Bello Hamza" />

Hanyoyin Damfara 5 Ta Intanet da Dabarun Kauce Musu (II)

Ci gaba daga jiya

Kwamputarka Ta shiga Hatsari Zamu Taimaka Maka

Sanarwa kan fito na tallar fasahar kariya na kwamputa irinsu “Antibirus DP 2010” ko “SecurityTool,”, ana sanar da kai cewar, na’uranka ta kamu da  mummunan hatsari. Daga nan sai nemi matsa hanyar da zai kai ka ga gano cutar da aka ce kwamputanka ta kamu dashi, zasu gyara maka matsalar amma zasu bukaci ka biya kudi kamar Dala 50 ko abin daya fi shi kadan, lallai za a share maka matsalar.

Tabbas zaka ga kamar an fitar maka da matsalar, amma a zahirin gaskiya a lokacin da ake kokarin share maka matsalar sun kwashe maka mahimman bayanan da suka shafi nambobin credit card dinka, sun kwashe maka kudade, sun kuma bar kwamputanka cikin halin ni ‘yasu.

Hanyar kaucewa wannan tarkon: Idan irin wannan gargadin ya fito maka a kwamputa, to kayi gaggawar kashe kwamfutarka ka kuma yi amfani da tsarin tsaftace kwamputa na ABG Anti-Birus ko ThreatFire AntiBirus.

Soyayya A Kafar Sada Zumunci

Sau da dama zaka hadu da wani ko wata a sahafin sada zumunci na Facebook ko Chat room ko kuma shafin wasanni na birtual game. Daga nan kuka ci gaba da tattaunawa hard a musayan hotuna, har kuka kai ga tattaunawa ta waya, daga kuka fada kogin soyayya har ka fara tunanin ka samu abokiyar zama rayuwar har abada, amma bayanin da zaka fuskanta shi ne wannan da kake so tana kasar waje ne, tana kuma bukatar kudaden magani ko na tikitin jirgin sama in har kana son ku hadu domin ci gaba da rayuwa tare.

Kafin ka ankara n wanke ka, babu wani haduwa a filin jirgi babu soyayya, kayi asarar kudadenka da mutuncin ka.

A halin yanzu an samu hanyoyi daban daban a shafukan intanet da ‘yan danfara suke yaudarar mutane da soyayyar karya domin sace musu kudade.

Shafukan sada zumunci wuri na yin abokai na hakika, har daga kasashen waje, amma ka lura, da zaran wani ya bukaci ka aika masa da kudade, to ka gaggauta katse huldar domin lallai akwai alamun ka fada soyayyar damfara.

Danfara Da Sunan Shafin Kasuwanci Na Gaskiya

Hakan yana faruwa kamar haka, kana sayayya a shafin da saba ka kuma yarda dasu na Amazon, bayan ka ga wani abun da kake bukata ka kuma aika sako sayen abin, sai ka ji shiru kamar an aika bawa garinsu.

Meke faruwa? To lallai ‘yan damfara ne, zasu iya aiko maka da jabun kayak o kuma su cinye kudadenka kai tsaye ba tare da aiko maka komai ba.

‘yan danfaran na amfani da tsarin Amazon ne na bayar da riba, su kan bayar da snarwar tallan kayyakinsu na tsawon mako uku zuwa hudu kafin a sayar da kayayyakin. Tunda tunda tsarin Amazon na tafiya ne kowanne mako biyu, yan danfaran zasu kwashe kudadensu da dadewa kafin wanda aka damfarar ya gane an wanke shi. Wannan tsarin damfaran ba wanda aka damfara kadai yake jin jiki ba har da masu kamfanin Amazon abin na damunsu.

Hanyar Kaucewa Fadawa Wannan Tsarin Damfara: ka lura da sabbin hajojin da ake tallarsu a shafin Amazon, ka kuma lura masu bayani akan abin da ake sayarwar kafin ka saya. Idan ka fada tarkon ‘yan damfara a shafin Amazon, ka gagauta kai koken ka domin tsarinsu ya tanadar cewa, za a biya kudaden da kayi asara ko kuma kayan jabu da aka aiko maka da sunasu, ka zama mai lura da bayanan da suke yi a shafinsu na Amazon Prime a kai a kai.

Exit mobile version