Hukumar gudanar da bindiken fannin aikin noma ta kasa (ARCN) ta gudanar da bincike da ban-da-ban a hukumomin aikin noma dake kasar nan, inda ta gano daya daga cikin kalubalen da suke kara karu da ake fuskanta na yunwa a kasar nan.
Babban Sakatare mai rikon kwarya na hukumar ta ARCN, Garuba Sharubutu, ne ya sanar da hakan a babban birni tarayyar Abuja.
Babban Sakatare mai rikon kwarya na hukumar ta ARCN, Sharubutu ya sanar da hakan ne a lokacin da yake rattaba hannu akan yarjejeniyar da hukumar ta kula da kungiyoyin kasuwanci masu zaman kansu da suka fito daga cibiyoyin gudanar da bincike a fannin aikin noma da ban-da-ban dake a kasar nan.
A cewar Babban Sakatare mai rikon kwarya na hukumar ta (ARCN) Garuba Sharubutu, idan har muna son a ci moriyar shirin Gwamnatin Tarayya na farfado da fannin tattalin arzinin kasar nan na (ERGP) da Gwamnatin Tarayya maici a yanzu take kan yin kokari akai dole ne a mayar da hankami yadda ya kamata.
Ya kara da cewa, ta hanyar hakan, munyi amannar cewa, hakan zai kara habaka fannin aikin noma a kasar nan haka manoman suma za su amfana sosai.
A cewar Babban Sakatare mai rikon kwarya na hukumar ta (ARCN) Garuba Sharubutu, ta hakan ne kuma zamu rage yunwa a kasar nan da kuma inganta tattalin arzikin da kuma samar da wadataccen abinci a daukacin fadin Nijeriya.
A cewar Babban Sakatare mai rikon kwarya na hukumar ta (ARCN) Garuba Sharubutu, ya kuma nuna jin dadi da kuma alfahari kan samar da cibiyoyin gudanar da bincike a fannin aikin noma kan gudunmawar da suke bai wa fannin na aikin noma a kasar nan.
Babban Sakatare mai rikon kwarya na hukumar ta Garuba Sharubutu ya ce, mun yi amannar cewa, daliban mu suna bukatar a samar masu da dakunan gudanar da yin gwaje-gwaje a fannin aikin noma a kasar nan.
Babban Sakatare mai rikon kwarya na hukumar ta Garuba Sharubutu ya kara da cewa, ba wasu da suka kware a wani fannin ake bukata suyi hakan ba, dole sai wadanda suka kware a fannin aikin noma, inda ya yi nuni da cewa, ba wai kwarrun likitoci za’a nemo ba don bunkasa fannin ba.
A cewar Babban Sakatare mai rikon kwarya na hukumar ta Garuba Sharubutu, manufar ita ce don a samar da fahimtar juna da Kamfanin na Dipton yadda shi ma zai shiga cikin gudanar da binciken a fannin na aikin noma a kasar nan.
A nasa martanin, Daraktan Kamfanin zuba jari da kasuwanci na Dipton Ike Willie-Nwobu, ya sanar da cewa, Kamfanin ba zai kaucewa daga kan yarjejeniyar da aka kulla ba.
Makarfi ya sanar da hakannne a hirar sa da manema labarai a Kaduna, inda Makarfi ya ce, rufe iyakokin, manoma da dama a kasar nan sunga alfanunun hakan domin sun samu dimbin arziki da kuma kara wadata kasar nan da abinci mai yawa.
Sai dai, ya kuma koka kan yadda gwamnatin tarayya ta sake bude iyakokin cikin sauri, inda ya kara da cewa, yan barandan masu shigo da amfanin gona ne daga kasar waje ne don a sayar mana suci kazamar riba kuma basa son harkar noma ta bunkasa a Nijeriya sune suke yin farfagandar cewa, wai za a yi yunwa a kasa, karya suke yi.
Ya sanar da cewa,illar da take yiwa kasa wajen shigo da abinci daga kasashen waje, illolin suna da yawa, inda ya yi nuni da cewa, ya yi nuni da cewa, kudin Nijeriya za a dauka da ya kamata a bunkasa kasar, amma dauka akwai wa wata kasa a shigo da abincin kuma sau da yawa abincin da ake shigo mana dashi muna jin tsoron sai ma ya tashi daga aiki a can kasar tunda suna da lokacin su in abinsu ya kai wani lokaci ko yana sabo ne, za a ce a ajiye shi ba za’ayi amfani dashi ba.
Ya yi nuni da cewa, tsoron da mukeji, ance akwai inda ma ake chanza buhu a shigo mana cututtuka iri-iri, mutanen su siya da tsada suna murna sun sayi kayan kasar waje saboda rashin kishi ta wannan bangaren.