Yusuf Shuaibu" />

Hanyoyin Da Mace Za Ta Bi Don Samun Karbu Wa Ga Mijinta

Amarya

Ita dai mu’amala wata aba ce da ake so mutum ya kyautata ta, tsakanin sa da kowa, har wanda ba musulmi ba. Ya kamata mata su lura da wadannan halaye kamar haka:Ita dai mu’amala wata aba ce da ake so mutum ya kyautata ta, tsakanin sa da kowa, har wanda ba musulmi

Biyayya
Dole ne a matsayin ki na matar aure ki kasance mai biyayya a cikin duk abin da mijinki ya ce ki yi, in har bai sabawa abin da Allah ya ke so ba. Ki ji a ranki ke fa bautar Allah kika zo, kuma ki sa a ranki cewa aure hanya ce da za ki nemi Aljanna da ita.

Gaskiya:
Fadin gaskiya a kowanne lokaci yana da muhimmanci, kuma zai jawo miki kauna da soyayyar mai gidanki. Haka kuma zai jawo miki yardar Allah. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai ita gaskiya tana shiryar wa zuwa ga biyayya ga Allah, ita kuma biyayyar Allah tana shiryar wa zuwa Aljanna. Ita kuma karya tana shiryarwa zuwa fajirci, shi kuma farirci yana shiryar wa zuwa wuta”.
Ashe dai fadin gaskiya zai iya jawo yardar Allah, domin kuwa in har an shiga Aljanna ai babu sauran fushin Allah kuma; kamar yadda karya za ta iya dawo fushin Allah.

Rikon Amana:
Ki kasance mai rikon amanar mijinki. Ki kiyaye kanki daga duk wani namiji wanda zai iya sa mijinki ya zarge ki a kansa. Ki yanke alaka da duk wanda mijinki baya son ki yi alaka da shi, kuma kar ki kulla wata alaka da duk wanda mijinki baya so ki yi alaka da shi. Ki kula da dukiyarsa, abin da ya shafi kayan amfani na gida ko kaddararsa ko kuma kudinsa. Ina jin labarin ana cewa wasu mata har duba aljihun mazajensu suke yi ko za su samu kudi su dauka. ‘Yar uwata kar ki yi haka domin rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya.

Kunya
Dole ne mace ta kasance mai kunya. Dole ne duk abin da zai sa mijin ta ya ji kunya a gaban jama’a ta kiyaye shi.

Hakuri
‘Yar uwa ta ka da ki yi tunanin rabin ranki ba zai bata miki rai ba. Wasu matan idonsu yana rufewa, wai don ita kadai ce ‘ya mace a gidansu ko ita ce ‘yar auta ko ita kadai aka haifa a gidansu, don haka yanda ake shagwabata a gidansu haka za a yi mata a gidan miji. Eh! Hakan zai iya faruwa, in kin yi sa’ar mijin da yake da fahimta. Za ki iya samun wanda zai baki gatan ma da ya fi wanda kika samu a gidanku, amma fa ki sa a ranki wata rana dole a samu matsala. To duk lokacin da matsalar nan ta faru ki yi hakuri ki manta da zancen. Wannan shi zai kara miki zaman lafiya a gidan mijinki.

Iya Magana
Wasu matan ba su iya magana ba. Suna ganin sa’annin su ne ko da kuwa mijin ya fi ta da shekara goma. Hajiya ki fahimci cewa shi fa namiji kansa a dan kunbure yake. Ko da kuwa kin girme shi da shekaru, shi yana ganin shi ne a gaba, domin shi ne mai gida kuma a ko da wani lokaci yana da ikon da zai yi abin da ya ga dama a gidansa. Sai ka ga miji yana bawa mace labarin wani abu mai muhimmanci, sai tace “tsaya, ka ce Allah” wannan zai sa ya ga kin raina masa hankali har ya fara tsanar ki.

