juye zuwa dareraku. Sai dai, samun saukin rashin ta da fitina a majalisar, wasu na danganta hakan da kwarewa ta bariki da Kabiru Kartabiya ke da. Ba ya ga yawon ta-zubar da ya yi a mabanbantan garuruwa da sunan neman dari da kwabo, irin su garin Fatakwal da Ikko da Inugu da makamantansu, mutumin, tsohon dan sinima ne, don ko a can ne ma yai katarin samun lakanin sunan na Kartabiya.

Ko shakka babu, Sani Feshi, na daga manya-manyan ‘yan majalisar dake haddasa rudu da yawan tankiya a wurin shan shayin na Kartabiya. Halayya ta biyu da Sanin ke da ita shi ne, a yi kwance-kwance a girba karya, kuma a yi funfurun bayan girba tan, a zuwan gaskiya ce a ka fadi. Har’ila yau, daga halayyar dake janyowa Sani bakin-jini ita ce, komai ya ji wani na fadi, sai ko ya zakalkale ya nuna ya ma fi mutum sanin abin.

Watarana majalisar ta Kartabiya ta yi cikar kwari, sai ya zamana mutane sun karkasu zuwa gungu-gungu suna ta fadin albarkacin bakinsu. Da alama wasu mutum biyu dake zaune bisa bencin dake hagun maishayi makaranta Littafin Allah ne, duba da jin irin kalaman da suke kai-kawo a kansu.

Wadancan mutane biyu, na tattaunawa ne game da banbance-banbancen dake a tsakanin Babbaku Da Farfaru. Sai tsulum Sani Feshi ya tsoma musu baki, har ma wai da kokarin cin-gyaran su. Inda yake cewa da su;

“Ku tsaya ku kwantar da kai na kare ku da abinda ba ku sani ba. Sabanin abinda na ji ku ke fassara kalmomin Babbaku da Farfaru. Idan an ce babbaku, a na nufin, duk wani Mai-damara, kama daga kan ‘yan sanda zuwa sojoji. farfaru kuwa, a na nufin, duk wani farar hula, muddin shi ba ciyaman ba ne ko dan majalisa ko gwamna ko shugaban kasa. sannan…”

Ai ko wadannan mutane biyu ba su bar Feshi ya sauka ba, suka kalubalence shi kalubale mai zafi. Sai ya zamana ma suna kokwantan cikar imanin Sanin. Sun nemi sanin, shin wai ainahinsa Musulmi ne tun azal koko Tubabba ne? Sun cigaba da bugun kirjin cewa, su fa iyayensu sai da suka taka matsayin Gangaran a farfajiyar Tilawar Al-Kur’ni. Saboda haka, babu wani fi’ili da za a zo musu da shi game da batun Al-kur’anin su saurari mutum.

Saboda tsaurin-ido irin na Sani Feshi, sai yake fada musu cewa, shi fa Kakansa a fagen sanin Alkur’ani tuni ya kere matsayin Gangaran shekaru arba’in da suka shude, yanzu haka shi Hantsilan ne. Kuma kowa ya sani a batu na Alkur’ani, daga kan gidanmu sai dai a shafa-fatiha. Tun da tazarar dake tsakanin Gangaran da Hantsilan tamkar tazarar dake tsakanin Sarki ne da Mai-unguwa. A karshe dai wadancan mutane biyu, sai tashi sukai suka tafi su na kwafa, amma Sani ko a-jikinsa.

Cikin dai masu shan shayin, sai wani ke kawo maganar ‘yan Matan Chibok tamanin (80) da aka saka. Nan ma dai caraf Sani Feshi ya fara rawar-kafar ya fi kowa sanin hakikanin wadancan ‘yan mata na Chibok, inda yake cewa wai akwai wata yarinya cikin matan da ake kira da Diyana John, wadda kusan Watanni shida da suka shude yake tattaunawa da ita a shafin zumunta na Fesbuk.

Kiri da muzu, Sani ya cigaba da cewa, wai waccan yarinya Diyana ta rike wuta cewa lalle-lalle sai ya aure ta a duk sa’ad da Allah ya sa suka tsira daga hannun wadancan ‘yan-tada-kayar bayan. Feshi ya cigaba da fadin cewa, ai yanzu haka ma waccan yarinya Diyana na daga cikin wadancan tamanin da aka sako.

Mutumin da ya kawo waccan magana ta ‘yan matan na Chibok, ko da ya ji Sani Feshi yai wancan taren-gaba, sai ya zamana ko ma tankawa bai yi ba, a karshe ma dai kade rigarsa yai ya bar wajen ba tare da ya kammala shan shayin nasa ba.

Ashe dai ba kullum ne ake kwana bisa gado ba, a bangaren hagun mai shayin, akwai wani mutum gajere mai kaurin gemanya dattijo, a na cikin hirar ne, sai ya kawo maganar mahaifiyar kwamishinan ‘yan sanda da aka yi garkuwa da ita tsawon kwanaki biyar da suka gabata.

Jin waccan magana ta mahaifiyar kwamishina, sai Sani Feshi ya gabza rantsuwa ya ce ya san yadda za a yi a kwato ta daga hannun wadancan ‘yan Garkuwa. Ya kara da cewa, saboda zaluncin mahukunta, bai faye son shiga irin wannan lamari ba.

Bayan Sani ya sauka ne, sai wannan mutumi ya ce da shi;

“Kai ko bawan Allah, yaya za a yi ka iya fidda babar kwamishinan?”.

