Hanyoyi Zama Lafiya Tsakanin Mata Da Dangin Mijinta

Wasu mata da yawa ba su sha da dadi a hannun dangin miji ba. Kafin mu yi nisa ya kamata mu san su wanene dangin miji. Galibi dai a kasar Hausa idan aka ce dangin miji, ana nufin uwar miji, uban mijin, yayyen miji, kannen miji da sauransu. Wadanda suke da alaka ta jini ga miji.

Idan aka yi rashin sa’ar samun sabani a tsakanin dangin miji da matar gida, to za ka ga duk abin da ta yi musu don farantawa ba su gani. Idan suka ga fari a gare ta za su ce baki, idan baki ne za su ce ja. Wannan kiyayyar za ta kai ga wata rana uwar miji ko ‘yan uwansa su fara zagin ta har ma da duka. Idan bala’i ya yi yawa, wasu su kan kai da cewa ko ya sake ta ko kuma a tsine masa ko kuma a juya masa baya. Idan ya yi  banza da su don kaunar da ke tsakaninsa da mai dakinsa ko dan kyautatawa da ta ke masa sai a ce ta mallake shi, nan ne wasu ‘yan’uwa kan shiga su fita don ganin sun cece shi daga hannun muguwar kamar yadda wasu ke fada.

A wasu lokuta kuma idan matar ta daure da talaucinshi, sai a kafa ma ta cewa lalle ita mai farar kafa ce, in kuma ya amince da ita tana adana masa dukiyarsa to nan sai a ce ta shiga malamai da bokaye ta mallake shi. Har ila yau Idan shi mijin mutun ne wanda ba shi da sha’awar kara aure, to nan ma ga dangin miji da ba su kaunar ta laifinta ne. In kuma yana da mata biyu ko fiye da haka wasu dangin miji sai su zabi daya su daura ma ta karar tsana walau mowa ce a gurin miji ko bora ce, duk dai wacce rashin sa’a ya hau kanta to za ta ji ba dadi. Abin mamaki sau tari za ka ga ba dangin miji mata kawai ba hadda wasu iyaye mazaje ko ‘yan’uwan miji maza su ma sun tsaya tsakaninsu da Allah ana zuba kishi da matan ‘yan’uwa ko ‘ya’ya.

Shawara a nan ita ce dangin miji su ji tsoron Allah su tuna suna da baya. Babu wanda ya ke son ya aurar da ‘yarsa sannan ya ga an hana ta sakewa a gidan aure ana mata wulakanci, na safe daban na rana daban. To abin da ba ka son a yi maka kar ka yi wa wani. Bayan haka, mu kasance masu tunani cewa shi fa Allah ba azzalumin kowa ba ne sai dai wanda ya zalunci kansa da kansa. Kuma shi mai ramawa wanda aka cuta ne a nan duniya da kuma lahira. Kuma ai ina ganin cewa ‘yar wata aka dauko aka baiwa danku amma saboda haka zai yi kyau ku taimaka masa wajen ganin ya sauke amanar nan da aka bashi tsakaninsa da Allah maimakon ganin kun tursasa shi ya ci wannan amanar da aka damka masa.

Allah ne ya ce a yi aure kuma sunna ne na Manzo Allah (SAW), to idan burinku a muzguna ma ta dalilin sunna to ai da Allah kenan mutun ya ke yi, don kuwa ba don umurninsa ba wata za ta iya zama a gidan mahaifanta har tsawon rayuwarta ba kuma tare da ta rasa komai ba.

An san da cewa akwai wasu matan ‘ya’ya ko dan uwa masu munanan halaye na ba gaira ba dalili, bukatunsu kawai su ma su muzguna maku ‘yan’uwan miji. Idan aka yi rashin dace Allah ya hada ku da hatsabibiyar matar dan’uwa, a shawara ta babban abin da za ku fi mayar da hankali a kai domin magance matsalar shi ne ku dukufa ga yin addu’a, Allah sai ya kawo maku mafita cikin ruwan sanyi ba tare da tada jijiyoyin wuya da kumfar baki ba. Shawara gare ta da yin banza da ita a yayin da ta yi kunnen uwar shegu shi ya fi don kuwa babu dadewa hakurinku zai biya, ko ta yi nadamar halinta ko watarana ku ganta a waje. Kamar yadda masu zantukan hikima na Hausa ke fadi, aure kam rai yake da shi idan lokacin rabuwa ya zo ko kuna so ko kuna ki za a rabu, ba sai kun yi sanadi ba, hakazalika in Allah ya so ganin su tare babu yadda za su raba ko shi mijin kam ba shi da ikon yanke zama sai hukuncin mahalicci. Babban abin yi kawain a nan hakuri shi ne maganin komai da komai. Idan mutun bai ji bari ba ai dole zai ji hoho, saboda haka ni ban ga dalililn da zai sa ‘yan’uwan miji su ce sun ara sun yafa a game da abin da ya shafi matsalar ma’aurata ba musamman dangane da abin da ya kebanta a tsakanin miji da mata.

Uwa ke ki ka haifi dan ki duk addu’ar da ki ka yi a kansa karbabbiya ce in sha Allah. Shawara gare ki, ki fuskanci Ubangijin ki da kukarki game da abin da ki ke ganin cutarwa a zamantakewar dan ki da matarsa. Shi Allah zai kwato shi in kin kuma jahilci abin ne Allah zai nuna miki gaskiya baro-baro ki fahimce ta. Amma in kin ce kina da karfi kan al’amarin sai ya kasance an bata goma daya ba ta gyaru ba, a sanadiyyar hakan ma dan naki da ake rigima a kansa sai ya shiga damuwa, duk abin duniya ya dame shi ya rasa inda zai sa kansa. Da zaran abin ya yi kamari  sai auren ya lalace, ita kuma matar ta tafi ta auro wani ta bar miki abin da ki ka lalata da fushin ki ko bakin ki ta hanyar yin Allah wadai ko tir ko kuma la’anta.

 

Exit mobile version