Sauraro Mai Kyau
Wasu matan idon miji yana yi musu zance sai ka ji sun ci gaba da harkokin gabansu. Idon ya yi magana sai ta ce “to ba kunne ne yake ji ba? Ai ina ji ka fada mana”. Wasu kuma miji yana yi musu magana sai ka ji suna cewa “kai ni ka dame ni”. To gaskiya hakan zai iya jawo miki matsala. Ba lallai sai ya sake ki ba, zai iya canja yanayin mu’amalarsa da ke kuma hakan zai hana ki kwanciyar hankali a gidan miji.

Godiya
Godiya a duk lokacin da miji ya yi miki wani abu komai kankantar sa yana da muhimmanci kuma yana kara soyayya. Ki tuna fa Allah ma yana so a yi masa godiya kamar yadda ya ce “tabbas in kuka gode min zan kara muku, (amma) kuma in kuka kafirce min, to azaba ta mai tsanani ce”.
Hakazalika, gode wa miji zai sa ya kara miki wani abun ma da baki yi tunani ba. In ya yi miki abu kika gode, sai ya samu kwarin gwiwar yi miki wani abu, amma in baki gode ba ko kika raina abin da ya kawo miki, to nan gaba ko ya yi tunanin yi miki wata kyauta sai ya fasa saboda yana tunanin kar ya kawo miki, ki watsa matsa kasa a ido.

Neman Shawarar Mijin
Neman shawarar mai gida abu ne mai kyau. Hausawa sun ce “ana yi da kai ya fi a ce ba a yi da kai”. Neman shawarar mai gidanki idon za ki yi wani abu zai saka shi ya ji ashe kin dauke shi da muhimmanci kuma zai yi kokarin ya baki shawara mai kyau dai-dai gwargwado.

Rashin Yawan Kuka
Wasu matan suna da yawan mita. Duk abin da aka yi mata sai ta yi magana. Wannan ya hada da in mai gidan ne ya yi mata laifi ko wani ne daga danginsa. Hakan yana da illa, domin yana daya daga cikin dalilan da suka sa mata suka fi yawa a wuta a lahira, saboda hadisi ya tabbata cewa wata ranar sallar idi Manzon Allah (SAW) ya yi sallar idi sai ya yi huduba bayan sallar, sannan ya wuce ya yi wa mata wa’azi, a ciki yake cewa “ku yawaita sadaka, domin ku ne mafi yawan makamashin wuta”. Sai wata mata ta tashi tsaye ta ce saboda me, ya Manzon Allah? Sai ya ce: “kun kasance kuna da yawan kai kara, kuma butulce wa abokin zama (wato miji)”.
Ashe kenan wadannan abubuan guda biyu za su iya kai wa mace wuta. Don haka ‘yar uwa, ina baki shawara da ki zama mai godiya ga mijinki kuma ki daina yawan magana a kan kowanne karamin abu da bai kai ya kawo ba.

Taimakon Sa In Allah Ya Baki Dukiya
Wani lokaci za ka ga mace ta fi mijinta karfin samu. To a wannan lokacin ya kamata ta rinka rage masa wasu abubuwan na gida. Hajiya, za ki iya yi wa mai gida dinki bai sani ba, sai dai kawai ya ga an kawo masa kaya a dinke, ko kuma ki dauki nauyin wani abu a gida, ki ba da kudi a yi. In dukiyar taki ma ta kai matsayin da za ki ba da zakka kuma kin san mijinki ya cancata, za ki iya fitar wa ki ba shi, domin shi yake da hakkin ciyar da ke ba ke kike da hakkin ciyar da shi ba.

Alaka Da Sauran Mutanen Da Suka Shafi Miji:
Wadannan sun hada da iyayen miji, abokiyar zama, kannen miji da yayunsa, ‘ya’yan miji wadanda ba ita ta haife su ba da ‘ya’yan da ta haifa. Ya zama dole mace ta kula da wadannan mutanen gaba daya, kuma ta mutunta kowa a cikin su.

Allah ya sa mata su dauki wannan shawara.

ba. Ya kamata mata su lura da wadannan halaye kamar haka:

Exit mobile version