Sani yai murmushi, kana ya ce;

“Kai malam, ni fa Allah ne ya yi ba zan shiga cikin irin wannan harka ta garkuwa da mutane ba. Kaf jagororinsu dake a Kudanci da Arewacin wannan Kasa waye wanda za a ce ban san shi ya san ni ba? Yanzu haka idan na ga dama, waya kawai zan yi a sake ta cikin ‘yan mintina kalilan”

Sai mutumin ya ce;

“Kai ko bawan Allah ba ka son kudi ne?”

Sani Feshi ya amsa da;

“Wannan ai maganar banza ce! Kamar ni a ce ba ya son kudi. Duk wajen nan, waye ya fi ni sanin muhimmancin kudin?…”

Nan da nan mutumin ya bai wa Feshi hakuri. Sai yake nuna cewa abinda ya sa ya fadi haka shi ne, saboda ya ga hukumar ‘yan sanda ta kasa ta sanya ladan naira miliyan biyar ne ga duk wanda ya ba da gudunmuwa aka kame wadancan da suka yi garkuwa da babar kwamishinan, amma sai gashi Sanin ya sani, amma bai damu da yai habzi da wadancan kudade ba.

Feshi ya amsa da cewa;

“Idan na nuna aka kama su, ai na san cikin ‘yan sandan sai wani ya tsegunta musu, daga karshe su zo su kashe ni a banza ba tare da na mori wancan lada da aka ba ni ba. Wannan ne dalilin da ya sa ba zan tona musu asiri ba”

A gaskiyar magana, Sani Feshi bai san wadancan ‘yan garkuwa ba. Kawai son iyawarsa ne ya sanya shi gilla karyar sanin na su. Tabbas! Da ya san sun, zai ko nuna su, kasantuwar daka-da-waje bai da tsabar kudi ko kadarar da za ta kai darajar naira dubu hamsin, sai kafirar karya.

Bisa kaddara, ashe dai wannan mutumi dan sandan farin kaya ne. Bayan ya kammala bugun cikin Sani ya gama jin komai, sai yai kamar zai je yai bawali, ashe waya ya buga zuwa ga Hedikwatar ‘yan sanda ta jiha, yana mai labarta musu cewa ya sami wata majiya mai tushe game da yadda za a kai ga tseratar da mahaifiyar kwamishina. Ya wassafa musu har yadda za su zo nan majalisar mai shayi su same shi.

Ko da mutumin ya dawo, sai ya ga Sani na neman tafiya. Sai ya tambaye shi, shin shayin nawa ne ya sha? Ya fada masa. Sai ya zare kudin ya biya. Sannan mutumin ya nemi da a fashewa Sani kwayaye biyar nan take. Sani yai wasu ‘yan zille-zille kamar ba zai ci wainar ba, a karshe dai ya share gindi ya zauna yana wani muzuran iska. Daga nan fa, sai Feshi ya hakimce ya dinga korowa majalisa ruwayoyin karya iri-iri.

Idan wani cikin ‘yan majalisa na neman karyata Sani, sai a ga wannan mutumi na ta wani faman kakkarewa. Saboda haka, sai Sani ya saki jikinsa yai ta harbo su. Shi ko wannan mutumi na lallabar Sani ne gudun kada a fusata shi ya ware gabanin zuwan wadancan jami’an tsaro da ya kira.

InnalillaHi!!!…Gabanin kammala toyawa Sani wainarsa, sai ga motocin ‘yan sandan kwantar da tarzoma kimanin goma sun afko majalisar Kabiru Kartabiya cikin matsanancin sauri tare da cin wani mummunan birki. Nan fa kura ta turnike waje, cikin salon iya aiki, kafin jama’ar wajen su yi wani kyakkyawan yunkuri tuni ‘yan sandan sun wa wurin gabadaya kawanya.

Da farko wasu cikin ‘yan majalisar sun tasamma tserewa, amma ganin zobe da jami’an tsaron suka yi wa majalisar cikin kiftawar ido, sai kowa jiki yai lakwas tare da fawwala lamari zuwa ga Allah bisa tilas.

Yayin da jagoran ‘yan sandan ya fito daga mota, sai aka ga ya zo cikin zafin nama ya kame tare da sarawa wannan mutumi mai yalwar gemu dake zaune dab da Sani mai shirin cin wainar kwai.

Wani abu mai kama da almara shi ne, sai wannan mutumi ya cewa mai shayi ya kammala toya wainar Sanin cikin nutsuwa suna jiran sa. Bayan mutumin yai wani irin kifce da idanunsa biyu, sai wadannan ‘yan sanda suka saitawa sauran jama’a hanya. Wasu biyar cikinsu suka zo gami da yin banga-banga a sasannin Sani Feshi suna muzurai, sannan ga muggan makamai rike a hannu.

Bayan kare toya wainar, wannan mutumi ya zare kudi cas ya biya. Sai ya nemi Sani Feshi da su je cikin mota, za a yi masa wasu ‘yan tambayoyi ne a can Hedikwata amma yanzu zai dawo. Nan fa Sani ya barke da kuka, fadi yake;

“Wallahi yallabai ba wani cikakken sani na yi musu ba face sanin shanu da azal…”

Sani na cikin waccan marairaita ne wani murdadden dan sanda gajere kuru yai wuf ya caskali wuyansa ta baya. Kan ka ce kwabo, tuni sanin ya baje a kas yana wani irin kakari. Sauran kuratan ‘yan sandan suka zaburo suka yayime shi suka watsa cikin mota.

A takaice dai aka tafi da Sarkin Karya. Kabiru mai shayi kuwa sai da yai Watanni uku bai dora sanwar shayin ba saboda tsananin firgici.

Mutari Anwar

 

Exit mobile version