Connect with us

KIWON LAFIYA

Hanyoyi Biyar Na Kiyaye Fata Daga Bushewa

Published

on

Rana mai zafi kokuma dan dumu- dumi ko ma zafi da dare, busasshe kuma iska mai tafowa da kura, wadannan da ma wasu suna nuna alama cewar an shiga lokacin bazara.
A wasu jihohi na Nijeriya musamman ma, a Arewa rana tana iya kasancewa mai zafi kamar zata kona fatar jikin mutum, yayin da kuma wasu jihohin tare da Lagos ita ranar tana da zafi sosai wadda zata iya sa mutum bai ji dadin rayuwarsa ba.
Yana da kyau a lura cewar da akwai maganar cutarwa da saboda yadda za, a fuskanci rana, abin da yana iya sa wa , a kamu da cutar sankara ta fata.wadanda wasu alamomi ne akan fatar jiki, da akwai kuma lokacin da za, a iya samun wata kala a fata, a dalilin kananan hanyoyin da jini ke bi, masu kama da zare.
Kamar yadda WebMD, wanda wani kamfani ne na Amurka ya bada labarin da ya danganci lafiyar Dan Adam da kuma walwalarshi, idan mutum yana fuskantar rana, hakan yana kawo wani abu akan fata da kuma fuska,wannan kuma yana bada cikakkiyar dama yadda ita fatar zata nuna tsufa.
Ya kara jaddada ita rana tana da wani nau’I na haske wanda ake kiran shi ultrabiolet yana samar da matsala a fatar jikin mutum abinda ake kira elastin, wanda wani sinadari ne a jikin mutum mai taimakawa wajen yadda abubuwa suke komawa wuraren da suka dace dasu, yana kuma tabbatar da hakan ya faru. Hakanan fata tana tana yagewa ko kuma ta hadu da wasu, abinda kan dauki dogon lokaci kafin a samu warkewa abubuwa su koma kamar yadda suke tun farko. Ko da yake matsalar da aka samu ta rana abin ba zai iya nunawa ba , idan mai jikin yana cikin kuruciyarsa, to a gaba zai iya bayyana.
Amma duk da yake da akwai matsalar rana a fatar jikin mutum, shi ma al’amarin zafi an gano yana taimakawa wajen kasancewa sandiyar shiga wani yanayin da mutum zai rasa ruwa, a jikin shi. Wannan kuma yana taimakawa wajen yaduwar ciwon bakon dauro da kuma gajiya.
Ga yadda jama’a zasu yi kokkarin taimakawa kansu saboda yaddazafi yake da tasiri, wadannan sune hanyoyin da za, abi domin a kasance da rayuwa cikin lafiya
A Sha Ruwa Da Yawa Don Kasancewa Yadda Ya kamata
Idan mutane suka kasance cikin zafin rana, wannan ana nufin za suyi zufa hakan kuma zai sa su rasa ruwa, ko dai sun fahimci irin halin da suke ciki, ko kuma basu sani ba. Shi yasa kwararru a bangaren kiwon lafiya suka ba mutane shawarar da su sha isasshen ruwa, kamar yadda wani rahoto da aka yi ma suna da Keck Medicine of USA wanda kuma ka buga akan Forbes.An bayyana lamun dake nuna ruwan jikin mutum ya fara karewa, wadannan alamu sun hada da fitsari mai ruwan dorawa, ciwon kai, tattaurewar fatar jikin mutum, gajiya, ba fitsari akai –akai, ciwon kai tsanani, rashin zuwan ban daki.
Shahararren masani akan fatar jikin Dan Adam Farfesa Frances Ajose ta bayyana cewar idan ana shan ruwa da yawa, hakan zai taimakawajen tabbatar da fata tana isasshen ruwa da zai maye wanda aka rasa, a sanadiyar zufa wadda a dalilin haka, akwai abubuwan da ba,a bukatarsu a jikin mutum. Bugu da kari ta kayyade yawan ruwan da mutum zai iya sha shi ne lita hudu, a kasa kamar Nijeriya. Wannan ya nuna ke nan ledar ruwa guda takwas mutum ya kamata ya sha ko wace rana.
Duk da haka cikin wannan lokaci mai zafi ana ba mutane shawarar su sha ruwan daya wuce hakan, ko kuma duk inda suka nufa ya kasance yana tare da ko na leda ko kuma na kwalba.Wannan zai kasance kamar yana tuna ma kan shi, masana sun ce mutum ba zai yi kuskure baakan maganar tafiya da ruwa,saboda ba wai yana daidaiata yanayin jikin mutum kadai bane, yana taimakawa wajen sa fata tazama cikin taushi, ga kuma taimakawa koda wajen aiki yadda ya kamata. Ga kuma taimakawa duk wuraren da abubuwa suka hadu, alal misali ba wanda ke zaune a Lagos wanda zai kasa shan ruwa lita hudu ko wace rana. Wanda kuma ke shan ruwa wanda bai kai lita hudu ba wannan bai dace da jikin Dan Adam ba, a wannan yanayi mai zafi kamar wannan.
Mutum Ya San Irin Kayan Da Zai Sa
Koda yake an ba mutane shawarar su yi duk yadda zasu iya su rika kare jikinsu da yadda zai samu haduwa da rana, a wannan yanayi. Duk da haka daakwai wsu dalilai da zasu sa mutane su shiga rana, ko dai ta harkar aiki , ko kuma a shiga saboda abin ya zama dole ne. Bincike ya nuna rana tana cikin tsananin zafinta tsakanin karfe goma na Safe zuwa hudu na Yamma. Shi yasa a irin wannan yanayi masana sun bada shawarar, ya dace mutane su kayayyaki masu kare su kamar riga shat mai dogon hannu, da wando da kuma hula mai fadidon ta kare fuska , hammata, da kunne daga rana. Wannan zai taimaka wajen sa fatar jikinsu ta kasance ko wane lokaci abar sha’awasaboda bata bushe ba. Yana kuma da kyau mutane su kasance cikin inuwa, musammman lokacinda ranar take cikin tsakiyar zafinta, wannan kuma zai sa a kauce ma shiga rana, abinda zai iya sawa dole sai zufa ta fita an rasa ruwan jikin mutum.
Sa Tabarau Mai Kare Hasken Rana
Wata hanya ta mutum zai kare idanun shi ba tare da wani abu ya same su ba, cikin wannan ya-nayi na zafi shi ne, ya rike sa Tabarau wanda zai kare idanun shi , lokacin da zai shiga ra-na.Amma kuma wasu mutane suna jin kunyar haka, saboda basu amfanin wannan ba. Ko kuma kawai suna jin kunya ne, ya kamata mutane su sani cewar akwai wasu sinadaren da suke fitowa daga rana, suna iya lalata wasu sassa na idanu, sannu sannu kuma hakan na iya shafar gani da idon mutumin watarana.
Advertisement

labarai