Connect with us

KIWON LAFIYA

Hanyoyin Da Mai Ciwon Sikari Zai Kauce Ma Warin Baki

Published

on

Kungiyar likitocin hakora ta Nijeriya (NDA) ta ba wa duk masu fama da cutar sikari, wato Diabetes, shawarar cewar da su rika gaggauta zuwa asibiti a rika yi mu su gwajin jini tare kuma da ganin likitan hakora lokaci zuwa lokaci, saboda yin hakan zai taimaka wajen kauce wa kamuwa da cututtukan da a ke kamuwa da su a sanadiyyar ciwon sikari.

Wadannan cututtuka kuwa sun hada da cututtukan dake kama baki musamman warin baki, makanta, hawan jini, rashin karfin kashi, ciwon koda, shanyewar bangaren jiki, rashin warkewar rauni da dai sauran wasu cututtukan.

A dalilin haka ne suke kira da wadanda suke fama da wannan cutar da su rika tsaftace kowane bangare na jikinsu musamman bakunan su, bayannan kuma su yawaita zuwa asibiti domin ganin likita.

Likitocin sun kuma bada wasu hanyoyi bakwai da za su taimaka wajen kauce wa haka

Zuwa asibiti domin yin gwajin jini da kuma ganin likitan hakora.

A daina yin amfani da magogin baki mai karfi wajen wanke baki sai kuma a rika kuskure baki lokaci zuwa lokaci, da ruwan kuskure baki da aka inganta wato ‘Mouth Wash’

Za a iya yin amfani da mankade a fata domin warkar da rauni a jiki.

A yawaita cin kayan lambu kamar su lemu, ayaba da ganyaryaki.

A rika shan magungunan wadanda likita ya bada a lokacin da ya kamata.

A kauracewa shan giya da kuma shan sigari.

A rika tsaftace jiki akai-akai.

Ciwon sikari na kama mutum ne idan aka samu matsala da wasu daga cikin abubuwan da ke sarrafa abincin da muke ci a cikin mu.

Insulin na aiki ne a jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar wa mutum kuzarin da yake bukata a jikin sa.

A sanadiyar rashin aikin ‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da ciwon sikari.

Sakamakon binciken majalisar dinkin duniya ya bayyana cewar cutar ta yi ajalin mutane miliyan 1.6 a duniya.

Majalisar ta bayyana cewar domin rage yaduwar ita wannan cutar za ta yi amfani  ne da watan Nuwanba na ko wacce shekara domin wayar da kan mutane ilollin da kuma hanyoyin kaucewa kamuwa da cutar sikari ko kuma diabetis.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: